Yadda Tinubu Ya Yi Amfani da Barazanar Trump, Ya Inganta Alakar Sojoji da Amurka

Yadda Tinubu Ya Yi Amfani da Barazanar Trump, Ya Inganta Alakar Sojoji da Amurka

Shugaba Donald Trump na Amurka ya taba zargin ana kashe Kiristoci a Najeriya, amma daga baya kasar ta fara bai wa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu tallafin sojojinta domin dakile ta'addanci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - A farkon watan Nuwambar 2025, wani sako da Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa a kafafen sada zumunta ya jawo damuwa a Najeriya.

Donald Trump wanda ya sake lashe zabe a 2024 ya yi ikirarin cewa Amurka na shirin shiga Najeriya “da makamai” saboda abin da ya kira kashe Kiristoci a kasar.

Yadda Tinubu ya sauya zargin kisan Kiristoci zuwa yaki da ta'addanci
Shugaba Bola Tinubu da takwaransa na Amurka, Donald Trump. Hoto: Bayo Onanuga, Donald J Trump.
Source: Twitter

Gwamnatin Tinubu ta karyata zargin kisan Kiristoci

Sai dai Gwamnatin Najeriya karkashin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi watsi da zargin, kamar yadda Punch ta ce.

Ta bayyana cewa matsalar tsaro na da alaka da ‘yan bindiga da kungiyoyin dauke da makamai, ba wai Kiristoci kadai ake kai wa hari ba.

Kara karanta wannan

Yadda yakin Iran da Isra'ila zai amfani Najeriya da tattalin arzikinta

Gwamnatin ta kuma jaddada cewa Musulmi da mabiya addinan gargajiya su ma suna fuskantar hare-hare daga wadannan kungiyoyi.

Duk da haka, gwamnatin Trump ta sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ta ke sanya ido a kansu kan batun ‘yancin addini, tare da yin barazanar kakaba takunkumi.

Haka kuma Amurka ta yi barazanar rage tallafin kudi da daukar wasu matakan hukunci kan kasar saboda abin da ta kira gazawa wajen kare Kiristoci.

Yayin da wasu ‘yan Najeriya suka fara nuna fargabar yiwuwar kai hare-haren bam a kasar, gwamnatin Tinubu ta sauya salon martaninta cikin nutsuwa, cewar The Nation.

Maimakon kalamai masu zafi, gwamnatin ta ce za ta yi maraba da taimakon Amurka wajen magance matsalolin tsaron da suka dade suna addabar kasar, cewar rahoton Al jazeera.

Ribadu ya yi kokarin gyara alakar Amurka da Najeriya
Malam Nuhu Ribadu da dan majalisar Amurka, Riley Moore yayin wata ganawa. Hoto: Nuhu Ribadu.
Source: Facebook

Yadda Tinubu ya rage barazanar Trump

Kabir Adamu, Daraktan kamfanin 'Beacon Security and Intelligence' da ke Abuja, ya ce gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yi nasara wajen rage barazanar da Donald Trump.

Sai dai ya ce babban kalubalen shi ne gwamnatin Najeriya ba ta bayyana cikakken bayani game da yadda aka cimma hakan ba.

Kara karanta wannan

Rasha: Amurka ta fara bakin jini a Turai saboda yakin Iran

Ya tambaya cewa:

“Da wane farashi ne gwamnati ta cimma wannan, har yanzu gwamnati ba ta fito fili ta sanar da ‘yan Najeriya irin yarjejeniyar da ta kulla da gwamnatin Amurka ba wadda ta kai ga rage tasirin wannan matsala.”
Trump ya tabbatar da kai hari Sokoto
Shugaba Donald Trump yayin kamfe a birnin New York. Hoto: @RealDonaldTrump.
Source: Twitter

Harin sojojin Amurka a jihar Sokoto

Bayan makonni kadan, a daren ranar 25 ga Disambar 2026, Amurka ta kai hare-haren sama a Arewa maso Yammacin Najeriya.

Sai dai rundunar sojin Amurka ta Afrika, wato 'United States Africa Command', ta bayyana cewa an kai hare-haren ne bisa bukatar hukumomin Najeriya.

Tun daga lokacin hadin gwiwar tsaro tsakanin kasashen biyu ya kara karfi musamman wurin yaki da ta'addanci.

Daga baya, sojojin Amurka 100 sun iso Najeriya domin taimakawa wajen horas da sojojin kasar kan yaki da kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Ma’aikatar tsaro ta Najeriya ta ce sojojin Amurka za su ba da tallafin fasaha da kuma raba bayanan sirri.

Ko da yake ba za su shiga yaki kai tsaye ba, amma za su taimaka wajen gano da kuma dakile kungiyoyin ta’adda.

Kara karanta wannan

An fara kiran Tinubu ya ajiye Amurka a gefe, ya dauki darasi daga kasar Iran

Kokarin Tinubu na juya alakar Amurka da Najeriya

Masu nazari sun ce wannan sauyi ya zo da mamaki ga mutane da dama, domin a cikin watanni uku kacal Najeriya ta sauya yanayin rikicin da Trump ya tayar zuwa hadin gwiwar soja.

Ryan Cummings, wani masani kan harkokin tsaro, ya ce labarin ya sauya daga takaddama zuwa hadin kai wajen magance matsalar tsaro.

Sai dai wasu masana sun ce wannan hadin gwiwa wata dabara ce ta Najeriya domin rage tashin hankali tsakanin kasashen biyu.

Duk da haka, wasu sun yi gargadin cewa kasancewar sojojin Amurka a Najeriya na iya kara karfafa kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Sun ce wadannan kungiyoyi kan yi amfani da labarin shigan sojojin kasashen waje wajen jawo sababbin mambobi da kuma yada farfaganda.

Haka kuma wasu na ganin matakin na iya kara raba kan ‘yan Najeriya saboda bambancin ra’ayi kan kasancewar sojojin Amurka a kasar.

Gwamnatin Tinubu ta magantu kan yakin Iran, Isra'ila

A baya, an ji cewa Gwamnatin Tarayya ta fitar da gargadin tsaro ga ’yan Najeriya mazauna Iran da kasashen Gulf ana tsaka da rigima.

Kara karanta wannan

Yaƙin Iran/Isra'ila: Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan ƙayyade farashin fetur

Wannan sanarwa ya biyo bayan kai hare-haren Amurka da Isra’ila kan Iran da ya tayar da hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ma’aikatar Harkokin Waje ta ce tana sa ido kan rikicin da ke kara kamari, tare da shawartar jama’a su guji wuraren sojoji da taruka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.