Yakin Amurka da Iran zai Rikita Duniya, Farashin Litar Fetur zai Doshi N2000 a Najeriya
- Kungiyar masu gidajen sayar da man fetur ta PETROAN ta yi gargadin cewa farashin fetur zai kara hawa daga yadda ya ke a yanzu
- Tun bayan fara yakin da Amurka da Isra'ila suka jawo da Iran a ranar 28 ga watan Fabarairu, 2026 inda aka kashe jagoran kasar
- Farashin dizal ma na iya kusantar N3,000 kan lita yayin da tashin farashin mai ke kara tsananta a kasuwar duniya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Kungiyar masu sayar da man feur PETROAN ta yi gargadi cewa farashin man fetur na iya tashin gwauron zabo a Najeriya.
Lamarin ya biyo bayan yaki da ake kan yi tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran da aka shafe akalla kwanaki 10 ana gwabzawa.

Kara karanta wannan
Yakin Iran da Amurka ya kara taba Dangote, ya canza farashin fetur karo na 3 a Najeriya

Source: Facebook
Daily Trust ta ruwaito PETROAN ya bayyana fargaba cewa ba iya fetur ne zai kara farashi sosai ba, har da man dizal zai iya kara farashi.
Ana fargaba kan farashin man fetur
Independent Newspaper ta wallafa cewa Shugaban PETROAN na kasa, Billy Gillis-Harry na tsoron farashin litar fetur zai iya tashi har zuwa kusan ₦2,000.
Hakazalika, kungiyar ta ce farashin litar dizal, na iya kusantar ₦3,000 idan halin da ake ciki a kasuwar makamashi ta duniya ya ci gaba da tabarbarewa.

Source: Getty Images
Ya yi gargadin cewa karin farashin man fetur na iya kara tsananta hauhawar farashi a kasa, tare da haddasa rasa ayyukan yi ga mutane da dama.
A cewarsa, karin farashin zai kuma haifar da karin kudin sufuri, wanda hakan zai sa farashin kayayyaki da hidimomi ya karu a fadin Najeriya.
Yadda farashin mai ya fara hawa - PETROAN
Gillis-Harry ya bayyana cewa kafin rikicin da ake yi a Gabas ta Tsakiya ya barke, ana sayar da fetur a kusan ₦774 kan lita.
Amma yanzu farashin ya haura ₦1,000 a kan kowacce lita, wanda ke nuna karin kusan 30% tun bayan fara yaki a Gabas ta Tsakiya.
Haka zalika, dizal wanda a baya ake sayarwa a kusan ₦950 kan lita, yanzu ya kai sama da ₦1,400 kan lita, abin da ke nuna karin kusan 49%.
Ya kara da cewa rikicin da ya kunshi kasashen Isra’ila, Amurka da Iran na ci gaba da janyo tashin hankali da tsoro a kasuwar man fetur ta duniya.
Farashin danyen mai ya tashi a duniya
A baya, kun ji cewa farashin danyen mai ya haura Dala 100 a kasuwannin duniya sakamakon yakin da ake gwabzawa tsakanin Amurka/Isra'ila da kasar Iran a makon da ya wuce.
Shugaba Donald Trump ya bayyana tsadar man a matsayin dan takaitaccen kalubale da duniya za ta fuskanta yayin da Amurka ke yaki ta shige gaba wajen jawo yakin.
Kasuwannin hannun jari na duniya sun fuskanci faduwar daraja yayin da Iran ta yi barazanar cewa farashin man zai iya kai Dala 200 yayin da ake ci gaba da gwabza wa.
Asali: Legit.ng
