Abubuwan da Musulmi zai Ya Samu Lada Sosai a 10 na Karshen Ramadan

Abubuwan da Musulmi zai Ya Samu Lada Sosai a 10 na Karshen Ramadan

  • Malaman addinin Musulunci na cigaba da kira ga al'umma su dage da ibada a daidai lokacin da watan Ramadan 2026 ke shirin karewa
  • Wani malamin addinin Musulunci, Sheikh Usman Muhammad Al-Juzuri ya yi bayani game da muhimmancin kwanaki 10 na karshen Ramadan
  • A hira da ya yi da Legit Hausa, Sheikh Al-Juzuri ya bayyana cewa daga daren 21 ga watan Ramadan ne za a shiga 10 na karshen watan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Malamin addinin Musulunci, Sheikh Usman Muhammad Al-Juzuri ya bayyana wasu muhimman abubuwa da ya ce ya kamata Musulmi ya mayar da hankali a karshen Ramadan.

Malamin ya bayyana cewa ana so kowa ya yi iya kokarinsa wajen ganin ya yi ayyuka masu yawa a kwana 10 na karshen watan.

Kara karanta wannan

Shugaban Faransa ya fara kokarin shawo kan Ikasar ran domin tsayar da yaki

Sheikh Usman Muhammad Al-Juzuri
Sheikh Usman Al-Juzuri yayin wa'azi a jihar Gombe. Hoto: Naziru Usman
Source: Facebook

Sheikh Al-Juzuri ya yi bayani ne a wata hira da ya yi da Legit Hausa ta wayar tarho yayin da ya ke gabatar da tafsirin Ramadan a jihar Borno.

Muhimmancin 10 na karshen Ramadan

Sheikh Usman Al-Juzuri ya bayyana cewa Musulunci ya tabbatar da cewa darare guda 10 na karshen Ramadan sun fi kowane dare daraja.

Malamin ya bayyana cewa ana samun fa'ida a dukkan darare da yini na kwanaki 10 na karshen watan, inda ya ce ana iya yin ibada da dare da kuma rana domin samun lada.

Malamin ya kara da cewa ana so kowa ya dage a kwanaki 10 na karshen Ramadan, domin a cewarsa, Annabi SAW yana dagewa yana kuma tayar da iyalansa su yi sallah a cikin dare.

Itikafi a karshen watan Ramadan

Sheikh Al-Juzuri ya bayyana cewa Itikafi na cikin muhimman ayyukan ibada da ake so duk wanda ya ke da dama ya yi a karshen watan Ramadan.

Kara karanta wannan

'Yajuju da Majuju sun bayyana suna kashe mutane a duniya,' Sheikh Gumi

A cewar malamin, Annabi SAW ya yi Itikafi a karshen Ramadan, kuma tun da ya fara bai taba dainawa ba har zuwa karshen rayuwarsa.

A kan haka, ya kara da cewa yana da matukar muhimmanci kowane Musulmi ya ribaci lokacinsa wajen yin abin da ya dace a kwanakin karshen watan.

Batun Lailatul Qadr

Malamin ya kara da cewa a karshen watan ake samun daren Lailatul Qadr, inda ya ce ana bukatar a yawaita karanta Qur'ani, sallahr dare da sauran ayyukan alheri.

Ya bayyana cewa ana so a yawaita sadaka a karshen watan, musamman idan aka dace da dare Lailatul Qadr mai tarin albarka.

Sheikh Al-Juzuri ya ce a daren Lailatul Qadr aka saukar da Al-Kur'ani kuma ana iya dacewa da shi a karshen watan, ya ce ana hasashen dacewa da shi a daren 27 ga watan Ramadan.

Ya kara da cewa Manzon Allah SAW ya ce duk wanda ya tsaya a daren Lailatul Qadr ya yi ibada Allah zai gafarta masa zunubansa.

"Ina kira ga duk wanda sakon nan ya riske shi, ya yawaita addu'a a daren Lailatul Qadr, musamman saboda halin da muke ciki a Najeriya."

Kara karanta wannan

Babu zama: Shugaba Trump zai nufi kasar Cuba da yaki bayan Iran

"Addu'a na da muhimmanci a wannan dare, saboda haka mu roki Allah ya yaye mana matsalolin da muke fama da su."
Sheikh Usman Muhammad Al-Juzuri
Sheikh Usman Al-Juzuri yayin tafsiri mako-mako a Gombe. Hoto: Naziru Usman
Source: Facebook

Bayanin da Sheikh Daurawa ya yi

A wani rahoto da Aminiya ta fitar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bukaci jama'a su yawaita addu'a, karatun Kur'ani da sauran ibada a 10 na karshen Ramadan.

Malamin ya bukaci a rika kabbarori, inda ya ce ana yin kabbarori daga faduwar ranar gobe sallah har a yi sallar Idi.

'Yajuju da Majuju sun bayyana,' Gumi

A wani labarin, mun kawo muku cewa Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya bayyana cewa Yajuju da Majuju sun bayyana a duniya.

Ya bayyana haka ne a wajen tafsiri a Ramadan 2026 yayin da ya ke sharhi game da rikicin da ake ta fama da shi Gabas ta Tsakiya.

Sheikh Gumi ya kawo alamomi da ya ce sun tabbatar da bayyanar Yajuju da Majuju, ya kawo misalin abubuwan da suka faru a Rasha da Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng