Falalar kwanaki goman karshe na watan Ramadan

Falalar kwanaki goman karshe na watan Ramadan

Har a yanzu lokaci bai kure ba da ya kamata musulmi su zage dantse da ba da himma wajen gudanar da ibada a yayin da bai wuce sauran kwanaki 8 ba mu yi bankwana da watan Azumin Ramalana na bana.

Koda mutum bai kasance ya dage da ibada ba a kwanakin da suka shude, a yanzu musulmi za su iya ribatar kwanakin da suka rage wajen tara dimbin lada.

A dage da rokon gafarar Ubangiji, nemansa da ya biya bukatu, sannan kuma a mika kai wajen yi masa ibada babu dare babu rana doriya a kan wadda aka saba yi a baya.

Ganin yadda galibin musulmai suke a yanzu, sun kasance cikin matsin lamba na aiki, kasuwanci, da hanyoyin samun na abinci a wannan wata na azumin Ramadana.

Sai dai fa wadanda suka san fa'idar da ke tattare da kwanakin da suka rage na wannan wata, su na watsar da jin dadin rayuwar duniya da kuma takaice duk wata walwala domin neman kusanci da Allah.

Kwanakin da suka rage na wannan wata su na cike da tarin falala marar misali, wadda ta sanya wasu ke kebance kawunansu wajen shiga Itikafi domin kara ingancin alaka da kuma kusanci da Mahallicci.

Ana ribatar wannan lokaci wajen gudanar da addu'o'i na neman Afuwa, Gafara da kuma Rahamar Allah. Yawaita karatun Al-Qur'ani da kuma waiwaye a kan ayyukan da mutum ya yi.

Daya daga cikin manyan ibadu da bisa al'ada aka saba yi a wannan lokaci, shi ne shiga Itikafi domin neman aminci da yardar Allah Khaliqu.

Wannan ita ce al'adar da aka saba gudanar wa a addinin Islama tun a lokacin saukar Wahayi kawo yanzu, kuma ta kasance al'adar da Annabin Tsira, Muhammad Sallallahu Alaihi Wassalam, ya tabbatar da ita kamar yadda Allah ya shar'anta.

Falalar kwanaki goman karshe na watan Ramadan

Falalar kwanaki goman karshe na watan Ramadan
Source: UGC

Ma'anar Itikafi dai ita ce kebance kai a cikin Masallaci da niyyar yi wa Allah ibada shi kadai saboda cancantar sa ba tare da hada shi da abokin tarayya ba, da nufin neman kusanci da shi.

A yayin Itikafi, ba wani abin da ake bukata face lura da salloli na nafila, nazarin karatukan da shafi addinin Islama, karatun Alqur’ani mai girma da yawaita Zikiri da ambaton Allah.

Ga wadanda basu samu damar shiga Itikafi ba, ya kamata su ci ribar wannan lokacin sosai don neman kusanci da Allah, yi wa dokokinsa da'a da biyayya, da nisantar da kai daga abubuwan da ya haramta da nufin samun rabauta.

KARANTA KUMA: Mutane 'yan shekaru 31 zuwa 40 sun fi saurin kamuwa da cutar korona - NCDC

A cikin darare goma na karshe wannan wata, akwai dare daya tamkar da bila adadin da Allah ya ke bude dukkanin kofofin Rahama, ya na umartar Mala'ikunsa su saukar da aminci har zuwa ketowar Al Fijr.

Allah ya sanya wa wannan dare suna Daren Laylatul Qadr, ma'ana daren da Allah ya ke Kaddara komai da izininsa. Shi ne daren da Allah a cikin Suratul Qadr ya ke cewa ya fi Darare Dubu Alheri.

Manzon Allah tsira da aminci su kara tabbatar a gare shi yana cewa: Duk wanda ya dace ya yi sallah a mafi girman darare wato Daren Laylatul Qadr, cikin yakini da neman yarda da ladan Allah, to an gafarta masa dukkanin abinda ya gabata na zunubansa.

Ana tsintar wannan mafificin dare a daya daga cikin darare na mara a kwanaki goma na karshen watan Ramadan, wato daren 21, 23, 25, 27 ko 29.

Ladan duk wata ibada da mutum zai yi a wannan dare, ya fi ladan ibadar da mutum zai gudanar ta watanni dubu, wanda shi ne kimanin tsawon rayuwar da mutum zai yi a doron kasa.

Mafificiyar addu'a da Manzon ya koyar kuma ya ce musulmi su dage da yi ta ita ce addu'ar neman Afuwar Allah kuma ya ba da addu'ar kamar haka wadda ya ce a yawaita yi a wannan lokaci:

“Allahumma innaka afuwwun tuhib-bul af-wa, fa-afu anni”

Falalar kwanaki goman karshe na wannan wata ya sanya ake kwadaitar da musulmi a kan shiga Itikafi domin sharbar duk wani romo da ke tattare da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel