Borno: An Kwantar da Jaruman Sojoji da aka Kashe a Yaki da Boko Haram
- Rundunar Sojin Najeriya ta yi jana’izar sojojin da suka rasu yayin fafatawa da ‘yan ta’addan Boko Haram a Jihar Borno
- An birne sojojin ne a makabartar sojoji ta Maimalari Cantonment da ke Maiduguri yayin da jama'a ke cike da jimamin rashin daka yi
- Shugabannin soji da gwamnatin Borno sun yi magana kan jarumtakar sojojin tare da ba wa iyalansu hakurain wannan lamari mai daga hankali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno - Rundunar Sojin Najeriya ta yi jana’izar wasu sojoji da suka rasu a fagen daga yayin ci gaba da yakin da ake yi da ‘yan ta’adda a jihar Borno.
An gudanar da jana’izar ne ranar Juma’a 6 ga watan Maris, 2026 a makabartar sojoji da ke Maimalari Military Cantonment a Maiduguri, babban birnin jihar.

Source: Getty Images
Jaridar Punch ta wallafa cewa jami’in hulda da jama’a na rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai a yankin Arewa maso Gabas, Laftanar Kanar Sani Uba ya tabbatar da hakan.
An birne jaruman sojoji a Borno
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Laftanar Kanar Sanni Uba ya sanar da jana'izar sojojin a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, 7a ga watan Maris 2026.
Da yake jawabi yayin jana’izar, kwamandan rundunar Operation Hadin Kai, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, ya bayyana cewa akwai radadi a wannan rasuwa.aisha

Source: Original
A cewarsa, aikin soja yana da lokutan farin ciki da nasara, amma akwai lokutan bakin ciki da ke tuna wa mutane irin farashin da ake biya wajen kare kasa.
Ya ce:
“A Cikin aikin soja akwai lokutan nasara da ke sa mu yi alfahari da jarumta, karfin gwiwa da hadin kan da ke nuna irin hidimar da muke yi. Amma akwai kuma lokutan bakin ciki da ke dora mana nauyi a zukatanmu, suna kuma tuna mana da hakikanin farashin hidima kamar yadda muka gani a yau."

Kara karanta wannan
Babbar magana: Ana tsaka da yaki da Iran, 'dan Majalisar Amurka ya dauko batun Najeriya
Janar Abubakar ya kara da cewa sojojin da suka rasu sun nuna jarumta, sadaukarwa da kuma jajircewa wajen cika aikinsu.
Rundunar sojin Najeriya ta yi rashi
Ya ce rasuwarsu ba rashi ba ne ga iyalansu kawai, har ma ga rundunar sojin Najeriya, dakarun kasar baki daya da kuma kasa gaba daya.
A kalamansa:
“Sun sadaukar da rayuwarsu ne domin wata manufa mafi girma fiye da kansu – wato kare kasa, jama’a da kuma alkawarin da suka dauka na kare martabar Najeriya."
Janar Abubakar ya kara da cewa sojojin sun yi yaki da jarumta tare da kiyaye kyawawan al’adun rundunar soji.
Ya kuma tabbatar wa iyalan mamatan cewa sadaukarwar da sojojin suka yi ba za ta tafi a banza ba, yana mai cewa za a biya dukkannin hakkokinsu cikin gaggawa domin tallafa wa iyalansu.
Haka kuma ya mika ta’aziyya ga iyalan mamatan a madadin Babban Hafsan Tsaro, Babban Hafsan Sojin Kasa da kuma dakarun Najeriya baki daya.
Manyan jami’an soji daga hedikwatar Operation Hadin Kai da rundunar 7 Division na sojin Najeriya sun halarci jana’izar, tare da kwamandan 25 Task Force Brigade.
Sai kuma jami’an gwamnatin Borno, shugaban karamar hukumar Damboa da kuma iyalai da ‘yan uwan sojojin da suka rasu.
'Yan ta'adda sun kashe sojoji a Borno
A baya, kun samu labarin cewa 'yan ta'adda da ake zargin Boko Haram ne sun kai hari sansanin sojoji da na 'yan gudun hijira a Ngoshe da ke Gwoza, jihar Borno.
Maharan sun yanka babban Limamin garin Ngoshe tare da kona gidaje da motocin yaki bayan dakarun soji sun gaza dakile harin da ya jawo mummunan asara.
Sanata Ali Ndume ya bukaci rundunar sojoji ta kaddamar da gagarumin samame a dajin Sambisa domin fatattakar yan ta'addan da ke suka fake a wajen suna kai hari cikin gari.
Asali: Legit.ng

