Ta Faru Ta Kare: Yakin Iran, Isra'ila da Amurka Ya Haifar da Matsala a Najeriya

Ta Faru Ta Kare: Yakin Iran, Isra'ila da Amurka Ya Haifar da Matsala a Najeriya

  • Yakin da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya ya fara shafar wasu sassa na duniya dangane da man fetur din da ake amfani da shi
  • Rikicin dai ya jawo farashin danyen mai ya yi tashin gwauron zabi a kasuwannin duniya wada hakan ya jawo samun kari a farashin man fetur
  • A Najeriya ma ba ta sauya zani ba, inda farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi a birnin Legas bayan matatar Dangote ta kara kudin kan yadda take sayarwa 'yan kasuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi inda ya kai kusan N1,080 a kowace lita a sassan birnin Legas.

Tashin ya auku ne sakamakon takaddama da ake yi a yankin Gabas Ta Tsakiya wadda ta janyo tashin farashin danyen mai a kasuwar duniya.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Majalisar Dinkin Duniya ta hango abin da zai faru sakamakon yakin Amurka da Iran

Farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi a Najeriya
Mutane na sayen fetur a wani gidan mai a Najeriya Hoto: NurPhoto
Source: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta ce wani rangadin kasuwa da aka gudanar a gidajen mai da dama a Legas a ranar Asabar, 7 ga wata Maris 2026 ya nuna karuwar farashin.

Farashin fetur ya yi tashin gwauron zabi

A yanzu farashin man fetur yana tsakanin N1,020 zuwa N1,080 kan kowace lita, dangane da wurin da gidan man yake.

Wannan sabon karin ya biyo bayan matakin da matatar Dangote ta dauka na sake kara farashin da take sayar da man fetur ga 'yan kasuwar da ke sayan man kafin su sayar wa jama'a a gidajen mai.

Farashin danyen mai ya tashi

A daidai lokacin hada wannan rahoto, danyen mai na Brent ana sayar da shi a kan kusan $92.69 kan kowace ganga.

Ana sayar da danyen man ne a kan wannan farashin sakamakon fargabar katsewar hanyoyin samar da mai saboda rikicin da ke kara tsananta tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran.

Kara karanta wannan

Yakin Amurka da Iran: Matatar Dangote ta yi magana kan yiwuwar samun man fetur a Najeriya

Masana harkar makamashi sun bayyana cewa wannan takaddama na iya kara matse hanyoyin samar da mai a duniya.

Farashin man fetur na iya kai wa N1,100

Sun yi gargadin cewa idan har farashin danyen mai ya ci gaba da tashi a kasuwar duniya, to farashin fetur a Najeriya na iya haura kusan N1,100 kan kowace lita.

A gefe guda kuma, binciken ya nuna cewa tuni gidajen mai da dama suka sauya farashin su domin ya yi daidai da sabon tsarin.

Hakazalika, a wasu yankunan birnin Ibadan na jihar Oyo ana sayar da man har a kan N1,200 a kowace lita.

Farashin ma fetur ya tashi a Legas
Wasu mutane a kan layin sayen man fetur a Najeriya Hoto: Pius Utomi Ekpei
Source: Getty Images

Legit Hausa ta tuntubi wani dan Achaba a birnin Legas, Faisal Abubakar, wanda ya tabbatar da tashin farashin man fetur din.

"Eh tabbas gidajen mai sun kara farashi domin a wasu wuraren ana sayarwa N1,040, N1,050 har zuwa N1,080."
"A yau na siya a kan farashin N1,050 sabanin farashin da na saya jiya a kan N950."

- Faisal Abubakar

Amurka ta amince da sayarwa Isra'ila makamai

Kara karanta wannan

Najeriya ta shiga jerin kasashe 3 da za su samu alheri sakamakon yakin Iran da Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnatin Amura karkashin jagorancin Shugaba Donald Trump, ta amince da sayarwa kasar Isra'ila makamai.

Gwamnatin ta Donald Trump ta yi amfani da ikon "gaggawa" domin kauce wa bukatar amincewar majalisa yayin da Washington da Tel-Aviv ke ci gaba da kai hare-hare kan Iran.

Shirin sayar da makaman ya haɗa da manyan bama-bamai na bai-ɗaya guda 12,000 nau'in BLU-110A/B, bama-bamai masu nauyin 1,000 pounds tare da ayyukan injiniya, sufuri, da goyon baya ta fuskar fasaha.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng