Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Farmaki Ministan Buhari, Sun Kona Ofishin Jam'iyya

Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Farmaki Ministan Buhari, Sun Kona Ofishin Jam'iyya

  • Wasu 'yan bindiga sun kai wa ayarin motocin Rotimi Amaechi hari tare da kona ofishin jam'iyyar ADC a garin Ubima dake Rivers
  • Jami'an tsaro sun fatattaki maharan zuwa cikin daji bayan musayar wuta yayin da Amaechi yake kokarin yin rijistar zama d'an ADC
  • Amaechi ya bukaci rundunar yan sanda da DSS su kamo tare da hukunta wadanda suka kai masa harin domin tabbatar da adalci

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Rivers - Tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi, ya bukaci hukumomin tsaro su kamo ƴan bindigar da suka farmaki ayarin motocinsa tare da ƙona ofishin jam’iyyar ADC a garin Ubima.

Tsohon ministan sufurin ya ziyarci mahaifarsa dake ƙaramar hukumar Ikwerre ne domin yin rijistar zama ɗan jam’iyyar ADC, amma wasu ƴan bindiga suka yi ƙoƙarin hana shi shiga garin.

Kara karanta wannan

An fara: Tsohon gwamna ya shiga ADC bayan kai masa hari da kona ofishinta

'Yan bindiga sun farmaki Rotimi Amaechi, sun kona ofishin jam'iyyar ADC.
Tsohon gwamnan Rivers, kuma tsohon ministan sufuri, Rotomi Amaechi. Hoto: @ChibuikeAmaechi
Source: Twitter

'Yan bindiga sun farmaki tsohon minista

Wannan harin ya tayar da hankulan mazauna yankin, inda maharan suka nuna tsantsar adawa da sauya shekar tsohon ministan, in ji rahoton Punch.

Rahotanni sun nuna cewa tun kafin ƙarasawar Amaechi garin Ubima da misalin ƙarfe 12:15 na rana, ƴan bindigar sun riga sun sa shinge a kan hanya tsakanin Ubima da Omuanwa.

Kazalika, a daren Alhamis, maharan sun ƙona ofishin jam'iyyar ADC na mazabar Ubima, sannan suka yi ta harbe-harbe tare da yin kaca kaca da ƙofar gidan iyayen Amaechi da harbin bindiga.

Maharan sun mamaye garin ne da nufin tsoratar da dukkan wani mai goyon bayan tsohon gwamnan, da kuma dakile shi daga abin da ya zo aiwatarwa.

Yadda jami'an tsaro suka kori 'yan bindiga

Yayin da ayarin motocin Amaechi ya isa wurin da ƴan bindigar suka yi shinge, jami'an tsaron dake tare da shi sun fafata da maharan.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe mahaifin tsohon mataimakin gwamna a Najeriya

Jami'an sun nuna ƙwarewa ta hanyar bude wuta, wanda hakan ya sa ƴan bindigar suka tsere cikin daji domin neman tsira, in ji rahoton The Cable.

Bayan ya zagaya ofishin da aka ƙona, Amaechi ya nuna jin daɗinsa ga kwamishinan ƴan sanda, daraktan DSS, da kuma kwamandan NSCDC na jihar bisa yadda suka ba shi agaji cikin gaggawa.

Amaechi ya bukaci bukaci jami'an tsaro su kamo 'yan bindigar da suka farmake shi.
Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya na kaddamar da ofishin jam'iyyar ADC a Rivers. Hoto: @ChibuikeAmaechi
Source: Twitter

Amaechi ya rarrashi mabiya ADC

Amaechi ya buƙaci mambobin jam'iyyarsa da kada su ɗauki doka a hannunsu, yana mai jaddada cewa aikin ƴan sanda ne su kamo tare da hukunta waɗanda suka kitsa wannan hari.

Ya bayyana cewa bai kamata wannan al'ada ta ci gaba ba, kuma hanya ɗaya tilo da jami'an tsaro za su nuna kin hakan shi ne ta hanyar hukunta masu laifin.

Ya kuma yi kira ga gwamnan jihar da ya tabbatar da samar da isasshen tsaro a faɗin jihar domin kauce wa rikicin da zai iya kai wa ga rashin doka da oda.

'Yan bindiga sun farmaki Peter Obi

A wani labari, mun ruwaito cewa, Yunusa Tanko, jagoran Obidient Movement ya yi zargin cewa 'yan bindiga sun kai hari kan tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi a Benin.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ana ciki yaki da Iran, tsohon soja ya tayar da tarnaki a majalisar Amurka

Tanko ya bayyana cewa wasu 'yan bindiga da ake zargin an dauko hayarsu don kisan kai ne suka farmaki Peter Obi tare da manyan jiga-jigan jam'iyyar ADC.

Lamarin ya faru ne lokacin da Peter Obi da sauran shugabannin jam'iyyar ADC suka halarci taron shelar komawar Barrister Olumide Akpata zuwa jam'iyyar ta ADC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com