Dalilin Gidan Gyaran Hali na Cigaba da Tsare Abba Kyari duk da Hukuncin Kotu

Dalilin Gidan Gyaran Hali na Cigaba da Tsare Abba Kyari duk da Hukuncin Kotu

  • Hukumar gidajen yari ta kasa ta tabbatar da cewa Abba Kyari har yanzu yana tsare a hannunta duk da wani hukunci da kotu ta yanke
  • A ranar Alhamis, 5 ga watan Maris, 2026 ne aka samun rahoton cewa kotu ta wanke dakataccen dan sandan daga zarge-zargen NDLEA
  • Sai dai hukumar ta bayyana cewa ba a fitar da cikakken rahoton ba, domin har yanzu yana fuskantar wadansu tuhume-tuhumen

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya ta bayyana cewa har yanzu dakataccen babban jami'in dan sanda, DCP Abba Kyari na tsare

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Samson Duza, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis 5 ga watan Maris 2026 a birnin Abuja jim kadan bayan labarin hukuncin kotu kan Kyari ya bazu.

Kara karanta wannan

"Kada a dagula siyasar Kano": NNPP ta aika sako kan shirin tsige Mataimakin gwamna

Kotu ta cigaba da tsare Abba Kyari
Abba Kyari sanye da farin kaya tare da wasu lauyoyinsa a kotu Hoto: Hamza Nuhu Dantani
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Samson Duza ya ce bayanan da suka bazu a kafafen yada labarai cewa an wanke Kyari gaba daya ba su bayyana ainihin gaskiya ba.

Dalilin ci gaba da tsare Abba Kyari

NAN ta wallafa cewa Samson Dazu ya bayyana cewa tsohon jami’in na ‘yan sanda yana fuskantar shari’o’i guda biyu daban-daban a gaban kotu.

Ya yi karin hasken cewa hukuncin da aka yanke shi daga zarginsu ya shafi daya daga cikin shari’o’in ne kawai.

A cewarsa, shari’ar da aka yanke hukunci a kanta ita ce wacce ta shafi zargin bayyana kadarori ba daidai ba.

Duza ya kara da cewa kotu ta yanke hukuncin wanke Kyari ne bayan ta gano cewa masu gabatar da kara ba su gabatar da isassun hujjoji da za su tabbatar da zargin ba.

Har yanzu ana shari'a da Abba Kyari
DCP Abba Kyari, dakataccen Shugaban IRT na rundunar yan sandan Najeriya Hoto: Datti Assalafiy
Source: Facebook

Ya ce:

“Yana da shari’o’i biyu. Daya ta shafi bayyana kadarori ba daidai ba, dayan kuma yana da alaka da zargin miyagun kwayoyi."

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar tsohon ministan Tinubu ya yake shi, yana kus kus da kusoshin adawa

Ya kara da cewa:

“Wadda aka wanke shi a kai ita ce ta bayyana kadarori ba daidai ba saboda rashin hujjoji ko rashin karfi a cikin shari’ar.”

Ana ci gaba da shari'a da Abba Kyari

Jami’in hulda da jama’ar ya kara da cewa duk da wannan hukunci, Abba Kyari ba zai fita daga kurkuku ba a halin yanzu.

Ya bayyana cewa har yanzu akwai wata shari’a daban da ta shafi zargin safarar miyagun kwayoyi da ake ci gaba da sauraro a kotu.

A cewarsa, wannan shari’a ba ta kare ba tukuna, don haka dole ne Kyari ya ci gaba da kasancewa a hannunsu har sai kotu ta yanke hukunci na karshe.

Ya ce:

“Shari’ar da ta shafi miyagun kwayoyi tana ci gaba da gudana a gaban kotu. Saboda haka, Kyari zai ci gaba da kasancewa a tsare har sai an kammala sauraron karar."

Kyari, wanda a baya ya jagoranci sashen IRT na rundunar ‘yan sandan Najeriya, ya shiga jerin matsalolin shari’a ne bayan zarge-zargen da suka danganta shi da safarar miyagun kwayoyi.

Kara karanta wannan

Jagoran Musulunci na Iran: Mutane 5 da za su iya maye gurbin Ayotallah Khamenei

Kotu ta yi hukunci a shari'ar Abba Kyari

A wani labarin kun ji cewa babbar kotun tarayya ta wanke DCP Abba Kyari daga tuhume tuhume 23 da suka shafi kin bayyana kadarori da NDLEA ta shigar gabanta.

Mai shari'a James Omotosho ya bayyana cewa NDLEA ta gaza gabatar da kwararan shaidu domin tabbatar da zargin da take yi wa Kyari na cewa ya yi ba dai-dai ba.

Har yanzu Kyari da wasu jami'an yan sanda hudu suna fuskantar wata shari'ar daban kan zargin safarar hodar iblis da wasu miyagun kwayoyi da NDLEA ke zarginsu da shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng