Abu Ya Girma: El Rufai Ya Kinkimo Sabon Aiki kan Takaddamarsa da Hukumar ICPC
- Ana ci gaba da musayar yawu tsakanin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da hukumar yaki da cin hanci ta ICPC
- El-Rufai da iyalansa sun mika bukatunsu ga hukumar ICPC kan wasu zarge-zarge da ta yi a kan tsohon gwamnan
- Sun bukaci ta gaggauta biyan diyya ko kuma su dauki matakan shari'a masu tsauri a kanta ba tare da bata lokaci ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, tare da iyalansa, sun mika bukatunsu ga hukumar yaki da cin hanci ta ICPC.
El-Rufai da iyalansa sun buƙaci biyan diyar kuɗi har Naira biliyan 15.6 daga hukumar ICPC shugabanta, da sauran jami’anta, sakamakon kama shi, tsare shi, da kuma bayanan ƙarya da aka fitar a kansa.

Source: Twitter
Wani mai amfani da @IU_Wakili a shafin X ya sanya wasikar da lauyoyin tsohon gwamnan suka fitar.

Kara karanta wannan
El Rufai: ICPC ta fitar da jerin abubuwa 67 da ta samu a gidan tsohon gwamnan Kaduna
El-Rufai na son diyya daga ICPC
Wannan buƙata ta biyo bayan iƙirarin da hukumar ta yi na cewa an gano “na’urorin saurarar maganganun mutane ta waya” a gidan El-Rufai.
A cikin wasiƙar da lauyoyin El-Rufai suka fitar mai kwanan wata 4 ga watan Maris, 2026, sun bayyana sanarwar da ICPC ta fitar a ranar 2 ga Maris, 2026 a matsayin ɓatanci da kuma yaudara, inda suka jaddada cewa hakan ya lalata mutuncin tsohon gwamnan a idon duniya.
A cikin wasikar, tsohon gwamnan ya zargi hukumar da ayyukan da suka take haƙƙinsa na ɗan adam, inda ya buƙaci biyan kuɗaɗe kamar haka:
- Naira Biliyan 5: Matsayin diyyar asarar da aka yi masa
- Naira Biliyan 5: Matsayin diyar hukunci ga hukumar domin hana sake aikata hakan
- Naira Biliyan 5: Matsayin diyyar asarar da aka jawo masa
- Naira Miliyan 500: Saboda bayanan ƙarya masu cutarwa
- Naira Miliyan 100: Matsayin kuɗin gudanar da shari’a
- Jimillar Kuɗin: Naira Biliyan 15.6.
Wadanne matakai za a dauka na gaba?
Lauyoyin El-Rufai sun ba hukumar sa’o’i 24 domin ta cika waɗannan buƙatu, idan kuma ba haka ba, za su ɗauki karin matakan shari’a.
Waɗannan matakai sun haɗa da shigar da ƙarar raina kotu a kan shugaban ICPC a babbar kotun tarayya, hanzarta shari’ar kare haƙƙin ɗan adam da neman beli a babbat kotun Abuja.

Source: Facebook
Shigar da ƙarar cin zarafi ta hanyar shari'a, tsare mutum ba bisa ƙa'ida ba, da kuma amfani da ofis ta hanyar da ba ta dace ba.
Haka kuma, lauyoyin sun yi barazanar kai rahoton zargin yin na takardar bogi ta umarnin tsare mutum domin bincike da kai ƙarar majistaren da ya sanya hannu kan takardar zuwa hukumar kula da aikin shari’a ta Abuja.
Haka kuma, sun yi barazanar shigar da kara zuwa hukumar kare haƙƙin ɗan adam ta Afirka.
Dan El-Rufai ya yi zargi kan ICPC
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, Mohammed Bello El-Rufai, ya yi maganganu kan hukumar ICPC.
Bello El-Rufai ya zargi ICPC da kokarin bata sunan mahaifinsa ta hanyar mayar da haƙƙinsa na yin shiru da tsarin mulki ya ba shi dama ya zama wani makami na yaƙi da shi.
'Dan majalisar ya yi zargin cewa ICPC ta fi mayar da hankali kan yaƙin kafofin yaɗa labarai maimakon bin tafarkin doka.
Asali: Legit.ng

