Bayan Rantsar da Shi, Shugaban Rundunar 'Yan Sandan Najeriya Ya Tabo Batun Yakin Iran da Amurka
- Sufetan 'yan sandan Najeriya da ya karbi rantsuwar kama aiki, Tunji Disu ya yi magana kan rikicin da ya barke tsakanin Iran da Amurka/Isra'ila
- IGP Disu ya bayyana cewa rundunar yan sandan kasar nan na bibiyar abubuwan da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya domin zama cikin shiri
- Ya kara da cewa rundunar tana daukar matakai da dama, ciki har da kara yawan sintiri da kuma yin aiki tare da shugabannin al’umma
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya na 23, Tunji Disu, ya bayyana cewa rundunar 'Yan Sanda na sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya.
Yankin Gabas ta Tsakiya dai ya fada cikin rikici da tashin hankali tun bayan barkewar yaki tsakanin Amurka/Isra'ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a karshen makon da ya gabata.

Source: Twitter
Sufeton yan sanda ya tabo yakin Iran da Amurka
A rahoton da Vanguard ta dauko, Tunji Disu ya bayyana cewa rundunar 'yan sanda na bibiyar abubuwan da ke faruwa a wannan yaki domin tantance ko hakan na iya yin tasiri a Najeriya.
Disu ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da ‘yan jarida na fadar shugaban kasa bayan rantsar da shi a matsayin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda na 23 a tarihin Najeriya.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ne ya jagoranaci rantsar da shi a wani dan taro da aka shirya a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Laraba, in ji tashar Channels tv.
Matakan da yan sanda ke dauka a Najeriya
Sabon Sufeto Janar ya ce rundunar ‘yan sanda ta kara kaimi wajen sa ido da kuma sintiri a fadin kasar domin tabbatar da doka da oda.
Disu ya ce:
“A ko'ina a duniya, ana amfani da tsarin aikin leken asiri wajen aikin ‘yan sanda. Mun san akwai wasu kungiyoyi a Najeriya da ke da alaka da wasu kungiyoyi na kasa da kasa, don haka yana da muhimmanci mu kasance cikin shiri.”
Ya kara da cewa rundunar tana daukar matakai da dama, ciki har da kara yawan sintiri a cikin jama’a da kuma yin aiki tare da shugabannin al’umma domin hana duk wani rikici da ka iya tasowa a cikin gida.

Source: Twitter
Sakon shugaban yan sanda ga al'umma
Sabon IGP din ya kuma gargadi ‘yan Najeriya da su guji yada labaran da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, yana mai cewa yada jita-jita na iya jawo tsoro a tsakanin jama’a tare da kawo cikas ga ayyukan tsaro.
Ya bukaci jama’a su rika amincewa da bayanan hukuma kawai tare da taimaka wa ‘yan sanda da bayanan sirri masu amfani.
Hadimin Tinubu ya yi maganar yakin Iran
A wani rahoton, kun ji cewa hadimin shugaban Najeriya, Ademola Oshodi ya yi tsokaci kan yakin da ya barke tsakanin Amurka, Isra'ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Oshodiya ce galibin wadannan rikice-rikice suna samo asali ne daga muradun kasa, yana mai jaddada cewa kamata ya yi kasashen duniya su fifita dokokin kasa da kasa.
Ya ce duk da Najeriya da za ta shiga yakin ba, amma kamata ya yi Majalisar dinkin duniya ta shiga gaba domin samar da masalaha mai dorewa.
Asali: Legit.ng

