Malamai Sun Yi Magana, Sun Fadi Yadda Yakin Iran da Amurka Ya Shafi Najeriya

Malamai Sun Yi Magana, Sun Fadi Yadda Yakin Iran da Amurka Ya Shafi Najeriya

  • Wasu malaman addinin Musulunci a Najeriya sun yi taro a gidan gwamnatin Legas, inda suka yi tsokaci game da yakin da ake Gabas ta Tsakiya
  • Malaman sun gargadi 'yan Najeriya, musamman mazauna Legas da su kauce shirya zanga-zanga saboda abin da ke faruwa a wasu a kasashe
  • Shugaban limaman kungiyar kungiyar Ansar-Ud-Deen, Sheikh Abdulrahman Ahmad ya yi kira ga 'yan Najeriya su rika taka tsan-tsana a lamura

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas - Malamai sun gargadi ‘yan Najeriya, musamman mazauna Lagos, da su guji duk wani nau’i na zanga-zanga ko wani abu da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya sakamakon rikicin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya.

Kungiyar manyan limaman Juma’a ce ta yi wannan kira yayin da take jawabi a taron Tafsirin Ramadan da buda-baki na shekarar 2026 da aka gudanar a gidan gwamnatin Legas a daren Talata.

Kara karanta wannan

Khamenei: An ɗage taron jana'izar jagoran addini a Iran yayin da ake harin magajinsa

Yadda malamai suka sha ruwa a Legas
Malamai a wajen taron shan ruwa a gidan gwamnatin Legas. Hoto: Lagos State Government
Source: Facebook

Gwamnatin jihar Legas ta wallafa a X cewa malaman sun ja kunnen jama'a kada su rika tsoma baki a yaƙin da ke gudana tsakanin Iran, Isra’ila da Amurka.

Magana kan yakin Amurka/Iran

Kungiyar manyan limaman Juma’a ta bakin babban mai kula da harkokin wa’azi na kasa kuma babban limamin kungiyar Ansar-Ud-Deen, Sheikh Abdulrahman Ahmad, ta yi kira ga jama’a da su kasance cikin natsuwa da kamewa.

Ta yi magana tana tana gargadin cewa bai kamata Najeriya ta bari abubuwan da ke faruwa a duniya su haddasa tashin hankali a cikin gida ba.

Ya ce ya kamata a yi amfani da watan Ramadan wajen yin addu’o’i domin dorewar zaman lafiya a Lagos da Najeriya baki ɗaya, maimakon gudanar da zanga-zanga ko nuna rashin jin daɗi dangane da rikicin Gabas ta Tsakiya.

Matsayar limaman ta zo ne a matsayin martani ga zanga-zangar da aka gudanar a wasu sassan ƙasar, musamman wadda 'yan Shi'a suka yi a Lagos kan kashe Ayatollah Ali Khamenei.

Kara karanta wannan

Luguden wutar Iran ya jefa Amurkawa cikin tsoro, suna korafi ga Trump

Yakin Amurka/Iran ya shafi Najeriya

Malamin ya bayyana cewa abubuwan da ke faruwa a duniya a halin yanzu suna shafar Najeriya, don haka akwai buƙatar yin tunani mai zurfi, neman mafita da kuma yawaita addu’a.

Ya ce:

“Ku yi hattara da fitina; idan ta faru ba waɗanda suka haddasa ta kaɗai za ta shafa ba, har da mu baki ɗaya. Rikicin da ke Gabas ta Tsakiya fitina ce.
"Wannan lokaci ne na addu’a, lokaci ne na zama masu samar da zaman lafiya; ba lokaci ba ne na zanga-zanga da gangami. Ba lokaci ba ne na cin mutunci ko tashin hankali. Lokaci ne na yin tunani cikin natsuwa."
"A yanzu haka ma tana shafar mu baki ɗaya. Ta yaya za ta ƙare? Na gaya wa jama’a su shirya yiwuwar ƙarin farashin mai. A yau idan ka cika tankin motarka za ka san nawa ake sayar da lita.
"Wata kila ma farashin zai iya ƙaruwa har ya kai Naira 2,000 kowace lita, ko ma ya fi haka, sai dai idan muka fuskance shi da addu’a.”

Kara karanta wannan

Yadda kisan Khamenei zai shafi 'yan Shi'a a Najeriya, rashinsa ya 'hada' kan Musulmi

Malaman Legas a gidan gwamnati
Malamai a taro a gidan gwamnatin Legas. Hoto: Lagos State Government
Source: Facebook

Ya kuma gargadi mutane da su guji yaɗa farfaganda ko shiga rikice-rikicen da ba su shafi ƙasar kai tsaye ba, yana mai kira ga ‘yan Najeriya da su yi addu’a ga waɗanda rikicin ya shafa a Gabas ta Tsakiya.

Trump zai tayar da rigima a Iran

A wani labarin, kun ji cewa an samu rahoton da ke nuna cewa gwamnatin Donald Trump na shirin hada kai da Kurdawa domin tayar da rikici a Iran.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da fafatawa a tsakanin Iran da Amurka/Isra'ila tun bayan kashe Ayatollah Ali Khamenei.

An bayyana cewa a yanzu haka Trump ya fara magana da Kurdawa domin duba yadda za su taimaka wajen dauke hankalin dakarun Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng