Tinubu Ya Nada Sabon Minista bayan Cire Mace a Kujerar, an Ji Ma’aikatar da Zai Rike
- Bola Ahmed Tinubu ya nada Taiwo Oyedele a matsayin karamin Ministan kudi, bayan sauyin mukamai da ya yi a ma'aikatar
- Sanarwar ta ce Oyedele zai maye gurbin Dr. Doris Uzoka-Anite, wadda za ta koma Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsare ta Kasa
- Kafin nadin, Oyedele ya jagoranci Kwamitin Shugaban Kasa kan Manufofin Haraji da Gyaran Tsarin Haraji na Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada sabon minista a Najeriya domin kara inganta ayyukan gwamnatinsa.
Shugaban ya Taiwo Oyedele a matsayin Karamin ministan kudi domin maye gurbin Dr. Doris Uzoka-Anite da aka sauyawa ma'aikata.

Source: Twitter
Mai bai wa shugaban kasa shawara kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ta shafinsa na X a ranar Talata, 3 ga Maris, 2026.

Kara karanta wannan
Ronaldo ya lallaɓa ya bar Saudiyya saboda rikicin Isra'ila, Iran? an ji gaskiyar zance
Dalilin nada minista a ma'aikatar kudi
Hakan ya biyo bayan shirin maye gurbin Uzoka-Anite, wacce za ta koma Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsare ta Kasa a matsayin karamar minista.
Onanuga ya ce shugaba Tinubu ya aike da sunan Oyedele ga majalisar dattawa domin tantancewa. Ana sa ran ba da dade wa ba Godswill Akpabio zai karanto wasikar.
Ya kara da cewa kafin nadin nasa, Oyedele dan asalin Ikaram, Akoko ne a jihar Ondo, shi ne shugaban Kwamitin Shugaban Kasa kan Manufofin Haraji da Gyaran Tsarin Haraji.
Kwamitin ya taka muhimmiyar rawa wajen sake fasalin tsarin harajin Najeriya domin kara inganta tattalin arziki da samar da kudaden shiga.
Onanuga ya bayyana Oyedele mai shekaru 50 a matsayin masani a fannin tattalin arziki, akawu kuma kwararre kan manufofin gwamnati.
Ya ce ya shafe sama da shekaru 22 yana aiki a kamfanin 'PricewaterhouseCoopers (PwC)', inda ya samu gogewa a harkokin kudi da haraji.

Source: Twitter
Karatu da kwarewar sabon ministan a Najeriya
Oyedele ya yi karatu a Kwalejin Fasaha ta Yaba, inda ya samu Babbar Diploma ta Kasa (HND) a fannin lissafin kudi da harkokin kudi.
Haka kuma ya yi karatu a Jami’ar Oxford Brookes, inda ya samu kwalin digiri a fannin lissafin kudi na aikace.
Ya halarci shirye-shiryen manyan darussa na shugabanci a Makarantar Tattalin Arziki ta London, da Jami’ar Yale, da Cibiyar Gordon ta Kimiyyar Kasuwanci, da kuma Makarantar Harvard Kennedy.
Oyedele ya kwashe shekaru 22 yana aiki a kamfanin PwC, inda ya shiga a shekarar 2001, ya kuma kai matsayin Abokin Hulda kan Manufofin Haraji da Jagoran Haraji na Afirka.
Haka zalika, Oyedele farfesa ne a Jami’ar Babcock da ke Ogun, sannan kuma malami na wucin gadi a Makarantar koyon Kasuwancin nan ta Lagos.
Fasto ya yi hasashen Tinubu zai yi garambawul
Kun ji cewa Fasto Ayodele ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu zai yi wasu manyan sauye-sauye a gwamnatinsa kafin karshen 2026.
Ya ce sauyin shugabannin tsaro na da nasaba da shirye-shiryen zaben shugaban kasa na 2027 da ake tunkara a Najeriya domin kara inganta harkokin mulki.
Malamin ya gargadi shugabannin tsaro su shirya, yana mai cewa hukuncin ya riga ya tabbata sai dai idan Allah ya sauya, hakan na zuwa bayan Sufeto-janar na yan sanda ya yi murabus.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
