Hadimin Tinubu Ya Tsoma Baki a Yakin Iran da Amurka, Ya Tura Sako Majalisar Dinkin Duniya
- Hadimin shugaban Najeriya, Ademola Oshodi ya yi tsokaci kan yakin da ya barke tsakanin Amurka, Isra'ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran
- Oshodi, mai taimakawa Bola Tinubu kan harkokin ketare, ya ce Majalisar dinkin duniya ya kamata ta shiga gaba wajen samar da mafita
- Ya bukaci kasashen da ke cikin wannan yaki da su mutunta dokokin kasa da kasa domin warware matsalar da ke tsakaninsu cikin ruwan sanyi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ademola Oshodi, babban mataimaki na musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kan harkokin kasashen waje ya tsoma baki kan yakin da ya barke tsakanin Iran da Isra'ila, Amurka.
Oshodiya ce galibin wadannan rikice-rikice suna samo asali ne daga muradun kasa, yana mai jaddada cewa kamata ya yi kasashen duniya su maida bin dokokin kasa da kasa a sahun farko.

Kara karanta wannan
Kwana ya kare: Sarki Mai Martaba a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya a watan azumi

Source: Twitter
Hadimin Tinubu ya gano abin da ke jawo yaki
A wata hira da ya yi da tashar Arise News a ranar Litinin, Oshodi ya bayyana muhimmancin hadin gwiwar kasashen duniya wajen warware rikice-rikice, musamman bayan barkewar yaki tsakanin Iran, Isra'ila da Amurka.
“Najeriya ta dade tana taka rawa a harkar hadin gwiwar kasa da kasa. Mun yi imanin cewa duk rikice-rikice suna da alaka da muradun kasa, amma muna bin tsarin doka,” in ji hadimin shugaban kasa.
Ya kara da cewa Nijeriya na ganin ya kamata kasar Amurka ta rike girmanta, ta rika shiga gaba wajen tunkara da magance irin wadannan yake-yake idan sun taso.
Oshodi ya tura sako Majalisar Dinkin Duniya
“Muna da yakinin cewa Majalisar dinkin duniya ya kamata ta shiga gaba wajen warware kowane irin rikici idan ya taso,” in ji shi.
Oshodi ya kuma bayyana cewa Najeriya ba za ta tsoma baki a wannan yaki na Iran, Amurka da Isra'ila ba, kasancewar ba ta shiga tattaunawar shirin nukiliyar da ake yi a baya ko yanzu ba.

Kara karanta wannan
Ana tsaka da musayar wuta, Iran ta samu gagarumin goyon baya a yaki da Amurka da Isra'ila
Ya kara da cewa duk da muradun da kasashen Amurka, Isra'ila da Iran ke da su, dole ne su mutunta kudurorin da suka dace na Majalisar Dinkin Duniya.
“Dole ne mu bi tsarin da zai bai wa kowa damar gabatar da muradunsa a gaban tarukan kasa da kasa, inda kowa zai samu damar fahimtar muradunsa da na wasu,” in ji Oshodi.

Source: Twitter
A ranar Asabar, ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya sanar da kai harin riga-kafi kan Iran, yayin da daga baya Shugaban Amurka, Donald Trump, ya tabbatar da cewa Amurka ta shiga aikin.
Hare-haren sun zo ne yayin da kasashen biyu ke kokarin kawo karshen shirin nukiliyar Iran, kamar yadda tashar Al-Jazeera ta ruwaito.
Yadda yakin Iran da Amurka zai taba Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa masana harkokin makamashi sun yi gargaɗin cewa rikicin Amurka da Iran na iya jawo tashin farashin fetur da dizal a Najeriya.
Sun bayyana cewa idan farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya ya haura Dala 90 kowace ganga, lallai hakan zai shafi farashin man fetur da dizal.
Masana sun ce duk wani dogon rikici a Gabas ta Tsakiya, musamman a mashigar ruwan 'Strait of Hormuz', na iya ƙara farashin mai a duniya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng