Kotu Ta Yi Ƙwarya Ƙwaryan Hukunci game da Bukatar Tsofaffin Kwamishinonin Kano a kan Abba

Kotu Ta Yi Ƙwarya Ƙwaryan Hukunci game da Bukatar Tsofaffin Kwamishinonin Kano a kan Abba

  • Kotun Masana’antu ta Ƙasa ta ƙi ya ke hukunci a kan ƙorafin da tsofaffin kwamishinonin jihar Kano suka shigar gabanta
  • Tsofaffin kwamishinonin da suka yi murabus sun shigar da ƙara suna neman a hana gwamnatin Kano kwace motocinsu
  • Mahmood Abba Namtari ya ɗage shari’ar zuwa 10 ga Maris, 2026 domin ci gaba da sauraron ƙarar kafin a yi hukunci a kan lamarin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Kotun Masana’antu ta Ƙasa da ke zamanta a sashen shari’a na Kano ta ƙi amincewa da buƙatar wasu tsofaffin ƴan majalisar zartarwa ta jihar Kano.

Tsofaffin kwamishinonin sun shigar da kara ne suna neman kotu ta dakatar da gwamnati daga kwace motocin da aka ba su yayin da suke kan muƙami.

Kara karanta wannan

Yakin Iran: Arewacin Najeriya ya shiga yankunan da ake sa wa ido

An kai gwamnatin Kano kara gaban kotu
Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Alƙali Mahmood Abba Namtari ne ya yanke hukuncin a ranar Litinin 2 ga watan Maris, 2026 bayan nazarin buƙatun wucin-gadi da tsoffin kwamishinonin suka shigar.

Ƙorafin tsofaffin kwamishinonin jihar Kano

Daily Post ta wallafa cewa tsofaffin kwamishinonin da dama ne suka shigar da korafi iri ɗaya, lamarin da ya sa kotu ta haɗa su wuri guda domin sauraro.

Alƙalin ya ƙi bayar da umarnin wucin-gadi na hana gwamnati kwace motocin, tare da umartar a saurari shari’ar bayan an bai wa dukkanin ɓangarorin damar gabatar da hujjojinsu.

Wannan na nufin ba za a hana kowa e motocin na wucin-gadi ba sai an fara jin ta bakin gwamnati da sauran waɗanda ake ƙara.

Waɗanda aka sanya a matsayin waɗanda ake ƙara sun haɗa da Babban Lauyan Jihar Kano, Gwamnan Jihar Kano da kuma Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano.

Kara karanta wannan

Yadda Amurka da Isra'ila ke amfani da AI wajen bin diddigi da kai hari kan mutane

Tsofaffin kwamishinonin sun samu wakilci daga lauyan Suraj Sa’ed, SAN, tare da wasu lauyoyi biyar a tawagarsa inda suke ƙalubalantar gwamnati.

An dage sauraron ƙarar tsofaffin kwamishinonin Kano

Masu ƙarar, waɗanda suka yi murabus a watan Janairu 2026, sun haɗa da Dr. Yusuf Ibrahim K/Mata, tsohon Kwamishinan kimiyya da fasaha da AVM Ibrahim Umar (Rtd), tsohon Kwamishinan tsaron cikin gida.

Kotu ta dage sauraron shari'ar tsofaffin kwamishinoni da gwamnatin Kano
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Sai kuma Nasir Sule Garo, tsohon Kwamishinan ayyuka na musamman da Adamu Aliyu Kibiya, tsohon Kwamishinan Jin-ƙai da Rage Talauci da Mustapha Rabi’u Musa Kwankwaso, tsohon Kwamishinan matasa da wasanni.

Sun shaida wa kotu cewa daga baya sun samu wasiƙa daga ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano tana umartar su da su mayar da dukkanin motocin gwamnati da ke hannunsu.

Kara karanta wannan

Dan Kwankwaso da tsofaffin kwamishinoni sun kinkimo rigima da gwamnatin Abba

Sun kuma ce sun samu wasu wasiƙu daga Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa na gargadin cewa za a iya ɗaukar matakin tilastawa domin kwato kadarorin gwamnati idan ba su bi umarni ba.

Bayan sauraron korafe-korafen, kotun ta dage shari'ar zuwa ranar 10 ga Maris, 2026 domin ci gaba da sauraron ƙarar kafin a yi hukuncin a kan dambarwar.

An nunawa gwamnatin Kano yatsa

A wani labarin, mun wallafa cewa kungiyar Kwankwasiyya ta fito ta yi zarge-zarge kan gwamnatin jihar Kano da Gwamna Abba kabir Yusuf ke jagoranta bayan sauya sheka.

Kwankwasiyya ta nuna damuwa kan abin da ta kira karuwar cin zarafin 'yan adawa da gwamnatin Kano ke yi tun bayan hadewa da APC ba tare da tuna hakaccin da aka yi mata ba.

Kungiyar ta nuna cewa abin da gwamnatin ke yi na toshe bakin 'yan adawa na jawo abin kunya a idon duniya ga jihar Kano, kuma zai hana a yi adawa da ayyukanta na suka saba doka ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng