Ta Faru Ta Kare: Iran Ta Kai Hari Ofishin Netanyahu, Firaministan Isra'ila

Ta Faru Ta Kare: Iran Ta Kai Hari Ofishin Netanyahu, Firaministan Isra'ila

  • Iran ta ce makaman linzamin Kheibar da ta harba sun sauka a ofishin Benjamin Netanyahu da kuma hedkwatar sojin Isra'ila
  • Makamin Kheibar yana da gudun gaske wanda ya ninka gudun sauti sau 16, kuma ya ratsa kariyar Isra'ila ta Iron Dome
  • Kodayake Iran ta ce ta ratsa tsarin Iron Dome, hukumomin Isra'ila ba su riga sun bayyana irin asarar da harin ya janyo mata ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Iran - Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) sun yi iƙirarin ƙaddamar da hari kan Isra'ila ta hanyar amfani da makami mai linzami samfurin Kheibar.

A cewar IRGC, makaman Kheibar da ta harba sun sauka kan ofishin Firayiminista Benjamin Netanyahu da kuma hedkwatar rundunar sojin saman Isra'ila.

Iran ta kai hari ofishin Benjamin Netanyahu, a Isra'ila.
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu tsaye a wani waje da makamin Iran ya sauka a 19 ga Yunin 2025. Hoto: MARC ISRAEL SELLEM/POOL/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Iran ta kai hari ofishin Netanyahu

Kara karanta wannan

Bayan kashe 'dan kasarta, China ta maida martani kan yakin Iran da Amurka, Isra'ila

Wannan hari, wanda Iran ta kira "rukuni na 10" na hare-hare, ya afku ne a matsayin martani ga kashe jagoran ƙasar Ayatollah Ali Khamenei, in ji rahoton Economic Times.

Sanarwar ta IRGC ta ce makaman sun daki rukunin ofisoshin gwamnati a Isra'ila, kodayake Isra'ila ba ta riga ta tabbatar da girman barnar da harin ya yi mata ba.

IRGC ta ce harin ta ya mayar da hankali kan ofishin firayiminista da kuma wuraren da manyan kwamandojin sojin saman Isra'ila ke zaune, in ji rahoton The Hindu.

Iran ta kuma bayyana cewa makamin Kheibar yana da ikon ratsa dukkan na'urorin kariya na sararin samaniya, ciki har da shahararren tsarin kariya na Iron Dome.

Har yanzu dai babu wata kafar yada labarai mai zaman kanta da ta tabbatar da ko makaman sun daki inda aka nufa ko kuma irin asarar da aka yi.

Menene makamin "Kheibar" (Khorramshahr-4)?

Makamin Kheibar, wanda kuma aka sani da Khorramshahr-4, wani nau'in makami ne mai cin dogon zango da Iran ta ƙera kuma ta fitar da shi a shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Yadda Saudiyya ta kakkabo wasu makamai da Iran ta harba a yaki da Amurka

An kera shi ne musamman domin ɗaukar manyan bama-bamai zuwa wurare masu nisa sosai. Ga manyan abubuwan da makamin zai iya yi:

  • Nisa: Yana iya tafiya har na tsawon kilomita 2,000, wanda ke nufin yana iya kaiwa kowane lungu na Isra'ila da mafi yawan yankin Yammacin Asiya daga cikin Iran.
  • Ƙarfin bam: Makamin na iya ɗaukar nauyin bam da ya kai kilogiram 1,500 zuwa 1,800, wanda hakan ya sa ya zama ɗaya daga cikin makaman da suka fi nauyi a rumbun makaman Iran.
Iran ta yi amfani da makamin Kheibar wajen farmakar ofishin Netanyahu
Makami mai linzami kirar Kheibar wanda kasar Iran ta yi amfani da shi wajen farmakar ofishin Netanyahu. Hoto: Morteza Nikoubazl/NurPhoto via Getty Images
Source: Getty Images

Dabarar ratsa na'urar Iron Dome

Wani babban abin tsoro game da makamin Kheibar shi ne gudunsa wanda ya nuna yana da saurin da ya wuce na gudun sauti, kamar yadda rahoton Turkiye Today ya nuna.

Yana yin tafiyar da ta kai Mach 16 a sararin samaniya, sannan ya komo Mach 8 yayin da yake shigowa cikin iska domin sauka kan abin harinsa.

Domin guje wa kakkabowa daga na'urorin kariya kamar Iron Dome, makamin yana amfani da dabarun McG da kuma MaRV waɗanda ke canza alkiblar makamin yayin da yake kan hanya.

Kara karanta wannan

Da gaske harin Iran ya hallaka Benjamin Netanyahu? an samu gaskiyar lamarin

Wannan na nufin koda na'urar 'radar' ta gano shi, yana iya saurin karkace wa kafin ta kakkabo shi. A baya, Iran ta taba iƙirarin cewa irin waɗannan makamai sun ratsa tsarin kariyar Isra'ila har suka daki filin jirgin saman Ben Gurion.

Iran ta farmaki Dubai da kasashe 2

A wani labari, mun ruwaito cewa, an ji karar fashe-fashe a Dubai da kasashe biyu a Gabas ta Tsakiya yayin da aka shiga ta na uku ta hare-haren Iran da Amurka.

Akalla mutane hudu ne suka riga mu gidan gaskiya a kasashen UAE da Kuwait sakamakon hare-haren makaman linzamin kasar Iran.

Wannan na zuwa ne yayin da aka rahoto wasu jiragen yakin Amurka sun yi karo da juna a Kuwait, da kuma mutuwar wasu sojojin kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com