Ribadu: ICPC Ta Kwato Na'urorin Kutsen Waya a Gidan El Rufai
- Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta ce ta kwato na’urorin sauraron waya da takardun tsaro daga gidan Nasir El-Rufai
- Hukumar da ke shari'a da El-Rufa'i kan zargin sauraron wayar Mashawarcin Shugaban Kasa Nuhu Ribadu ta ce an gano kayan a Abuja
- El-Rufa'i da bakinsa ya bayyana cewa sun samu wadansu bayanai bayan sun ji abubuwan da aka tattauna a wayar Ribadu
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta a Najeriya, ICPC ta bayyana cewa ta kwato wasu na’urori da ake zargin za su iya sauraron tattaunawar waya.
Haka kuma ta ce ta samu na'urorin ne tare da muhimman takardun tsaro, daga gidan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da ke Aso Drive a Abuja.

Source: Facebook
Jaridar The Nation ta wallafa cewa a cikin takardar rantsuwa da jami’in shari’a, David Efuk, ya gabatar a gaban Babbar Kotun Tarayya ta Abuja, ICPC ta fadi yadda ta samo na'urorin.
El-Rufa'i: ICPC ta samo shaidar kutsen waya
Daily Post ta wallafa cewa shaidan ICPC ya ce hukumar ta samu umarnin kotun majistare da ke Bwari a ranar 19 ga Fabrairu, 2026.
Hukumar ta bayyana cewa umarnin ya ba ta dama na tsare El-Rufai har na tsawon kwanaki 14, wanda zai ƙare a ranar 5 ga Maris, 2026.
Hukumar ta musanta zargin tsare shi ba bisa ƙa’ida ba, tana mai cewa duk abin da ta yi ya bi matakan doka kamar yadda aka tsara.

Source: Twitter
Ta ce an gudanar da binciken gidan ne a gaban matarsa, Hadiza Isma El-Rufai, da ɗansa, Hon. Mohammed Bello El-Rufai.
A cewarta, an gano takardu masu matuƙar muhimmanci da ka iya shafar tsaron ƙasa, tare da na’urorin maganadisu da ake zargin za su iya yin kutse cikin tattaunawar waya.
ICPC na zargin El-Rufa'i da rashin hadin kai
ICPC ta kuma yi zargin cewa Nasir El-Rufai ya ƙi ba ta haɗin kai yayin tambayoyi, yana mai cewa zai yi shiru ne har sai an gurfanar da shi a kotu.
Ta ƙara da cewa wani hadiminsa da ake zargi yana da alaƙa da binciken ya fice daga ƙasar nan zuwa kasar waje.
Hukumar ta ce akwai tambayoyi kan makomar Euro miliyan 1.4, da kuma wasu kuɗi da ake zargin an fitar da su daga asusun kudin shiga na jihar Kaduna.
Hukumar ta yi zargin cewa waɗanda jimillarsu ta kai N2,158,799,199. Haka kuma, ana zargin an tura N428,122,180.18 zuwa wasu asusun da ba a bayyana ba.
Sauran zarge-zargen sun haɗa da rashin mayar da wasu kudin shiga cikin asusun TSA, da kuma karya dokar saye da sayarwa ta jihar Kaduna ta 2016.
An kuma yi zargin cewa gwamnatin da ta gabata ta karɓo bashin cikin gida da na waje mai yawa domin ayyukan raya ƙasa, amma wasu ayyukan sun tsaya duk da cewa an biya kuɗinsu.
Kotu ta ki sauraron bukatar El-Rufa'i
A baya, mun wallafa cewa babbar kotun tarayya dake Abuja ta dage shari'ar Nasir El-Rufai zuwa watan Afrilu bayan hukumar DSS ta gaza gurfanar da shi a gabanta.
Hukumar DSS ta shigar da ƙarar tsohon gwamnan ne kan zargin kutse ga wayar Nuhu Ribadu, mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro bayan kalamansa.
A wata hira da El-Rufa'i ya yi ya bayyana cewa sun samu wadansu muhimman bayanai a kan shirin da Ribadu ke yi a kansa na shirin kama shi idan ya dawo Najeriya.
Asali: Legit.ng


