Majalisar Dinkin Duniya Ta ba Gwamnati Wa’adi a Sake Nnamdi Kanu? Gaskiya Ta Fito

Majalisar Dinkin Duniya Ta ba Gwamnati Wa’adi a Sake Nnamdi Kanu? Gaskiya Ta Fito

  • Wani bidiyo a kafofin sadarwa ya yi ikirarin cewa Majalisar Dinkin Duniya ta bai wa Najeriya wa’adin kwanaki 60 game da Nnamdi Kanu
  • Bincike ya gano babu wata hujja da ke nuna cewa UN ta kafa wa’adi ko ta tura batun ga Kwamitin Tsaro
  • Hukumar UNWGAD na bayar da shawarwari ne kawai, ba ta da ikon tilasta wa kasa sakin wanda aka tsare

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - An yi ta yada wasu rahotanni game da tsoma bakin Majalisar Dinkin Duniya kan hukuncin da aka yi wa Nnamdi Kanu.

Wani rubutu da bidiyo da aka wallafa a kafofin sadarwa sun yi ikirarin cewa Majalisar Dinkin Duniya (UN) ta ba gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 60 domin saki shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.

An karyata rahoton cewa Majalisar Dinkin Duniya ta ba gwamnati wa'adi kan Kanu
Shugaba Bola Tinubu da Nnamdi Kanu da aka tura gidan yari. Hoto: @DOlusegun, STEFAN HEUNIS.
Source: Getty Images

Sai dai binciken da TheCable ta yi kan rahoton da ake yadawa ta gano kwata-kwata babu gaskiya a labarin.

Kara karanta wannan

Najeriya ta cire tsoro ta karyata rahoton Amurka kan Kiristoci

Rahoton da ake yadawa kan Nnamdi Kanu

A rahoton da ake yadawa, an ce Hukumar UN mai kula da tsare-tsare ba bisa ka’ida ba (UNWGAD) ta mika batun ga Kwamitin Tsaro na Majalisar da ma Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka bayan Najeriya ta gaza sakin Kanu daga gidan yari na Sokoto.

Bidiyon mai tsawon minti biyar da dakika takwas, wanda shafin Selected TV ya wallafa, ya samu dubban masu martani da kuma wadanda suka yada shi.

Muryar namiji na bayyana cewa wa’adin kwanaki 60 ya kare, kuma saboda gwamnatin ta kasa sake shi a gidan yari, Majalisar Dinkin Duniya ta fara aiwatar da matakin hukunta rashin bin umarni.

Ana yada jita-jitar cewa Majalisar Dinkin Duniya ta tsoma baki kan shari'ar Kanu
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Kanu: An karyata wa'adin Majalisar Dinkin Duniya

Binciken ya nuna babu wata shaida a shafin Majalisar Dinkin Duniya da ke nuna an kafa sabon wa’adi ko an tura karar Najeriya zuwa Kwamitin Tsaro kan batun Kanu.

Tun kafin a yanke masa hukunci, UNWGAD ta fitar da ra’ayi mai lamba 25/2022 inda ta ce kama da tsare Kanu ya saba ka’ida, tare da ba da shawarar a sake shi kuma a biya diyya.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sanya har yanzu hukumar EFCC ba ta gurfanar da Nasir El Rufai ba

Amma ra’ayoyin wannan hukuma ba su da karfin doka da za su tilasta wa kasa sakin wanda aka tsare, kuma ba ta da ikon kafa wa’adi ko kakaba takunkumi kai tsaye.

Haka kuma babu wata shaida da ke nuna cewa Amurka ta sanar da kakaba takunkumi ko kwace kadarorin Najeriya bisa wannan batu.

Dangane da girman zargin, duk wani matakin hukuma daga Majalisar Dinkin Duniya zai jawo rahotanni daga manyan kafafen yada labarai na duniya.

Don haka, ikirarin cewa Majalisar Dinkin Duniya ta tilasta wa Najeriya sakin Nnamdi Kanu ta hanyar wani mataki na doka ba gaskiya ba ne.

Yan Biafra sun hadu da dan majalisar Amurka

A baya, an ji cewa haramtacciyar kungiyar IPOB ta ce hadin kan Najeriya bai kare Kiristoci daga hare-hare ba fiye da shekaru 60 da aka dade ana fama da su.

IPOB ta bayyana cewa matsalar tsaro a Najeriya ta samo asali ne daga tsarin kasa da aka gada tun mulkin mallaka da Turawa suka yi a kasar.

Kungiyar ta yi magana ne bayan dan majalisar Amurka da ya zo Najeriya, Riley Moore ya bayyana cewa ba ya goyon bayan raba Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.