Sheikh Gumi Ya Ragargaji Amurka kan Neman Soke Shari'a a Najeriya, Ya Ce ba Ja da Baya

Sheikh Gumi Ya Ragargaji Amurka kan Neman Soke Shari'a a Najeriya, Ya Ce ba Ja da Baya

  • Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi wa kasar Amurka raddi game da maganar shari'a
  • Ya bayyana cewa maganar da ake cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya ba gaskiya ba ne, ya ce har daga kasashen waje an karyata hakan
  • A sakon da ya fitar, malamin ya bayyana cewa dole 'yan siyasar Najeriya su hada kai wajen yaki da kudirin da 'yan majalisar Amurka suka gabatar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Fitaccen malamin addinin Musulunci, Dr Ahmad Abubakar Gumi, ya yi magana kan Shari’a a Najeriya, yana mai cewa haƙƙi ne na Musulmi, kamar yadda Amurka ke kare muradun Kiristoci.

Sheikh Gumi na mayar da martani ne kan rahotannin da ke cewa wasu ’yan majalisar dokokin Amurka sun miƙa wa shugaba Donald Trump, inda suka buƙaci a soke shari’a da dokokin batanci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Najeriya ta cire tsoro ta karyata rahoton Amurka kan Kiristoci

Sheikh Ahmad Gumi yana wa'azi
Sheikh Ahmad Gumi yana yi wa jama'a wa'azi. Hoto: Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Facebook

Martanin Ahmad Gumi ga kasar Amurka

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, malamin ya bayyana cewa al'ummar Musulmi na da ’yancin su tafiyar da rayuwar su bisa koyarwar addininsu.

Malamin ya ce:

“Shari’a haƙƙi ne na Musulmi kamar yadda Amurka ta ga ya dace ta kare Kiristoci kawai,”

Magana kan ta'addanci a Najeriya

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Malamin ya ce Musulmi ne mafi yawan waɗanda matsalar rashin tsaro ta shafa amma kuma Amurka na cewa za ta shigo kasar domin kare Kiristoci.

“A lokaci guda kuma, Musulmi ne mafi yawan waɗanda ke fama da wannan ɓoyayyen ta’addancin da aka shigo da shi cikin ƙasa”

In ji Gumi.

A wani saƙon dabam, malamin ya yi tambaya kan abin da ya kira fuska biyu a tattaunawar duniya kan addini da shugabanci.

Ya ce:

“Gwamnatin Amurka ta goyi bayan Isra’ila ta rayu bisa tsarin addininta, amma ya zama haram Musulmi su rayu bisa koyarwar Alƙur’ani,”

Kara karanta wannan

Zargin kashe Kiristoci: Matakai 6 da ake son Trump ya ɗauka a kan Najeriya

Shugaban Amurka, Donald Trump
Donald Trump yayin yi wa Amurkawa jawabi a taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Maganar kai hari Iran daga Amurka

Sheikh Ahmad Gumi ya yi zargin cewa Amurka na dar-dar wajen kai hari Iran ne saboda yawan man da jiragen kasar za su bukata wajen zirga-zirga.

Malamin ya ce Amurka na fargabar Iran za ta iya toshe mashigar Harmouz domin hana shigar mata da mai daga kasashen Larabawa idan aka fara yakin.

A bidiyon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sheikh Ahmad Gumi ya ce saboda haka ne Amurka ta shiga Venezuela mai arzikin mai, yanzu kuma ta shiga Najeriya.

Najeriya ta karyata zargin Amurka

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta yi martani game da wani rahoto da 'yan majalisar Amurka suka mikawa Donald Trump.

Rahoton ya kunshi zargin kisan Kiristoci da ya bukaci Trump ya dauki wasu matakai a Najeriya ciki har da bukatar soke Shari'ar Musulunci.

Ministan yada labaran Najeriya, Mohammed Idris ya bayyana cewa abin da 'yan majalisar suka fada a cikin rahoton ba gaskiya ba ne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng