Yadda Ƴan Bindiga Suka Kashe Mutane 50, Suka Ƙone Gari Guda Ƙurmus a Zamfara
- 'Yan bindiga sun babbake kusan dukkanin gidajen garin Dutsin Dan Ajiya dake jihar Zamfara tare da kashe akalla mutane 50
- Shugaban karamar hukumar Anka, wanda ya tabbatar da harin, ya bayyana cewa 'yan bindigar sun toshe kofofin tsira ga jama'a
- An rahoto cewa mazauna garin sun yi ta maza, sun fafata da yan bindigar har na tsawon sa'o'i uku kafin harsashin su ya kare
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Zamfara – Wasu ’yan bindiga da suka kai mummunan hari ƙauyen Dutsin Dan Ajiya da ke Ƙaramar Hukumar Anka a jihar Zamfara, sun ƙona kusan dukkan ƙauyen tare da kashe aƙalla mutum 50.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Anka, Bashir Musa Anka, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa da manema labarai a ranar Litinin.

Source: Getty Images
Yadda aka kai hari a kauyen Zamfara
Mazauna yankin sun ce maharan sun toshe dukkan hanyoyin shiga da fita domin hana jama’a tserewa, sannan suka riƙa harbi ba kakkautawa, lamarin da ya haddasa firgici da gudun ceton rai, in ji rahoton Daily Trust.
Bashir Musa Anka ya ce mazauna ƙauyen sun yi artabu da ’yan bindigan daga misalin ƙarfe 3:00 na rana zuwa 6:00 na yamma, amma bayan alburusansu sun ƙare, maharan suka samu rinjaye kansu.
Ya ƙara da cewa dukkan rumbunan ajiyar hatsi na ƙauyen sun ƙone su, tare da lalata kusan kashi biyu cikin uku na gidaje da dukiyoyi.
Hare-hare sun yi ƙamari a Anka ta Yamma
Shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana cewa matsalar tsaro ta daɗe tana addabar yankin Anka ta Yamma, inda cikin watanni biyu da suka gabata aka samu hare-hare makamantan haka.
Yankunan da hare-haren ya fi shafa a dan tsakanin nan su ne Barayar Zaki, Waramu, Matsifi da ma ƙauyen Tungar Nagode, in ji Bashir Anka.
Malam Bashir Anka ya yi kira ga Gwamna Dauda Lawal da ya gaggauta daukar mataki tare da kai agajin gaggawa ga garuruwan da abin ya shafa.
Mazauna Zamfara na ƙorafi kan rashin tsaro
Wani mazaunin yankin, Malam Shafi’u Anka, ya ce ƙauyen mai gidaje tsakanin 160 zuwa 200 ya koma kufai, inda gidan mai unguwa da masallaci kaɗai suka tsira.
Ya ce an rawaito harin ya biyo bayan ƙin amincewar mazauna ƙauyen su sasanta da ’yan bindigar da suka farmake su, in ji rahoton Punch.

Source: Original
Hakazalika, Abdullahi Sani, mai shekaru 41, ya ce an kashe masa ’yan uwa uku a harin.
“Babu wanda ya yi barci jiya, duk muna cikin raɗaɗin abin da ya faru,” in ji Abdullahi.
A cewarsa, mazauna yankin sun sanar da jami’an tsaro da hukumomin yankin lokacin da suka hango sama da babura 150 ɗauke da maharan, amma ba su samu wani taimako ba.
Wani ɗan majalisar da ke wakiltar Bukkuyum ta Kudu, Hamisu Faru, ya ce maharan sun mamaye ƙauyen tun misalin ƙarfe 5:00 na yammacin Alhamis har zuwa kusan 3:30 na asubahin Juma’a, suna ƙona gine-gine tare da harbin mutanen da suka yi ƙoƙarin tserewa.
An kashe mutane a kauyen Ware
A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kashe mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba yayin wani hari da suka kai a Zamfara.
An tabbatar da mutuwar mutane 11 biyo bayan wani hari da 'yan bindiga suka kai a kauyen Ware da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.
Ɗan majalisar dokokin jihar Zamfara mai wakiltar mazaɓar Tsafe ta Yamma, Amiru Ahmad Keta, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


