Najeriya Ta Cire Tsoro Ta Karyata Rahoton Amurka kan Kiristoci

Najeriya Ta Cire Tsoro Ta Karyata Rahoton Amurka kan Kiristoci

  • Gwamnatin Najeriya ta yi martani game da wani rahoto da 'yan majalisar Amurka suka hada da ya shafi rashin tsaro a wasu sassan kasar nan
  • 'Yan majalisar sun hada rahoton ne bisa zargin musgunawa Kiristoci da suka ce ana yi a Najeriya inda suka mika shi ga shugaba Donald Trump
  • Biyo bayan lamarin, Najeriya ta bayyana cewa babu wani tsangoma ko musguna wa da ake yi wa wasu saboda addini a wani yanki na kasar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin tarayya ta jaddada matsayarta cewa babu abin da ya shafi tsangwamar addini a Najeriya.

Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan yayin da yake mayar da martani kan rahoton da wasu ’yan majalisar dokokin Amurka suka miƙa wa shugaba Donald Trump.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya ragargaji Amurka kan neman soke shari'a a Najeriya, ya ce ba ja da baya

Donald Trump da Bola Ahmed Tinubu
Donald Trump a hagu da Bola Ahmed Tinubu a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Getty Images
Source: Getty Images

Legit Hausa ta tattaro bayanai game da martanin da Najeriya ta yi ne a wani sako da ma'aikatar yada labarai ta wallafa a shafinta na X.

Martanin Gwamnatin Najeriya ga Amurka

Bayan rahoton da Amurka ta fitar, Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya bayyana karara cewa babu wani tsarin gwamnati da ke ƙarfafa tsangwama saboda addini.

Ministan ya ce Najeriya ta sha bayyana cewa babu wata ƙungiyar addini da ake kai wa hari a cikin matsalar rashin tsaro da ta addabi ƙasar.

Ya ce:

“Gwamnatin tarayyar Najeriya ta lura da sabbin bayanai da shawarwari da suka fito daga tattaunawa a majalisar dokokin Amurka,
"Waɗanda ke cikin rahoton haɗin gwiwa kan tsangwamar Kiristoci a Najeriya da kwamitin harkokin waje da na kasafin kuɗi na majalisar wakilai suka miƙa wa fadar White House dangane da halin tsaro a Najeriya."

Martani kan tsangwamar Kiristoci

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa gwamnatin Najeriya ta ki yarda da ikirarin 'yan majalisar Amurka na cewa ana nunawa Kiristoci wariya a kasar.

Kara karanta wannan

Zargin kashe Kiristoci: Matakai 6 da ake son Trump ya ɗauka a kan Najeriya

Ta ce:

“Najeriya ta amince cewa wasu sassan ƙasar na fuskantar manyan ƙalubalen tsaro, ciki har da ta’addanci, fashi da makami, da rikice-rikicen ƙabilanci da suka shafi al’umma da dama.
"Gwamnatin narayya na matuƙar damuwa kan asarar rayuka da dukiya sakamakon hakan, kuma muna miƙa ta’aziyya ga dukkan waɗanda abin ya shafa da iyalansu, ba tare da la’akari da addini, ƙabila ko yanki ba.
“Yana da muhimmanci a bayyana a sarari cewa Najeriya ba ta da, kuma ba ta taɓa samun, wani tsarin gwamnati na tsangwamar addini ba.
Rikice-rikicen da hukumomin tsaro ke fuskanta ba su samo asali daga manufar gwamnati ko son kai na addini ba, sai dai daga rikitarwa na barazanar tsaro da suka haɗa da ta’addanci,"
Ministan yada labaran Najeriya
Ministan yada labarai, Mohammed Idris na bayani a taro. Hoto: @FMINONigeria
Source: Twitter

Donald Trump ya zagi alkalan Amurka

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Donald ya zagi manyan alkalan Amurka kan hana shi sanyawa kasashen duniya haraji ciki har da Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda masu jin Faransanci sun shigo Najeriya suna kashe mutane

Kotun kolin Amurka ta yi hukuncin da ya soke wasu matakai da Donald Trump ya dauka a shekarar 2025 game harkokin wajen kasar kan haraji.

Bayan zagin da ya yi wa alkalan, Shugaba Trump ya bayyana cewa zai cigaba da lafta wa kasashe haraji ta wasu hanyoyin da yake da su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng