Yadda Gobara a Kasuwannin Kano a cikin Watanni 2 ta Kassara Jarin sama da Naira biliyan 6
Farkon shekarar nan ta 2026 ta zo wa ƴan kasuwa a Kano da mummunar jarrabawa ta gobara a lokuta da dama. A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Kano – An samu gobara akalla uku a cikin ƙasa da watanni biyu a Kano, lamarin da ya jefa ƴan kasuwa a cikin halin ni ƴa su. A kasuwar Singer da ta shahara wajen sayar da kayan masarufi na yau da kullum kawai, an yi gobara sau biyu a ƙasa da wata biyu.

Source: Original
Sanarwar da Sanusi Bature D-Tofa, hadimin gwamnan Kano ya wallafa a shafinsa na Facebook ya tabbatar da faruwar gobarar a ranar 2 ga watan Fabrairu, 2026. Legit ta tattaro gobarar da aka yi a kasuwannin Kano tare da irin asarar da aka tafka a wannan ɗan tsakani.

Kara karanta wannan
NOA ta gargadi 'yan kasuwa, ta gano abubuwa 2 da za su kawo wahala a watan Ramadan
Manyan gobara 3 da aka yi a Kano
1.Gobara a kasuwar Singer
A cikin daren 2 ga watan Fabrairu na shekarar 2026, an samu wata mummunar gobara da ta tashi a tsakar dare a kasuwar Singer. A wata sanarwa da Darakta janar kan yada labaran gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna ya jajanta wa yan kasuwa.

Source: Facebook
Gwamnan ya ce gwamnatin jihar na tare da ‘yan kasuwar a wannan hali na ƙunci, musamman ganin yadda gobarar ta lalata kayayyaki da darajarsu ta kai daruruwan miliyoyin Naira.
Gwamnan ya umarci hukumomin da abin ya shafa, musamman Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano da sauran jami’an tsaro, su ƙara kaimi wajen ɗaukar matakan rigakafin gobara a kasuwar.
2. Gobara a Singer karo na 2
Ba a gama jimamin gobarar farko ba, sai wata mummunar wuta ta sake tashi a kasuwar Singer a ranar 14 ga Fabrairu, 2026, inda ta haddasa mummunar asara.
Channels TV ta wallafa cewa Shugaban kasuwar, Junaid Zakari, ya bayyana lamarin a matsayin ɗaya daga cikin mafi muni a tarihin kasuwar.
Ya ce:
“Wannan na daga cikin mafi munin abu da muka fuskanta a kasuwar Singer. An yi asarar dukiyoyi da darajarsu ta haura N5bn.”
Ya ƙara da cewa sama da shaguna 'yan kasuwa akalla 1,000 ne gobarar ta shafa, lamarin da ya jefa daruruwan iyalai cikin matsin rayuwa.
Junaidu Zakari ya yaba da yadda jami’an kashe gobara da na tsaro suka gaggauta isa wurin, yana mai cewa duk da haka, asarar ta riga ta yi yawa.
Shugaban kasuwar ya buƙaci gwamnatin jiha da jama’a su kawo ɗauki domin taimaka wa ‘yan kasuwar da abin ya shafa su farfaɗo da sana’o’insu.
3. Gobarar kasuwar Dakata
Yayin da ake jimami tare da takaicin gobara biyu a kasuwa guda, sai kwatsam aka hi tashin wata gobarar Fatima da ke kwanar Dakata a Kano.
Gobara ta lalata kusan shaguna 100 kuma ta ci daga tsakar dare har wayewar garin Allah a ranar 20 ga watan Fabrairu, 2026. A wata sanarwa hukumar Kashe gobara ta Kano ta fitar, ta ce ta samu kiran gaggawa daga wani mai suna Mista Joseph kan tashin gobarar.

Kara karanta wannan
DSS na shirin gayyatar yaran El Rufa'i, matar Dadiyata ta yi magana kan dauke mijinta

Source: Facebook
An tura jami’an kashe gobara daga hedkwatar hukumar, tashar Dakata da tashar Rijiyar Zaki domin shawo kan lamarin. Da suka isa wurin, sun tarar da cibiyar masana’antar mai faɗin kafa 300 da 200 ta kama da wuta. An kiyasta cewa a wannan kasuwa, an tafka asarar kuɗi tsakanin Naira miliyan 700 zuwa Naira miliyan 800.
Gobara ta tashi a filin jirgi
A baya, mun wallafa cewa hukumar FAAN ta tabbatar da tashin gobara a wani sashen filin jirgin sama na Muratala Muhammed da ke jihar Legas a karshen mako.
Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta kama a wani bangaren da ake yi wa gyara domin sabunta shi da nufin inganta walwalar fasinjoji, sai dai lamarin ya zo da sauki.
FAAN ta kwantar da hankulan fasinjoji da ke kai komo a filin jirgin, inda ta ce babu wanda ya rasa ransa sakamakon gobarar kuma tuni aka samu nasarar shawo kanta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
