Bala da Gwamnonin da ba Su Samu Zuwa Buda Bakin da Tinubu Ya Kira a Aso Rock ba

Bala da Gwamnonin da ba Su Samu Zuwa Buda Bakin da Tinubu Ya Kira a Aso Rock ba

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi buda baki da wasu daga cikin gwamnonin jihohi a Fadar Gwamnati da ke Abuja a ranar 23 ga watan Fabrairu, 2026.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya fara buda baki da gwamnoni da 7.00 na yamma a Aso Rock.

Wannan shi ne karo na uku a jere da shugaban kasar ke gayyatar gwamnonin jihohi domin irin wannan taro na musamman a Aso Rock Villa.

Tinubu ya sha ruwa da wasu gwamnonin Najeriya
Gwamna Umaru Dikko Radda (hagu), Bala Mohammed na Bauchi (dama) da wasu gwamnoni a buda baki da Tinubu (tsakiya) Hoto: Umaru Dikko Radda/Gov Abdullahi A. Sule Mandate/Sen Bala AbdulKadir Mohammed
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa taron an ya samu halartar gwamnonin Najeriya, sai dai ba dukkaninsu ne suka je ba.

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya halarci zaman tare da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila.

Kara karanta wannan

Sheikh Murtala Asada ya yi fatali da neman yafiyar Tinubu, ya jero dalilansa

Gwamnonin da aka yi buda baki da su

Wasu daga cikin gwamnonin Najeriya sun halarci taron shan ruwa da Shugaba Tinubu yayin da aka kai azumi na shida.

1. Abba Kabir Yusuf na jihar Kano

2. Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa

3.Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba

4.Gwamna Alex Otti na jihar Abia

5. Gwamna Uba Sani na Kaduna

6. Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo

7. Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun

8. Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo

9.Gwamna Ahmed Usman Ododo na jihar Kogi

10. Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno

11. Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe

12. Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sakkwato

13. Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta

14. Gwamna Mohammed Umaru Bago na jihar Neja

15. Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa

16. Gwamna Francis Nwifuru na Ebonyi

A jawabinsa da ya wallafa a shafin Facebook bayan shan ruwan, Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce wannan ne karo na uku da Tinubu ke irin wannan taro a Aso Rock.

Kara karanta wannan

Abin da Tinubu ya gayawa Gwamna Abba yayin buda baki da gwamnoni

Wasu gwamnoni sun sha ruwa a Abuja
Shugaba Bola Tinubu (tsakiya), Kashim Shetiima daga hagu ga Tinubu da wasu gwamnonin Najeriya Hoto: Gov Abdullahi A Sule Mandate
Source: Facebook

Shi kuwa Umaru Bago na jihar Neja ya bayyana cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yaba da yadda gwamnatinsa ke aiki da gaske a jihar.

A sakon da hadiminsa a kan yada labarai, Bologi Ibrahim ya wallafa a Facebook, ya ce Tinubu ya nemi da ya kara hazaka wajen yi wa jama'ar da suka zabe shi aiki.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu halartar buda bakin kwanaki kadan bayan ya rabu da jam'iyyarsa ta NNPP zuwa APC.

Gwamnonin da ba su sha ruwa da Tinubu ba

Wasu gwamnonin kasar nan ba su samu damar halartatar taron buda bakin ba duk da guda daga cikinsu, Bala Mohammed na Bauchi ya aika mataimakinsa.

Wasu gwamnoni ba su yi buda baki da takwarorinsu da Tinubu a Abuja ba
Shugaban Najeriya Bola Tinubu yayin buda baki da wasu daga cikin gwamnonin Najeriya Hoto: Gov. Abdullahi A Sule Mandate
Source: Facebook

Gwamnonin da ba su sha ruwa da Tinubu ba sun hada da:

1. Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri

2. Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno

3.Gwamnan Katsina, Dikko Radda

4. Gwamnan Anambra, Charles Soludo

5. Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed

Kara karanta wannan

Buda baki: Shugaba Tinubu ya sha ruwa tare da wasu gwamnoni a watan Ramadan

6. Gwamnan Benua, Hyacinth Alia

7. Gwamnan Bayelsa, Douye Diri

8. Gwamnan Kuros Riba, Bassey Out

9. Gwamnan Kwara, Abdulrazaq Abdul

10. Gwamnan Ekiti, Biodun Oyebanji

11. Gwamnan Legas, Babajide Sanwo Olu

12. Gwamnan Filato, Caleb Muftwang

13. Gwamnan Ondo, Lucky Orimisan Aiyedatiwa

14 Gwamnan Oyo, Seyi Makinde

15. Gwamnan Osun, Ademola Adeleke

16. Gwamnan Ribas, Simi Fubara

17. Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni

18. Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal

Ba a kai ga sanin abin da ya hana gwamonin zuwa taron buda bakin ba, sai dai akwai rashin jituwa musamman a tsakanin gwamnonin PDP biyu Seyi Makinde da Bala Muhammad da Shugaba Bola Tinubu.

Haka kuma a yan makonni da suka gabata, Gwamna Dauda Lawan ya zargi Shugaban kasa da hana jiharsa kudin tallafi da ake ba wa jihohi saboda sabanin ra'ayin siyasa.

Dalilin Tinubu na amincewa da dokar zabe

A baya, mun wallafa cewa Sanata Opeyemi Bamidele ya kare gaggawar da Bola Ahmed Tinubu ya yi na rattaba hannu kan dokar gyaran zaben Najeriya ta 2026.

Kara karanta wannan

Kano: Sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jawo tarnaki a jam'iyyar APC

Shugaban masu rinjaye a Majalisar dattawan ya ce babu dalilin da zai sa shugaban kasa ya yi jinkirin zartar da dokar bayan Majalisa ta amince da shi bayan an duba ta da kyau.

Sanata Opeyemi Bamidele ya bayyana cewa sabuwar dokar zaben za ta kara inganta harkokin zaben Najeriya ta yadda 'yan kasa za su gamsu gabanin 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng