Musulmi na Korafi kan Shugaban INEC, Manyan Malaman Coci Sun Mika Bukata ga Majalisa
- Kungiyar Limaman Cocin Katolika ta Kasa (CBCN) ta bukaci Majalisar tarayya ta sake nazari kan kudirin dokar zaben da ta amince da shi a 2026
- Malaman addinin sun ce bai kamata Majalisar ta zama mai magana biyu ba kan amfani da fasahar zamani a dokokinta
- A cewarsu, duba da yadda mutane suka fara kauracewa fitowa kada kuri'a, ya kamata Majalisa ta wajabta tura sakamako ta intanet kai tsaye
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ƙungiyar Manyan Limaman Katolika ta Najeriya (CBCN), ta bukaci Majalisar Tarayya ta gaggauta sake nazari game da gyaran dokar zaɓe, musamman batun wajabta aika sakamakon zaɓe kai tsaye ta intanet.
Wannan na zuwa ne makonni kadan bayan Majalisar shari'a ta Najeriya ta nemi a tsige shugaban hukumar zabe ta kasa, (INEC), Farfesa Joash Amupitan.

Kara karanta wannan
A karshe, an ji dalilin da ya sa Tinubu ya yi gaggawar sa hannu a sabuwar dokar zaben Najeriya

Source: Facebook
Bukatar da limaman coci suka aika Majalisa
Sai dai a nata bangaren kungiyar limaman cocin Katolika ta bukaci Majalisar dattawa ta sake komawa ta duba yiwuwar wajabta tura sakamakon zabe ta intanet, kamar yadda The Cable ta rahoto.
Shugaban Cocin Katolika na Owerri kuma shugaban CBCN mai barin gado, Lucius Ugorji, ne ya yi wannan kira a ranar Lahadi yayin zaman buɗe taron farko na 2026 a Sakatariyar Katolika ta Najeriya da ke Abuja.
Da yake jawabi, Ugorji ya nuna damuwa kan abin da ya kira “raguwar yawan masu kaɗa ƙuri’a a hankali” a zaɓuɓɓukan ƙasa.
Ya ce yawan fitowar masu zaɓe ya sauka daga kashi 69 cikin ɗari a 2003 zuwa mafi ƙanƙanta na kashi 23 cikin ɗari a 2023.
Ya ce wannan koma baya na nuna yadda amincewar jama’a da tsarin zaɓe ke raguwa, lamarin da ke jefa tantama kan sahihancin shugabannin da aka zaɓa, musamman idan ƙalilan ne ke ba su kuri’a.

Kara karanta wannan
Magana ta fito: Shugaba Tinubu ya fadi dalilin sanya hannu a dokar zabe duk da korafe korafe
Bukatar aika sakamako ta na'ura
Ugorji ya ce domin dakatar da wannan koma baya, dole ne dokar zaɓe ta wajabta aika sakamakon zaɓe kai tsaye daga na’urar tantance masu zaɓe ta BVAS zuwa manhajar duba sakamako ta INEC (IReV).

Source: Facebook
Limamin cocin ya kuma soki abin da ya kira rashin daidaito a dokokin da Majalisar tarayya ke yi, yana mai kafa hujja da dokar haraji ta 2025, kamar yadda Punch ta kawo.
Ya ce Majalisa ta amince da Dokar Haraji ta 2025 wadda ta wajabta amfani da tsarin fasahar zanani wajen adana bayanai, amma kuma ta gaza wajbta tsarin fasaha na tura sakamakon zabe.
“Bai kamata 'yan Majalisa su bari a ɗauke su a matsayin masu magana biyu. Duniya na kallo, kuma sama da komai, Allah ma na kallo,” in ji shi.
Dalilin gaggawar sa hannu a dokar zabe
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Opeyemi Bamidele ya kare gaggawar da Bola Ahmed Tinubu ya yi na rattaba hannu kan dokar gyaran zaben Najeriya ta 2026.
Idan ba ku manta ba shugaban kasa ya sa hannu kan dokar zabe cikin sa’o’i 24 kacal bayan Majalisar Dokoki ta ƙasa ta amince da ita, lamarin da ya haddasa ce-ce-ku-ce.
Sai dai shugaban masu rinjaye a Majalisar dattawan ya ce hakan ba abin mamali ba ne, domin akwai kyakkyawar alaka da hadin kai tsakanin masu da tsaki kan dokar zabe.
Asali: Legit.ng
