'An Kashe Mutane 10,' Zanga Zanga Ta Barke a Filato, An Rufe Wata Babbar Hanya
- 'Yan bindiga sun kashe mutane 10 a hare-haren da suka kai kauyukan Jol da Dorowa Babuje a kananan hukumomin Riyom da Barkin Ladi
- Matasa da mata a jihar Filato sun toshe babban hanyar Jos domin yin zanga-zangar nuna bacin rai kan kisan mutane 10 da aka yi
- Shugaban kungiyar BYMA ya yaba bayyana yadda 'yan bindigar suka kai hare-hare a garuruwan duk da an ankarar da sojoji
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Amurka - Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin Amurka ta kara sunayen wasu 'yan Najeriya 19 a cikin jerin sunayen masu aikata laifuffuka mafi muni a kasar.
Filato - Wasu fusatattun ƴan bindiga sun kai hare-hare a yankunan Jol da ke ƙaramar hukumar Riyom da kuma Dorowa Babuje a ƙaramar hukumar Barkin Ladi ta Jihar Filato.
Wannan hari da aka kai tsakanin ƙarfe 8:00 zuwa 9:00 na daren Lahadi, ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane 10 tsakanin daren jiya da safiyar Litinin.

Source: Original
An kashe mutane 10 a Filato
Shugaban ƙungiyar matasan Berom (BYMA), Lauya Solomon Dalyop, ya shaidawa Channels TV cewa an kashe mutane tara a Dorowa Babuje, yayin da mutum ɗaya ya rasa ransa a garin Jol .
Dalyop ya bayyana cewa maharan da suka farmaki Jol sun zo ne a kan babura daga yankin Manga, duk da cewa an ankarar da jami'an tsaro tun da wuri.
Sai dai jami'an tsaron "Operation Rainbow" sun yi nasarar fatattakar maharan, wanda hakan ya rage yawan asarar rayukan da aka yi a yankin.
A Dorowa Babuje kuwa, maharan sun fito ne daga yankin Jong-Wereh inda aka yi imanin sun daɗe suna yin sansani a can.
Zanga-zanga ta barke a Filato
Sakamakon waɗannan kashe-kashe, matasa da mata a ƙaramar hukumar Barkin Ladi sun fito zanga-zanga a safiyar Litinin inda suka toshe babban hanyar da ta kai birnin Jos.
Masu zanga-zangar sun lashi takobin cewa ba za su buɗe hanyar ba har sai an kamo waɗanda suka aikata wannan danyen aiki an hukunta su.
Rahoton jaridar The Cable ya nuna cewa an tsinci ƙarin gawarwaki guda biyu a Dorowa Babuje a safiyar yau, yayin da wasu mutane uku ke kwance a asibiti sakamakon raunuka masu tsanani.

Source: Twitter
Babu martani daga jami'an tsaro
Wannan lamari ya jefa tsoro da fargaba a zukatan mazauna yankunan, waɗanda ke kiran gwamnati da ta ƙara ƙarfafa tsaro yanzu.
Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, kakakin rundunar ƴan sandan Jihar Filato, Alfred Alabo, bai amsa kiran waya ba domin jin ta bakin rundunar game da hare-haren.
Rundunar soji da sauran jami'an tsaro suna ci gaba da sintiri a yankunan domin dawo da doka da oda da kuma lallashin masu zanga-zanga su buɗe hanya.
An kashe Fulani a Filato
Tun da fari, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kashe Fulani makiyaya tare da sare kan daya daga cikinsu a hanyarsu ta komawa gida daga sauraron tafsiri.
Kungiyar Miyetti Allah ta yi zargin cewa 'yan kabilar Berom ne suka kai harin, yayin da su kuma matasan Berom suka musanta zargin.
Rundunar soji ta Operation Enduring Peace ta tabbatar da faruwar lamarin sannan ta bayyana matakan da ta dauka na ganin an kamo 'yan ta'addar.
Asali: Legit.ng

