Sojoji Sun Cafke Mai Kawo Jirage ga 'Yan Ta'adda, An Kashe Kwamandan Boko Haram

Sojoji Sun Cafke Mai Kawo Jirage ga 'Yan Ta'adda, An Kashe Kwamandan Boko Haram

  • Dakarun sojoji na rundunar Operation Hadin Kai sun samu nasarori a yakin da suke yi da 'yan ta'adda a yankin Arewa maso Gabas
  • Sojojin sun samu nasarar cafke wani tsohon mutum wanda ke samarwa da 'yan ta'adda jirage marasa matuka
  • Hakazalika, sojojin sun samu nasarar hallaka wani kwamandan Boko Haram bayan shirya masa harin kwanton bauna

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadin Kai (OPHK) sun tsananta farmaki kan ’yan ta’addan Boko Haram a jihohin Adamawa da Borno.

Dakarun sojojin sun yi nasarar kama masu taimaka wa miyagun, kashe wasu ’yan ta’adda, da kuma ƙwace makamai da jirage marasa matuka da ake amfani da su wajen kai wa jami’an tsaro hari.

Sojoji sun samu gagarumar nasara kan 'yan ta'adda
Shugaban sojojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Juma’a, 20 ga watan Fabrairun 2026 wadda jami’in yaɗa labarai na rundunar OPHK, Laftanar Kanal Sani Uba, ya sanya wa hannu, kuma aka sanya a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun shiga uku, sojoji sun kaddamar da shirin kakkabe su a jihohin Arewa 2

An kama mai kai wa 'yan ta'adda kayayyaki

“Dakarun ɓangare na 4 a ƙarƙashin runduna ta 28 Task Force Brigade sun kama wani matashi mai shekaru 28, Ismail Muhammed, wanda ke samar wa ’yan ta’adda kayan da suke bukata, a yankin Visik da ke karamar hukumar Hong a jihar Adamawa.”
"Abubuwan da aka samu a hannunsa sun haɗa da jigidar bindigar AK-47, alburusai masu kaurin 7.62mm, kayan sojoji da kuma nau’ikan abinci daban-daban."

- Laftanar Kanal Sani Uba

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan ta’adda​

A wani harin daban da aka kai a ƙaramar hukumar Madagali, dakarun sojojin sun yi nasarar kashe wani kwamandan ’yan ta’adda, Abdullahi Mafa, yayin wani harin kwantan ɓauna da suka kai a kewayen kogin Visik.

Sojojin sun ƙwace bindiga nau’in AK-47 da jigidar bindigar shake da alburusai a hannunsa.

An cafke mai samar da jirage marasa matuka

Biyo bayan bayanan sirri da suka samu, dakarun sun kuma kama wani tsoho mai shekaru 64, Dauda Usman Gubula, wanda aka bayyana a matsayin mai taimaka wa ’yan ta’adda kuma mai samar musu da jirage marasa matuka.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Wasu jagororin 'yan bindiga 17 sun shiga hannu, 'yan sanda sun jero sunayensu

Wadannan jirage marasa matukan ne dai ’yan ta’addan ke sarrafawa domin kai wa dakarun sojoji hari.

Abubuwan da aka ƙwace a hannunsa sun haɗa da, jirage marasa matuka guda biyu, kayan gyara da haɗa su da abin caji (Power bank) har 20.

An cafke mai samar da jirage marasa matuka ga 'yan ta'adda
Mai samar da jirage marasa matuka ga 'yan ta'adda da sojoji suka cafke Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Wannan nasara ta cafke jirage marasa matukan ta nuna yadda ’yan ta’addan ke ƙara amfani da fasahar zamani a hare-harensu.

A jihar Borno kuma, dakarun OPHK tare da haɗin gwiwar ’yan banga da dakarun sa-kai na CJTF, sun dakile yunƙurin ’yan ta’adda a yankin Ngamdu, inda suka kashe wani mai leƙen asiri da ke kokarin kutsa kai cikin sansanin sojoji.

An kaddamar da rundunar fatattakar 'yan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa Babban hafsan tsaron kasa (CDS), Janar Olufemi Oluyede, ya kaddamar da rundunar kakkabe 'yan ta'adda a jihohin Kwara da Neja.

Janar Olufemi Oluyede ya bayyana cewa rundunar za ta mayar da hankali wajen ragargazar 'yan ta'adda a jihohin biyu.

Ya bayyana rundunar za ta rika shiga dazuzzuka da wurare masu wuyar shiga domin kakkabe maboyar tsagerun 'yan ta'addan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng