Kano: An Takaita Zirga Zirga, Mabiya Kwankwaso da Abba za Su Fafata a Zabe
- Rundunar 'yan sanda ta sanar da takaita zirga-zirga a kananan hukumomin Birni da Ungogo yayin da ake shirin zaben cike gibi a jihar Kano
- Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta sanar da cewa a gobe Asabar, 1 ga Fabrairu za a gudanar da zaben cike gibi a Kano, Abuja da sauransu
- Wannan ne karon farko da bangaren Sanata Rabiu Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf za su fafata a zabe bayan sauya shekar gwamnan
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta sanar da takaita zirga-zirga a kananan hukumomin Birni da Ungogo gabanin zaɓen cike gibi na majalisar jiha da za a gudanar a ranar 21 ga Fabrairu, 2026.
Sanarwar ta biyo bayan taron kwamitin shawarwari na hukumomin tsaro a lokacin zabe (ICCES), wanda kwamishinan INEC a Kano, Zango Abdu, ya jagoranta.

Source: Facebook
Legit Hausa ta gano cewa kakakin rundunar 'yan sandan jihar ya wallafa a Facebook cewa a ranar 19 ga Fabrairu, 2026 kwamitin ICCES ya yi zama a Kano.
An shirya gudanar da zabe a Kano
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, CSP Abdullahi Kiyawa, ya fitar rundunar ta sanar da cewa ta takaita zirga-zirga a jihar.
Kiyawa ya bayyana cewa:
“ICCES ta kammala shirye-shiryen tsaro gabanin zaɓen cike gibi da za a yi a mazabun Birni da Ungogo a ranar 21 ga Fabrairu, 2026.”
Mataimakin shugaban ICCES kuma kwamishinan ’yan sanda, Ibrahim Adamu Bakori, ya sanar da mazauna yankunan cewa:
“Tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, an ɗauki dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya da gudanar da zaɓe cikin ’yanci, adalci a mazabun Birni da Ungogo.”
An takaita zirga zirga a Kano
Sanarwar ta ce an haramta zirga-zirgar motoci, adaidaita sahu da babura daga ƙarfe 12:00 na dare zuwa ƙarfe 6:00 na yamma a ranar Asabar, 21 ga Fabrairu, 2026, wadda ita ce ranar zaɓe.
Punch ta wallafa cewa sanarwar ta ƙara da cewa:
“Sai dai za a ba da izini ga motocin da ke aikin gaggawa kamar motar asibiti, motar kashe gobara da motocin jami’an zaɓe da masu sa ido da aka tantance.”
A cewar rundunar, masu kaɗa ƙuri’a da suka cancanta kaɗai za a bari a wuraren zabe, yayin da wakilan jam’iyyun da INEC ta tantance kaɗai za su samu izinin kasancewa a wuraren zaɓe.
Haka kuma, ta ce ba za a ba kungiyoyin tsaro na jiha kamar ’yan banga, Neighbourhood Watch, Hisbah, jami’an KAROTA da sauransu damar kasancewa a wuraren zaɓe ba.
Abba da Kwankwaso za su fafata
Wannan shi ne karon farko da za a gwada karfin siyasa tsakanin gwamna Abba Kabir Yusuf da ya koma APC da kuma Sanata Rabiu Kwankwaso da ya ke NNPP.

Source: Facebook
Abba Kabir Yusuf ya shafe shekaru tare da Rabiu Kwankwaso kafin daga bisani su raba hanya a siyasance bayan samun mukamin gwamna.
Jihohin da za a yi zabe a 2026
A wani labarin, mun kawo muku cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta sanar da cewa za ta gudanar da zabe a wasu jihohi da yankuna.
A ranar Asabar, 21 ga watan Fabrairun 2026 INEC za ta gudanar da zaben cike gibi a jihohin Kano da Rivers da na kananan hukumomi a Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa idan shekarar 2026 ta kara nisa, hukumar zabe za ta gudanar da zaben gwamna a jihohin Osun da Ekiti.
Asali: Legit.ng


