'Yan Ta'adda Sun Shiga Uku, Sojoji Sun Kaddamar da Shirin Kakkabesu a Jihohin Arewa 2
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin kafa runduna ta musamman biyo bayan harin da 'yan ta'adda suka kai a jihar Kwara
- Babban hafsan tsaro (CDS), Janar Olufemi Olatubosun Olufemi, ya kaddamar da sabuwar rundunar samar da tsaron a jihar Kwara
- Janar Oluyede ya zayyano manufofin da ake son rundunar ta cimmawa domin kakkabe 'yan ta'addan da ke kai hare-hare
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kwara - Babban hafsan tsaron kasar nan (CDS), Janar Olufemi Olatubosun Oluyede, ya lashi takobin gudanar da “gagarumin farmakin sojojoji kan ’yan ta’adda da miyagu” a jihohin Kwara da Neja.
Janar Oluefemi Olatubosun Oluyede ya bayyana hakan ne biyo bayan ƙaddamar da rundunar Operation Savannah Shield a hukumance.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce an gudanar da taron ne a barikin Sobi, wanda shi ne hedikwatar wannan runduna ta hadin gwiwa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa ta.

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: Wasu jagororin 'yan bindiga 17 sun shiga hannu, 'yan sanda sun jero sunayensu
An kafa rundunar ragargazar 'yan ta'adda
Shugaba Tinubu ya amince da kafa rundunar ne bayan harin ta’addanci na baya-bayan nan da aka kai Kaiama a jihar Kwara da wasu sassa na Neja.
Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ne ya ƙaddamar da rundunar tare da babban hafsan tsaro da babban hafsan sojojin kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, a ranar Alhamis, 19 ga watan Fabrairun 2026.
An tura motocin yaki sama da 30 masu ɗauke da manyan bindigogi, gami da motocin yaki masu sulke (APCs).
Janar Oluyede ya bayyana cewa wannan aiki wani babban mataki ne na mayar da martani ga karuwar rashin tsaro a shiyyar Arewa ta Tsakiya.
A cewarsa, kwararar ’yan ta’adda daga iyakokin kasar nan da haɗin gwiwar da ke tsakanin miyagu daga Arewa maso Yamma da yankin Sahel sun rage amincewar jama’a tare da tsananta rashin tsaro, jaridar The Punch ta kawo labarin.
Me ye manufar kafa rundunar?
Ya ce manufar rundunar Operation Savannah Shield shi ne kare daukacin jihar Kwara da sassan jihar Neja da ke maƙwabtaka da ita, kakkabe ’yan ta’adda, lalata hanyoyin masu garkuwa da mutane, da maido da doka da oda.
Janar Oluyede ya ce rundunar za ta rika yin aiki da bayanan sirri da haɗin gwiwa tsakanin sojoji, 'yan sanda, da sauran hukumomin tsaro.
Hakazalika ya ce za a ba da kulawa ta musamman ga dazuzzuka da yankuna masu wahalar ratsawa, musamman kewayen dajin Kainji Lake National Park, wanda miyagu ke amfani da shi a matsayin maboya.
Shugaban sojoji ya ba da tabbaci
Janar Oluyede ya tabbatar wa mazauna yankin cewa wannan aiki ba na ɗan lokaci ba ne; tsari ne mai dorewa har sai an samu nasara.

Source: Twitter
Gwamna AbdulRazaq ya bayyana kaddamar da rundunar a matsayin babban sauƙi ga mazauna yankin, musamman waɗanda hare-haren ’yan bindiga da ’yan ta’adda suka shafa.
Gwamnan ya yarda cewa ko da yake an samu ci gaba wajen tabbatar da tsaro a Kudancin Kwara, amma yankin Arewacin Kwara na fuskantar babban ƙalubale, wanda hakan ya sa kafa wannan runduna ta haɗin gwiwa ya zama tilas.
'Yan ta'adda sun kashe mutane a Kebbi
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan ta'addan Lakurawa sun kai wasu hare-haren ta'addanci a jihar Kebbi.
Tsagerun 'yan ta'addan sun hallaka mutane sama da 30 tare da lalata kauyuka guda bakwai a hare-haren da suka kai.
Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta kara da cewa 'yan ta'addan sun kuma yi awon gaba da wasu shanaye.
Asali: Legit.ng

