Magana Ta Fito: Shugaba Tinubu Ya Fadi Dalilin Sanya Hannu a Dokar Zabe duk da Korafe Korafe

Magana Ta Fito: Shugaba Tinubu Ya Fadi Dalilin Sanya Hannu a Dokar Zabe duk da Korafe Korafe

  • Majalisar tarayya ta kammala aikin yi wa dokar zabe ta shekarar 2026 kwaskwarima tare da mika ta ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba wa dokar hannu a ranar Laraba, 18 ga watan Fabrairun 2026
  • Mao girma Bola Tinubu ya yi bayani kan dalilinsa na sanya hannu a dokar wadda ake ta cece-kuce kan wasu bangarorin ta

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya kare matakinsa na sanya wa dokar gyaran zaɓe ta shekarar 2026 hannu

Shugaba Tinubu ya ce ingancin zaɓe ya dogara ne kacokan kan yadda ake tafiyar da shi da kuma sa idon ɗan adam, maimakon tura sakamako kai tsaye ta yanar gizo kai-tsaye a take.

Tinubu ya yi magana kan sanya hannu a dokar zabe
Shugaba Bola Ahmed tare da jagororin majalisa yayin da yake sa hannu kan dokar zabe ta 2026 Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce Tinubu ya yi wannan jawabin ne jim kaɗan bayan sanya wa dokar hannu a fadar shugaban kasa da ke Abuja, a ranar Laraba, 18 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

An ji abin da ya roka da Tinubu ya yi waya da Shugaban gwamnatin kasar Jamus a tarho

Sanya hannun na zuwa ne a daidai lokacin da ake takaddama kan ko ya kamata a riƙa tura sakamakon zaɓe kai-tsaye ta yanar gizo daga mazaɓu.

Me Tinubu ya ce kan dokar zabe?

“Wannan ba shi ne mafi muhimmanci ba kamar yadda bangarorin tarihi na wannan al'amari suke. Abin da ke da muhimmanci shi ne tafiyar da tsarin ta yadda ba za a samu rudani ba, babu tauye hakkin 'yan Najeriya, kuma dukanmu za mu ga dimokuradiyya ta bunkasa."

- Shugaba Bola Tinubu

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa ko ma wane irin tsarin fasaha aka yi amfani da shi, mutane ne ke gudanar da zaɓe kuma su ne ke kammala shi.

“Ko yaya tsarin yake da kyau, mutane ne ke tafiyar da shi, mutane ne ke daukaka shi, kuma mutane ne ke kammala sakamakon."

- Shugaba Bola Tinubu

Matsayar Tinubu kan tura sakamakon zabe

Da yake magana kan muhawarar tura sakamakon zaɓe, Tinubu ya ce ba kwamfuta ce za ta tantance sakamakon karshe ba, sai dai jami'an zaɓe da aka ayyana, jaridar Vanguard ta kawo labarin.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fito ya nemi afuwar 'yan Najeriya bayan fara azumi

“Hasali ma, dangane da sakamakon karshe, ba za ku yi magana da kwamfuta ba, za ku yi magana ne da mutane waɗanda za su sanar da sakamakon karshe."
“Kuma idan kuka kalli jigon muhawarori daban-daban, watakila ya kamata 'yan Najeriya su tambayi karfin intanet namu. Ya ya karfin fasaharmu yake a yau? Yaya karfin fasaharmu zai kasance a gobe don amsa kiran tura sakamako kai tsaye ko akasin haka?”

- Shugaba Bola Tinubu

Za a ci gaba da amfani da takarda

Shugaban kasar ya sake nanata cewa tsarin kada ƙuri'a har yanzu ana yin sa ne da hannu, tun daga bayar da takardar zaɓe har zuwa ƙirga su.

“Muddin ka bayyana da kanka a matsayin mai kada kuri’a a kowace rumfar zabe, ana ba ka takardar zabe da hannu, ka kebe ka dangwala wa wanda kake so, ka jefa kuri’arka ba tare da tsangwama ko tsoma baki ba, daga baya kuma ana kirga kuri’un da hannu, a ware su, sannan a kidaya su da hannu."

- Shugaba Bola Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu a dokar zabe
Shugaba Bola Ahmed Tinubu lokacin da yake sanya hannu a dokar zabe Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Batun tura sakamako ta yanar gizo

A cewarsa, abin da ake turawa ta yanar gizo kawai shi ne bayanan lissafi da aka rubuta a takardar EC8A bayan an kammala tattara su da hannu.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Shugaba Tinubu ya rattaba hannu kan sabuwar dokar zabe

“Daidaiton lissafin ne kawai zai shiga takardar EC8A. Abin dai na takarda ne asali. Tura wannan sakamakon na takarda shi ne abin da muke kallo."
“Kuma muna bukatar mu guje wa matsalolin na'ura, ina farin ciki da kuka yi hakan, da tsoma baki, da kuma kutse maras amfani a wannan zamanin na ilmin kwamfuta."

- Shugaba Bola Tinubu

Shugaba Tinubu ya nemi afuwar 'yan Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed ya mika kokon bararsa ga 'yan Najeriya, yayin da aka fara azumin watan Ramadan.

Mai girma Bola Tinubu ya fito ya nemi 'yan Najeriya da su yafe masa idan har ya yi musu ba daidai ba a tsawon lokacin da ya kwashe a ofis.

Hakazalika, ya bukaci 'yan Najeriya na kowane addini da su yi addu'ar neman zaman lafiya tare da ba da goyon baya ga ƙoƙarin da ake yi na yaƙi da ta'addanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng