Ramadan 2026: Jerin Manyan Malaman Najeriya da Wuraren Tafsirinsu
- A yau Laraba, 18 ga watan Fabrairun 2026 al'ummar Musulmi a Najeriya suka tashi da azumi kamar 'yan uwansu na wasu kasashe
- Malamai da dama sun tafi birane da kauyuka a jihohin Najeriya 36 da FCT, Abuja domin gabatar da tafsirin Al-Kur'ani mai girma
- A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro muku wurare a jihohin da manyan malamai za su gabatar da tafsirin azumin Ramadan na bana
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kungiyoyin addinin Musulunci daban-daban sun tura malamai tafsirin Al-Kur'ani mai girma yayin da aka fara azumin watan Ramadan.
Bincike ya nuna cewa wasu malamai za su gabatar da tafsirin Al-Kur'ani a jihohinsu, yayin da wasu kuma aka tura su wasu jihohi na dabam.

Source: Facebook
A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro muku jerin wasu manyan malaman Najeriya da wuraren da za su yi tafsirin Ramadan a 2026.
Wuraren tafsirin malamai na 2026
Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya wallafa a Facebook cewa zai gudanar da tafsiri a Masjidud Da'awa da yamma a jihar Bauchi.
Malamin da ya kware wajen iya bayani zai yi tafsirin watan Ramadan a gida, ba zai bar jihar Bauchi ba.
A daya bangaren, Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi ya bude tafsir a Tudunwada jihar Kaduna ranar 15 ga Fabrairun 2026 kamar yadda ya wallafa a Facebook.
Babban 'dan na Marigayi Sheikh Dahiru Bauchi zai bi sahun mahaifinsa wanda ya dade yana tafsiri a Kaduna.
Farfesa Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo zai gabatar da tafsirin Al-Kur'ani mai girma a masallacin Gwallaga da ke jihar Bauchi.
Jibwis Nigeria ta sanar da cewa Sheikh Muhammadu Kabir Haruna Gombe zai gabatar da tafsiri a Hedkwatar Izala da ke Utako a Abuja.
Shugaban Izala mai hedkwata a Filato, Sheikh Sani Yahaya Jingir zai yi tafsirin Al-Kur'ani a masallacin 'Yan Taya a jihar Filato.
Karin malamai da za su yi tafsiri
Wasu rahotanni sun bayyana cewa limamin masallacin kasa da ke Abuja, Farfesa Ibrahim Makari zai gabatar da tafsiri a masallacin da yamma.
Shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa zai gabatar da tafsiri a Masallacin mai Unguwa Doma da ke Jekadafari Gombe.
Sheikh Isa Ali Pantami kuma ya sanar a shafinsa na Facebook cewa zai fara tafsiri a masallacin Annur da ke Abuja daga 1 ga Ramadan 1447.

Source: Facebook
Shugaban Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau zai yi tafsirin a Jimeta da ke jihar Adamawa yayin da mataimakinsa, Sheikh Usman Isa Taliyawa zai yi a Filin Kwallon Bolari a Gombe.
Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi zai jagoranci tafsirin Al-Kur'ani mai girma a masallacin Sultan Bello da ke jihar Kaduna.
Wasu wuraren tafsiri a Ramadan 2026
Mataimakin shugaban malaman Izala, Sheikh Sheikh Yusuf Sambo zai gabatar da tafsiri a masallacinsa da ke Rigacikun a jihar Kaduna.
Sheikh Dr Bashir Aliyu Umar kuma zai gabatar da tafsirin Al-Kur'ani mai girma a masallacin Al-Furqan da ke jihar Kano, Najeriya.
Sheikh Abdul Razak Yahaya Haifan zai gabatar da tafsirin azumin shekarar 2026 a Gwagwalada da ke Abuja yayin da Farfesa Mansur Sokoto zai yi a masallacin Abu Huraira da ke Sokoto.
Sheikh Abdallah Usman Gadon Kaya zai yi tafsiri a Kanbariki, Kumo a Gombe, Dr Abubakar Muhammad Sani Birnin Kudu kuma a masallacin Galadanci da ke Birnin Kudu.
Wasu malamai da ba samu bayani a shafukansu ba sun hada da Sheikh Sharif Ibrahim Saleh, Sheikh Qaribullah Nasiru Kabara, Sheikh Muhammad Bin Usman Kano.
Dr. Kabir Asgar zai gudanar da tafsirinsa ne a masallacin Area 8 unguwar Garki a Abuja. Zai karantar da maza da mata da karfe 4:00 da yamma da kuma 10:30 na safe.
Shirin da ya kamata a yi a Ramadan
A wani labarin, mun hada muku rahoto na musamman game da abubuwan da ya kamata kowane Musulmi ya yi a shirin tarbar Ramadan.
Daga cikin muhimman abubuwan akwai tsara lokaci domin samun damar halartar wuraren ibada yadda ya kamata a cikin watan.
Kiyaye lokutan da ake tafsiri da halartansu na cikin abubuwan da ya kamata Musulmi ya shirya yi yayin da watan Ramadan ya kama.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


