A Zo a Nema: Gwamnatin Tarayya Ta Bude Shafin Daukar Matasa Aiki a Najeriya
- Ma'aikatar ilimi ta sanar da daukar kwararrun malamai na fasaha domin farfado da makarantun kimiyya da sana'o'i na tarayya a fadin kasar
- Wannan mataki na daya daga cikin manufar 'Renewed Hope' ta Shugaba Bola Tinubu domin rage karancin kwararrun ma'aikata a Najeriya
- An bukaci wadanda suka san suna da kwarewar da ake bukata, da su cike fom din neman aikin daga nan zuwa ranar 16 ga watan Maris, 2026
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Ma’aikatar ilimi ta tarayya ta sanar da cewa ta bude shafin daukar ma'aikata a karkashin wani shiri na musamman da za a shafe shekara guda ana yi.
Gwamnatin tarayya ta ce wannan dama, an bude ta ne domin farfaɗo da kwalejojin fasaha na tarayya (FTC) ta hanyar ɗaukar masu ba da horo.

Kara karanta wannan
Gwamna ya tausaya wa ma'aikata, ya masu wata garaɓasa a wurin aiki saboda Ramadan

Source: Twitter
An bude shafin daukar ma'aikata
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai mai kwanan wata 17 ga Fabrairu 2026, da aka wallafa a shafin ma'aikatar na X.
Ma'aikatar ilimi ta ce wannan yunƙurin wani ɓangare ne na ƙoƙarin sake fasalin shirin samar da ilimin sana'o'i na TVET ƙarƙashin "Renewed Hope" na Shugaba Bola Tinubu.
Wannan shiri zai magance giɓin ƙwararrun ma'aikata a Najeriya ta hanyar amfani da ƙwararrun masana masana'antu waɗanda za su iya koyar da fasahar zamani ga dalibai.
Wani bangare na sanarwar ta ce:
"Wannan shiri na shekara guda, zai taimaka wajen cike gibin fasaha a Najeriya da kuma tabbatar da cewa an aiwatar da shirin TVET cikin inganci."
Yadda za a nemi aikin koyarwar
A cewar ma’aikatar, shirin ɗaukar ma'aikatan ya shafi ƙwararrun masana fasaha waɗanda ke da ƙwarewar koyarwa domin ganin dalibai sun iya abin da aka koya masu a aikace.
Wannan shirin daukar aikin, wani ɓangare ne na sauye-sauye masu faɗi da gwamnati ke yi, da nufin samar da kwararrun matasa da za su yi gogayya a kasuwar ƙwadago da ke sauyawa a kowane lokaci.
An buƙaci masu sha'awar neman aikin da su cike wannan fom ɗin neman aiki ta yanar gizo ta hanyar amfani da shafin da ma'aikatar ta samar.

Source: Getty Images
Ranar da za a rufe neman aikin
Ma’aikatar ta jaddada cewa za a tantance dukkan fom fom din da aka cike ta hanyar gaskiya da adalci, kuma wadanda suka cancanta ne kawai za a tuntuba.
Shafin neman aikin zai kasance a buɗe har zuwa ƙarfe 11:59 na daren ranar Litinin, 16 ga watan Maris, 2026, in ji rahoton Punch.
Ma’aikatar ta sake jaddada aniyarta na mayar da makarantun fasaha na tarayya su zama cibiyoyin ƙwararru don haɓaka fasaha, ƙirƙira, da kuma shirya ƙwararrun ma'aikata ga ƙasa.
An bullo da wata doka ga masu neman aiki
A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamnatin tarayya ta wajabta gwajin miyagun kwayoyi kan duk wanda ke neman aikin domin tsaftace tsari da samar da ingantaccen aiki.
Wannan mataki na zuwa ne yayin da ake kara samun yawaitar ta'amali da miyagun kwayoyi, musamman tsakanin matasan Najeriya.
Gwamnatin tarayyar ta umarci kowace ma'aikata da hukumomin gwamnati su hada kai da hukumar NDLEA domin fara aiwatar da dokar yayin daukar ma'aikata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

