Babban Albishirin Dangote ga ’Yan Najeriya kan Farashin Naira a 2026

Babban Albishirin Dangote ga ’Yan Najeriya kan Farashin Naira a 2026

  • Attajirin dan kasuwa a Najeriya har Afrika, Aliko Dangote, ya yi albishir ga yan kasa game da farashin Naira idan aka kwatanta da dala
  • Ya yaba wa manufofin gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Bola Tnubu yana cewa sauye-sauyen tattalin arziki sun fara ba da sakamako
  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ce bangaren masu zaman kansu na da muhimmanci wajen bunkasa masana’antu.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya yi magana kan manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Dangote ya bayyana cewa darajar Naira za ta kara karfi, inda ya ce za ta iya kaiwa ₦1,000 kan dala guda kafin karshen shekarar 2026.

Dangote ya yabawa matakan gwamnatin Tinubu kan tattalin arziki
Attajirin dan kasuwa Aliko Dangote da Bola Tinubu. Hoto: Dada Olusegun.
Source: Twitter

Dangote ya magantu kan darajar Naira

Dangote ya fadi hakan ne ranar Talata 17 ga watan Fabrairun 2026 a Abuja yayin kaddamar da manufofin masana’antu na Najeriya, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

'Yana neman ruguza kasa': Gwamnati ta haramta amfani da dukan kafofin sadarwa

Majiyoyi sun tabbatar da cewa taron da ya samu halartar Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, da sauran manyan baki.

Ya ce duk da cewa a halin yanzu dala na kusan ₦1,300, sauye-sauyen da gwamnati ta aiwatar sun fara haifar da kyakkyawan sakamako, musamman ga masana’antun cikin gida.

Ya ce:

“Yau Dala na kan N1,340. Mai Girma Mataimakin Shugaban Kasa, zan iya tabbatar maka cewa, da abin da na sani, idan aka dakile duk wadannan shigo da kayayyaki daga waje, darajar kudinmu a wannan shekarar zai iya sauka zuwa N1,100 idan muka yi sa’a. Abin da ya rage kawai shi ne, watakila gwamnati ta dakatar da kara karfin Naira domin ta ci gaba da tara karin Naira.”
Dangote ya yi hasashen darajar Naira a shekarar 2026
Attajiri, Aliko Dangote da ya zayarci Bola Tinubu a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Tattalin arziki: Dabarar da Dangote ya kawo

A cewarsa, dakile shigo da kayayyaki daga waje zai taimaka wajen karfafa darajar Naira, sai dai ya ce akwai bukatar a kula da daidaito domin tattalin arziki kada ya shiga tangarda.

Dangote ya bukaci gwamnati ta kare masu zuba jari na cikin gida ta hanyar samar da karin tallafi da ingantattun ababen more rayuwa kamar wutar lantarki, wadda ya ce har yanzu tana zama kalubale ga harkokin kasuwanci.

Kara karanta wannan

Rigimar da ta kaure a Majalisar wakilai ta kara tsanani, wasu yan majalisa sun yi fushi

Ya jaddada cewa manufar bunkasa masana’antu dole ne ta zo da cikakken kariya ga ‘yan kasuwa domin samar da ayyukan yi da habaka tattalin arzikin kasa.

A nasa jawabin, Shettima ya ce bangaren masu zaman kansu na taka muhimmiyar rawa wajen cimma manufofin sabuwar manufar masana’antu ta Najeriya, cewar TheCable.

Ya kuma bayyana cewa kamfanin simintin Dangote kadai ya biya haraji na kimanin Naira biliyan 900 a shekarar 2025, alamar irin gudunmawar da bangaren ke bayarwa ga tattalin arziki.

Dangote ya sake fitar da farashin mai

A wani labarin, Matatar Dangote ta rage farashin man fetur daga N799 zuwa N774 kan kowace lita kuma an gano matakin ya fara aiki nan take a fadin Najeriya.

Hakan na zuwa ne bayan Aliko Dangote ya sanar da kara kudin mai a lokacin da aka kammala bukukuwan karshen shekarar 2025 aka shiga 2026.

Masana harkar mai sun ce matakin na nuna sabon tsari a kasuwar man fetur yayin da Dangote ya fara maganar zuba jari a kasar Burundi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.