Ramadan 2026: Fitar Maniyyi da Wasu Abubuwa 6 da Ke Lalata Azumi
Yayin da aka fara azumin Ramadan na shekarar 2026, al'ummar Musulmi sun dukufa wajen neman lada da dukkan falalar da ke cikin wannan wata mai albarka.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Azumi na ɗaya daga cikin manyan ibadu, wanda ya ƙunshi kame kai daga sha'awoyi kamar na abinci, abin sha, saduwa da iyali da tsakar rana da sauran abubuwan da ke ɓata shi.

Source: Getty Images
Abubuwa 7 da ke karya azumi a Ramadan
Ga jerin abubuwa bakwai da ke ɓata azumi a Ramadan, kamar yadda jami'ar UMS ta rahoto a shafinta na intanet:
1. Cin abinci ko shan ruwa da gangan
Yin hakan da gangan a cikin ranar Ramadan yana ɓata azumin Musulmi. Allah ya bayyana a Suratul Baqarah cewa a ci, a sha har alfijir ya keto, sannan a cika azumi har zuwa dare.
Amma idan amai ya zo da kansa ba tare da an yi sanadin sa ba, to azumi yana nan da ingancinsa.
2. Jinin Haila da na haihuwa
Mata a Musulunci sun samu sassauci lokacin haila da nifasi (jinin haihuwa). Idan mace ta ga jini yayin da take azumi, azuminta ya karye, kuma dole ne ta rama wannan azumin bayan Ramadan.
3. Fitar da maniyyi da gangan
Idan mutum ya fitar da maniyyi da gangan (kamar ta hanyar wasa da al'aura), azuminsa ya ɓaci. Amma idan hakan ya faru ba tare da nufin sa ba (kamar yin mafarki), hakan ba ya ɓata azumi.
A cikin fatawar da ya bayar a shafinsa na YouTube, fitaccen malamin Musulunci, Mufti Menk, ya jaddada cewa wasa da al'aura har maniyyi ya fito, yana karya azumi.
4. Yin jima'i a tsakar rana ana azumi
Ma'aurata da suka yi jima'i a tsakar rana, alhalin ana azumin Ramadan, azuminsu ya karye, kuma za su fuskanci hukunci mai tsanani.
Dole ne wanda ya yi jima'i da tsakar rana ana azumi ya yi kaffara, wanda ya haɗa da ƴanta bawa, ko azumin wata biyu a jere, ko kuma ciyar da matalauta guda sittin idan ba ya da ikon yin sauran.
5. Shan taba
A cewar malaman mazhabar Shafi'i, shan taba yana ɓata azumi domin hayaki ne da mutum ke ja da gangan zuwa cikin cikinsa.
A cikin littafin Agar Tak Hanya Lapar dan Dahaga: Panduan Puasa Ramadhan Sehat dan Berkah wanda Iqbal Syauqi Al-Ghifary, Sheikh Sulaiman ya buga, aka wallafa a shafin Cibiyar El Bukhari, an ce shakar hayakin girki ko na hanya wanda ba a iya kauce masa ba ya karya azumi.
6. Yin amai da gangan

Source: Getty Images
Amai yana nufin amayar da abinci daga ciki ta baki. Idan Musulmi ya yi amai da gangan, azuminsa ya ɓaci, kamar yadda Dr. Zakir Naik ya sanar a cikin bidiyon da ya wallafa a shafinsa na YouTube.
Amma idan amai ya zo da kansa ba tare da an yi sanadin sa ba, to azumi yana nan da ingancinsa.
7. Ridda
Idan mutum ya fice daga addinin Musulunci (ridda) yayin da yake azumi, azuminsa ya ɓaci nan take. Hakan za ta kasance ne domin imani da Allah shi ne babban sharadi na yin azumi da karɓuwar sa.
Malamai sun shawarci Musulmi da su nisanci gulma, kalaman banza, da faɗace-faɗace domin kiyaye ladan azuminsu.
Shawarwari ga matasa a Ramadan
Wani shugaban makarantar Islamiyya a Funtua, Malam Yahaya Lawal Mailafiya, a zantawarsa da Legit Hausa, ya shawarci matasa da su yi amfani da wannan mata don gyara alakarsu da Allah.
Malam Yahaya Mailafiya ya ce:
"Wannan lokaci ne da matasa za su gyara alakarsu da Allah. Matasa musamman wadanda ke aikata munanan laifuffuka, kamar kallon fina finan batsa, shaye shaye, bin mata, istimna'i da sauransu, su yi amfani da wannan wata don sauya dabi'unsu.
"Idan har mutum zai iya shafe kwanaki 29 ko 30 ba tare da ya sha abin gusar masa da hankali ba, ko ya yi sata, ko ya bi mata, ko ya yi istimna'i ko ya kalli hotuna ko bidiyon batsa, ina ga zai iya ci gaba da sauran rayuwarsa ba tare da ya sake komawa rayuwarsa ta baya ba.
"Amma komai yana farawa ne da niyya, da kuma sanya wa a rai cewa mutum yana so ya canja rayuwarsa. Da yardar Allah sai ka ga ka daina munanan halayen nan."
Malam Yahaya ya ce ya bada wadannan shawarwarin ne saboda yadda ake samun matasa na shiga ire-iren halayen nan da ke lalata gobensu da zubar masu da kima a cikin al'umma, kuma ya jefa su a halaka gobe kiyama.
An ga watan Ramadan a Najeriya
A wani labari, mun ruwaito cewa, kwamitin ganin wata a Najeriya ya fitar da sanarwa kan ganin watan Ramadan domin fara azumi a kasar.
Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya tabbatar da ganin jinjirin watan Ramadan a Najeriya a daren ranar Talata 17 ga watan Faburairun 2026.
Sanarwar da aka fitar da kawo karshen watan Sha'aban tare da tabbatar da shiga Ramadan wacce ta kasance mafi girma da daraja a cikin sauran watannin Musulunci.
Asali: Legit.ng



