Mata Zalla: Abubuwa huɗu da ya kamata Mata suna yi yayin Jinin al'ada

Mata Zalla: Abubuwa huɗu da ya kamata Mata suna yi yayin Jinin al'ada

- Karanta ku ji sirrukun da zasu saukakawa Mata yayin da bakonsu na wata-wata ya ziyarce su

Kamar yadda aka sani shi jinin al'ada Mata ne suke yinsa, jini ne da mata ke fitarwa daga jikinsu na tsawon wani lokaci a duk wata, ko dai a farkon wata, tsakiya ko kuma a karshensa.

Mata Zalla: Abubuwa huɗu da ya kamata Mata suna yi yayin Jinin al'ada
Mata Zalla: Abubuwa huɗu da ya kamata Mata suna yi yayin Jinin al'ada

Sai dai akwai abubuwa da dama wanda mace mai jinin al'ada ya kamata ta lura da su, dalili kuwa shi ne domin tabbatuwar ingantaciyyar lafiya a tare da ita da kuma kaucewa kamuwa da wasu kwayoyin cututtuka.

Wasu abubuwan na da kyau a guje musu saboda halin da jikin mace ke kasancewa a yayin jinin al'adar, domin zasu iya cutar da mai jinin al'ada ko da kuwa kina da bukatar yin su, wasu kuma yana da kyau a yi su domin kaucewa fadawa wani yanayi na daban.

Kamar yadda ubangiji ya hallice mutane mabambamta, haka zalika yanayin jikin kowa yake da bambamci wanda hakan yana da matukar tasiri wajen faruwar wani abu ga ilahirin gangar jiki, dan haka yana da kyau mace mai jinin al'ada ta lura da abubuwa guda hudu da za a bayyana a kasa:

1. Kauracewa abincin da ke dauke da gishiri sosai

Mata Zalla: Abubuwa huɗu da ya kamata Mata suna yi yayin Jinin al'ada
Mata Zalla: Abubuwa huɗu da ya kamata Mata suna yi yayin Jinin al'ada

Bincike ya tabbatar da cewa duk mace da take yin jinin al'ada, yana da kyau ta rage cin duk wani abu da yake dauke da gishiri sosai a cikinsa, domin hakan yana taimakawa wajen tsinkewar jininta wanda hakan zai iya bata matsala a ko da yaushe.

2. Sauya Kunzugun Jinin Al'ada (Pad)

Mata Zalla: Abubuwa huɗu da ya kamata Mata suna yi yayin Jinin al'ada
Mata Zalla: Abubuwa huɗu da ya kamata Mata suna yi yayin Jinin al'ada

Yana da matukar tasiri da kuma kyau ga mace mai jinin al'ada take sauya nafkin din da ta yi kunzugu da shi ko kuma abinda suke amfani da shi domin tare jinin wato (Pad) akalla duk bayan sa'o'i 3-4 domin hakan ne kawai zai taimaka wajen hana mace kamuwa da wasu kwayoyin cututtuka na Bacteria.

3. Daina amfani da farin wandon ciki (Pants)

Mata Zalla: Abubuwa huɗu da ya kamata Mata suna yi yayin Jinin al'ada
Mata Zalla: Abubuwa huɗu da ya kamata Mata suna yi yayin Jinin al'ada

A lokacin da mace ke yin jinin al'ada yana da kyau ta kauracewa amfani da farin pants, domin kaucewa bata shi da jinin al'adar wanda daga Karshe yi masa hidima da kuma tsaftace shi zai zamo abu mai wahala. Yana da kyau a bar amfani da shi har tsawon lokacin da jinin zai dauke, wanda daga bisani za a iya kuma amfani da shi ba tare da fuskantar wata matsala ba.

4. Motsa jiki yayin jinin al'ada

Mata Zalla: Abubuwa huɗu da ya kamata Mata suna yi yayin Jinin al'ada
Mata Zalla: Abubuwa huɗu da ya kamata Mata suna yi yayin Jinin al'ada

Sau da yawa za a ga macen dake jinin al'ada bata fiya yin wasu ayyuka na motsa jiki ba, sai dai a ganta a zaune ko a kwance, wanda ya hada da kallon na'urar Talabijin ko kuma zama ba tare da katabus.

KU KARANTA: Budurwa ta shiga cakwakiya bayan da saurayi ya sulale ya bar ta ce a kawo mata abincin Naira 11,800 ranar farko

Amma bincike ya nuna cewa motsa jiki ga mai jinin al'ada abu ne mai matukar amfani domin yana taimakawa jiki sosai tare da saukaka zafin ciwon mara ga mai jinin al'adar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel