Manya Sun Fara Nuna Damuwa da Jibge Sojojin Amurka da aka Soma a Najeriya
- Wasu fitattun ’yan Najeriya sun yi Allah-wadai yadda Najeriya ta bude kofa ake jibge sojojin Amurka a wasu daga cikin sassan kasar nan
- Mutane irinsu babban lauya mai fafutukar kare hakkin dan adam, Femi Falana SAN na ganin wannan kutse ne ga cin gashin kan Najeriya
- Sun buƙaci gwamnati ta ƙarfafa sojojin cikin gida maimakon dogaro da ƙasashen waje domin yaki da matsalolin da suka dabaibaye ta
FCT Abuja - Wasu manyan ’yan Najeriya sun yi tir da kasancewar sojojin Amurka a Najeriya, suna mai cewa hakan shiga hakkin kasa mai cin gashin kanta ne.
A makon da ya gabata ne jiragen sojin Amurka suka fara sauka a Najeriya,watanni kadan bayan barazanar da Shugaba Donald Trump ya yi wa kasar.

Source: UGC
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa jami’an Amurka da na Najeriya sun shaida wa kafafen yaɗa labarai cewa kusan sojoji 200 na Amurka za a tura domin bayar da shawara da horo.
An yi tir da shigowar sojojin Amurka Najeriya
Jaridar Leadership ta ruwaito a cewar jami’an Amurka, ana sa ran zirga-zirgar jiragen za ta ci gaba a makonni masu zuwa a matsayin wata manufa ta wucin gadi domin tallafa wa yaƙin da ake yi da ta’addanci.
Sai dai Hedikwatar Tsaro ta Najeriya (DHQ) ta jaddada cewa mutanen Amurkan ƙwararrun masu fasaha ne kawai da za su yi aikin shawara da horo, ba sojojin faɗa ba.

Source: Facebook
Ta ce duk ayyukansu za su kasance ƙarƙashin iko da jagorancin gwamnatin Najeriya tare da haɗin gwiwa da Rundunar Sojojin Najeriya.
Amma lauya mai fafutukar kare hakkin dan adam, Femi Falana da Jibrin Ibrahim da sauran 'yan gwagwarmaya sun ce kasancewar sojojin Amurka ya keta hakkin kasar.
Sun tuno yadda aka soke yarjejeniyar tsaro ta 1960 tsakanin Birtaniya da Najeriya sakamakon adawar da jama’a suka nuna.
Masu faftuka sun shawarci Najeriya
Su Femi Falama sun ambaci jawabin Murtala Mohammed a taron hadin kan Afrika a 1976, inda ya jaddada cewa shiyyar ba za ta ci gaba da zama ƙarƙashin ikon wata ƙasa ta waje ba.
Sun kuma yi nuni da cewa a 2001 an janye wata yarjejeniyar haɗin gwiwar soja da Amurka bayan adawa daga Ma’aikatar Tsaron kasar nan.
Sannan a 2005 Majalisar Dattawa ta soke yarjejeniyar kariya ga ’yan Amurka daga kotun hukunta masu laifi ta duniya bisa saba wa kundin tsarin mulki.
Sun ce kundin tsarin mulki na 1999, sashe na 12(1), ya tanadi cewa duk wata yarjejeniya da wata ƙasa ba za ta zama doka ba sai Majalisar Dokoki ta amince da ita.
Sun ƙi amincewa da ra’ayin cewa sojojin Najeriya ba su da ikon kare ƙasar, suna mai cewa rundunar ta taka rawar gani a ayyukan wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya.
Sun ba da shawarar cewa maimakon miƙa tsaro ga kasar waje, a inganta rundunar ’yan sanda da sojoji, a ƙarfafa tattara bayanan sirri, a kyautata jin daɗin sojoji, a kuma zuba kudin da suka dace a bangaren.
A bangarensa, Farfesa Jibrin Ibrahim ya nuna damuwa cewa a yau wasu ’yan Najeriya na ganin duk wani taimako daga Amurka abin maraba ne, ba tare da fahimtar illolinsa ba.

Kara karanta wannan
Ministan Tinubu ya jero yankunan da aka ba sojojin Amurka izinin shiga a Arewacin Najeriya
Ya tambaya ko a wace ƙasa tsoma bakin tsaron Amurka ya haifar da dorewar zaman lafiya, yana mai cewa a maimakon haka sau da yawa yana ƙara rura wutar rashin tsaro ne.
An shiga damuwa kan sojojin Amurka a Najeriya
A baya, mun wallafa cewa hankalin 'yan Najeriya ya karkata kan zuwan sojojin Amurka 100 kasar, musamman bayan jin labarin cewa an sauke su a jihar Bauchi.
Fitaccen lauya mai kare hakkin dan adam, Audu Bulama Bukarti ya yi wa gwamnatin Najeriya tambayoyi game da sauke sojojin da ayyukan da za su yi.
Barista Bulama Bukarti ya bayyana cewa 'yan Najeriya sun cancanci sanin yarjejeniyar da gwamnatin Bola Tinubu ta kulla da sojojin Amurka da takamaiman aikinsu.
Asali: Legit.ng

