Manyan Tambayoyi da aka Yi wa Tinubu kan Jibge Sojojin Amurka a Bauchi
- Hankalin 'yan Najeriya ya karkata kan zuwan sojojin Amurka 100 kasar, musamman bayan jin labarin cewa an sauke su a jihar Bauchi
- Lauya mai fashin baki, Audu Bulama Bukarti ya yi wa gwamnatin Najeriya tambayoyi game da sauke sojojin da ayyukan da za su yi
- Barista Bukarti ya bayyana cewa 'yan Najeriya sun cancanci sanin yarjejeniyar da gwamnatin Bola Tinubu ta kulla da sojojin Amurka
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Bayan gwamnatin Najeriya ta tabbatar da zuwan sojojin Amurka, 'yan kasa sun fara yi wa shugaba Bola Ahmed Tinubu tambayoyi.
Hedkwatar tsaro ta sanar da cewa jami’an sojin Amurka 100 sun isa filin jirgin sama na Bauchi domin tallafa wa rundunar sojojin Najeriya a horo da musayar bayanan sirri.

Kara karanta wannan
Ministan Tinubu ya jero yankunan da aka ba sojojin Amurka izinin shiga a Arewacin Najeriya

Source: Facebook
Barista Audu Bulama Bukarti ya bayyana cewa sanarwar gwamnatin Najeriya ta bar baya da kura a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Tambayoyi kan zuwa sojojin Amurka
Lauya Bulama Bukarti ya ce sanarwar da rundunar tsaro ta yi a Facebook ba ta fayyace ko sojojin za su ci gaba da zama a Bauchi ba ko kuma suna kan hanyarsu ta zuwa wani wuri dabam.
Ya ce:
"Idan har za su zauna a Bauchi, ya dace jama’a su san dalilin da ya sa aka zaɓi jihar maimakon wuraren da ake fama da ta’addanci kai tsaye kamar Zamfara, Niger ko Borno."
Ya kara da cewa mai yiyuwa ne akwai hujjojin da suka shafi dabaru ko tsare-tsare masu ƙarfi da suka sa Najeriya ta yanke shawarar sauke su a Bauchi.
Ya kara da cewa:
"Amma idan babu cikakken bayani, rashin tabbaci kan haifar da jita-jita. La’akari da yadda batun kasancewar sojojin ƙasashen waje a ƙasar Najeriya ke da matuƙar muhimmanci, wajibi ne ne a bayyana wa jama'a gaskiya."

Kara karanta wannan
Kurunkus: Sojojin Amurka 100 sun shigo Najeriya, hedkwatar tsaro ta fadi Abin da ya kawo su
Karin tambayoyi ga Tinubu
Bugu da ƙari, Bulama Bukarti ya ce ya kamata a sanar da ’yan Najeriya dalla-dalla kan ainihin iyaka, tsawon lokaci da kuma sharuddan turo sojoji, maimakon ambaton “horo da musayar bayanan sirri” kawai.
"Jama’a na da haƙƙin sanin tsawon lokacin da jami’an Amurkan za su zauna, irin horon da za su bayar da kuma hanyoyin sa ido da Najeriya za ta bi wajen kula da wannan haɗin gwiwa."
Inji Bulama
Ya kara da cewa idan haɗin gwiwar halastacciya ce, mai iyaka kuma tana da amfani ga muradun Najeriya, to bayani a fili zai ƙarfafa amincewar jama’a.

Source: Getty Images
Bulama ya jaddada cewa yin shiru ko ɓoye bayanai na iya ƙara rura wutar zargi, jita-jita da yaɗuwar bayanan ƙarya a lokacin da ake matuƙar buƙatar gaskiya da fayyace al’amura.
Martanin kwamitin shari'a ga Amurka
A wani labarin, kun ji cewa kwamitin shari'a na kasa ya yi magana kan zargin da dan majalisar kasar Amurka ya yi wa Sanata Rabiu Kwankwaso.
Kwamitin shari'a ya zargi Amurka da amfani da bayanan bogi kan daukar wasu matakai da suka shafi Najeriya, inda ya ce hakan bai dace ba.
Ya kara da cewa akwai rashin adalci a zargin da aka yi wa Kwankwaso, musamman lura da cewa shi kadai aka ware a cikin 'yan siyasar Najeriya.
Asali: Legit.ng
