Rigimar da Ta Kaure a Majalisar Wakilai Ta Kara Tsanani, Wasu Yan Majalisa Sun Yi Fushi
- Wasu daga cikin mambobin Majalisar wakilai sun fice daga zaman gaggawa da aka gudanar yau Talata, 17 ga watan Fabrairu, 2026
- Rahotanni sun nuna rigima ta kaure a zaman majalisar ne yayin da aka gabatar da kudirin soke gyaran dokar zabe da aka riga aka amince da shi
- Wannan lamari ya tayar da hayaniya bayan Shugaban majalisar, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya jagoranci kada kuri'ar murya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Rigimar da ta kaure a zaman Majalisar wakilan tarayya yau Talata, 17 ga watan Fabrairu, 2026 ta kara kamari, yan majalisa sun fara kai wa bango.
Rahotannin da muka samu yanzu haka na nuni cewa wasu daga cikin mambobin Majalisar sun fusata matuka har sun fice daga zauren Majalisar tun kafin a kammala zaman.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa hakan ya biyo bayan kin amincewarsu da yunkurin soke matakin da Majalisar ta dauka a baya kam kudirin dokokin zaben Najeriya.
Rikicin ya fara ne bayan Shugaban Kwamitin Dokoki da Harkokin Kasuwanci na Majalisa, Hon. Francis Waive, ya gabatar da kuduri na neman majalisar ta janye amincewarta da kudurin da aka zartar a ranar 23 ga Disamba, 2025.
Hon. Waive ya tuna cewa an amince da kudurin a Disamba 2025, amma daga baya wani kwamitin hadin gwuiwa ya yi zama domin daidaita gyaran dokar zaben da wanda Majalisar dattawa ta yi.
A cewarsa, binciken kwamitin ya gano wasu kura-kurai da aka samu a wasu anade-tanade na dokar, wanda ya sa ake buƙatar majalisa ta sake nazari kan matsayarta ta farko.
Nan take shugaban Kwamitin Harkokin Zaɓe na Majalisa, Hon. Adebayo Balogun, ya mara wa kudurin baya.
Yadda kuri’ar murya ta haddasa rikici
Kakakin Majalisa, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ya gabatar da kudurin domin kada kuri’ar murya, kamar yadda tashar Channels tv ta tattaro.
An ruwaito cewa duk da cewa muryar wadanda suka ce “A’a” ta fi ƙarfi fiye da “Eh”, sai ya yanke hukunci cewa “Eh” ne suka yi rinjaye, lamarin da ya jawo hayaniya daga wasu ’yan majalisar.
Sakamakon haka ne, Hon. Abbas ya kira zaman sirri domin dawo da doka da oda, amma hakan bai warware matsalar ba, domin zaman ya sake rikicewa.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Rigima ta kaure a Majalisar Wakilai, an fara tayar da jijiyoyin wuya a Abuja

Source: Facebook
Sabanin 'yan majalisa kan sashe na 60(3)
’Yan majalisar sun ci gaba da nuna rashin amincewarsu musamman kan Sashe na 60(3), wanda ya shafi wajabcin tura sakamakon zaɓe ta intanet daga kowace rumfa.
Sun miƙe tsaye a zauren majalisa tare da hana Mataimakin Kakakin Majalisa, Benjamin Kalu, wanda ya karbi Tajudeen Abbas, ya ci gaba da jagorantar zaman.
A ƙarshe, wasu daga cikin ’yan majalisar da ke nuna ɓacin rai sun fice daga zaman majalisar domin nuna adawarsu.
Majalisar wakilai ta gyara dokar zabe
A wani rahoton, kun ji cewa Majalisar wakilan Najeriya ta yi gyara ga bangaren tura sakamakon zabe a dokar zaben 2026 wadda ta amince da ita a baya.
Majalisar ta amince da nau’in da majalisar dattawa ta riga ta amince da shi, wanda ya ba da damar tura sakamakon zaɓe ta intanet.
Wannan amincewa ta zo ne a daidai lokacin da mambobin majalisar na ɓangaren adawa suka nuna rashin amincewarsu da yunkurin soke asalin gyaran da aka yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
