Jirgin Ruwa Ya Kifar da 'Yan Rakiyar Amarya, Mata Sun Mutu

Jirgin Ruwa Ya Kifar da 'Yan Rakiyar Amarya, Mata Sun Mutu

  • Gwamnatin jihar Kebbi ta nuna alhini kan rasuwar wasu mata daga cikin masu rakiyar amarya a haɗarin jirgin ruwa a karamar hukumar Yauri
  • Gwamna Nasir Idris ya nuna matukar damuwa game da rasuwar matan, haka zalika shugaban karamar hukumar Yauri inda matan suka fito
  • Wasu rahotanni sun nuna cewa sama da mutane 100 ne a cikin kwale-kwalen da ya yi hadarin, inda akalla mata 13 suka riga mu gidan gaskiya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kebbi - Gwamnatin Kebbi ta bayyana matuƙar alhini kan wani mummunan hatsarin jirgin ruwa da ya faru a karamar hukumar Yauri, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 14, mafi yawansu mata 'yan rakiyar amarya.

Gwamna Nasir Idris ya jajanta wa iyalan mamatan, Masarautar Yauri da mazauna yankin, inda ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi mai raɗaɗi da ya jefa jihar cikin jimami.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ware Naira biliyan 1, zai ciyar da talakawa abinci a watan Ramadan

Yadda aka yi jana'izar 'yan rakiyar Amarya a Kebbi
Wajen sallar gawar 'yan rakiyar amarya a Kebbi. Hoto: Ashiru Bello Kane
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa hatsarin ya faru ne a ƙauyen Gumbi da ke karamar hukumar Yauri bayan raka amarya zuwa gidan mijinta a ƙauyen Gwarzo da ke karamar hukumar Ngaski a Kebbi.

Sakon ta'aziyyar gwamnan jihar Kebbi

Gwamnan jihar da shugaban karamar hukumar Yauri, Abubakar Shu’aibu, ya wakilta a sallar jana’iza, ya buƙaci iyalai da al’ummomin da abin ya shafa da su yi haƙuri tare da ɗaukar lamarin a matsayin ƙaddarar Allah Maɗaukakin Sarki.

Vanguard ta rahoto ya ce:

“Ina roƙonku da ku karɓi wannan lamari da zuciya ɗaya, ku tuna cewa babu abin da ke faruwa sai da sanin Mahaliccinmu,”
“Allah yana aikata abin da Ya so a lokacin da Ya so, kuma babu wanda ke da ikon tambayarsa.”

Yadda 'yan rakiyar amarya suka rasu

Da yake ƙarin bayani kan hatsarin, Hon. Shu’aibu ya ce mutanen na dawowa ne daga rakiyar amarya lokacin da jirgin ruwan da ake zargin ya yi lodi fiye da kima ya kife tare da jefa fasinjoji cikin ruwa.

Kara karanta wannan

Shekarau: Yayan tsohon gwamnan Kano ya riga mu gidan gaskiya bayan jinya

Ya kara da cewa:

“Sama da mutum 100 ne ke cikin jirgin ruwan lokacin da hatsarin ya faru. Abin takaici, mutum 14 — mata 13 da yaro guda — sun rasa rayukansu,”
Taswirar jihar Kebbi
Taswirar jihar Kebbi a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

An yi jana'izar 'yan rakiyar amarya

Shugaban karamar hukumar Yauri ya ƙara da cewa an birne mamatan bisa koyarwar addinin Musulunci, inda aka yi musu addu’o’in neman gafara da rahama.

“Muna roƙon Allah (SWT) Ya gafarta musu kura-kuransu, Ya kuma ba su Aljannatul Firdausi. Haka kuma muna roƙonSa Ya ba iyalansu da Masarautar Yauri baki ɗaya juriyar ɗaukar wannan babban rashi,”

- Inji shi

Gwamnatin jihar ta sake jaddada tausayinta ga al’ummar Yauri, tare da tabbatar musu da goyon baya a wannan lokaci na jimami, sakamakon ɗaya daga cikin munanan hatsarin jirgin ruwa da aka fuskanta a yankin a ‘yan shekarun nan.

Ana adawa da 'yan Arewa a Rivers

A wani labarin, mun kawo muku cewa an yi zanga-zangar adawa da jinin 'yan Arewa a birnin Fatakwal na jihar Rivers saboda wani rikici da aka yi.

Kara karanta wannan

'Da sauran rina kaba': DSS ta 'gano' shirin sake kai mummunan hari a Kwara

Rahotanni sun nuna cewa masu zanga-zanga sun bukaci gwamnatin jihar ta fatattaki 'yan Arewa da ke zaune a Rivers zuwa jihohinsu.

Shugaban Hausawa mazauna jihar Rivers ya yi Allah wadai da zanga-zangar tare da kira ga jami'an tsaro su gaggauta daukar mataki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng