An Sace Amarya Da Y'an Rakiyar ta 10 Kan Hanyar su Ta Zuwa Gidan Angonta
Wani labari da ya kidima daukacin al'ummar garin Birnin Gwari dake jahar Kaduna, shine na wayar gari da jin labarin sace amarya da yan rakiyarta su goma a jiya Asabar da misalin karfe 8:00 na dare.
Premium Times ta rawaito cewa, uku daga cikin wadanda aka sace sun sami damar kubuta.
Wani tsohon shugaban karamar hukumar Birnin Gwari da ya nemi a sakaya sunansa yace:
"Titin zuwa Funtua ya zame mana barazana domin, a kowanne lokaci za ka iya kacibus da irin wadan nan mutanen. Suna cin karen su babu babbaka saboda kamar iyaka ce tsakanin Birnin Gwari da Katsina."
Ko a Juma'ar da ta gabata, an sace wasu matasa biyu kusa Uduwa dake Birnin Gwarin dai. Hakazalika kwanan nan ne aka kaiwa wasu sojoji hari a yankin, wanda yayi sanadiyyar hallaka sojoji bakwai a yankin.
DUBA WANNAN: Sanata Shehu Sani ya kara rubutawa Buhari wasika a karo na biyu, ya bashi wata shawara
A wani labarin dsa Legit.ng ta wallafa, kun ji cewar, Sanata mai wakiltar jihar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai, Shehu Sani, ya sake aike da wani sako ga shugaba Buhari a karo na biyu cikin sati guda.
Sanatan ya aike da sakon ne biyo bayan barkewar cece-kuce a kan wata kyauta da gidauniyar tsohon mai fafutikar neman 'yan bakaken fata a kasar Amurka, Martin Luther king (MLK), ta bawa shugaba Buhari.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng