Harin 'Yan Bindiga Ya Ritsa da Shugaban Karamar Hukuma a Kaduna, an Kashe Mutane

Harin 'Yan Bindiga Ya Ritsa da Shugaban Karamar Hukuma a Kaduna, an Kashe Mutane

  • ’Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Kaduna da ke yankin Arewa maso Yamma na Najeriya
  • Tsagerun 'yan bindigan sun kashe mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a harin wanda suka kai a karamar hukumar Kajuru
  • Harin na 'yan bindiga ya kuma jawo an kona motocin manyan mutane a wurin jana'izar mahaifin wani babban dan siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai harin ta'addanci a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

'Yan bindigan sun kashe mutane biyu tare da kona motar shugaban karamar hukumar Kajuru, yayin wani hari da suka kai a kauyen Ugom.

'Yan bindiga sun kashe mutane a Kaduna
Taswirar jihar Kaduna, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa 'yan bindigan sun kai harin ne a ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 200 sun shiga garuruwa 3 da Asubah, sun kashe mutane sama da 30

'Yan bindiga sun kashe mutane a Kaduna

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun mamaye unguwar Ehwakya da ke cikin kauyen, inda suka riƙa harbin kan mai uwa da wabi, lamarin da ya jefa mazauna garin cikin firgici.

Majiyoyi daga yankin sun bayyana sunayen waɗanda suka riga mu gidan gaskiya a matsayin Bitrus David (ɗan shekara 25) da kuma Goma Idi (ɗan shekara 40).

An kuma bayyana cewa maharan sun mamaye yankin Dogon-Noma, inda mutane suka taru domin jana’izar mahaifin wani ɗan siyasa mai suna Usman D. Stingo.

Wasu ganau sun bayyana cewa mutanen da suka zo jana'izar sun tsere domin tsira da rayukansu yayin da maharan suka buɗe wuta kusa da wurin jana’izar.

An kona motar shugaban karamar hukuma

Yayin harin na 'yan bindiga, an kona akalla motoci huɗu, ciki har da motar shugaban karamar hukumar, Dauda Madaki, da kuma motar shi kansa Usman D. Stingo.

Shugaban kungiyar ci gaban Ugom, Onnusim Alhaji Ishaya, ya bayyana harin a matsayin abin banza da takaici.

Kara karanta wannan

Shiri ya baci: 'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda da fararen hula a Benue

“’Yan bindiga sun kai hari ga al’ummarmu, suna harbi ba kakkautawa. An tabbatar da mutuwar matasanmu biyu. A wurin jana’iza da ke Dogon-Noma, an kona motoci, har da ta shugaban ƙaramar hukumar.”

- Onnusim Alhaji Ishaya

Ya kara da cewa har zuwa lokacin bayar da wannan rahoton, ba a san inda wasu mazauna garin suke ba, inda ya yi kira ga hukumomin tsaro da su kawo dauki cikin gaggawa.

'Yan bindiga sun kai hari a Kaduna
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani Hoto: @ubasanius
Source: Facebook

Me 'yan sanda suka ce kan lamarin?

Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya ci tura.

Legit Hausa ta kira wayarsa domin samun karin bayani da tabbatar da aukuwar harin, amma bai dauka ba, bai kuma biyo ba har zuwa lokacin kammala hada wannan rahoton.

'Yan bindiga sun kashe mutane

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-haren ta'addanci a wasu garuruwa na jihar Neja.

Tsagerun 'yan bindigan sun kashe aƙalla manoma 32 a jerin hare-hare da suka kai kan garuruwan Tunga-Makeri, Konsoko da Pissa a karamar hukumar Borgu.

Majiyoyi sun bayyana cewa maharan wadanda yawansu ya kai sama da 200, sun kwashe sa’o’i suna aikata ta’asar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng