Kurunkus: Hedkwatar Tsaro Ta Yi Magana kan Jiragen Sojojin Amurka da Suka Shigo Najeriya

Kurunkus: Hedkwatar Tsaro Ta Yi Magana kan Jiragen Sojojin Amurka da Suka Shigo Najeriya

  • Hedkwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta tabbatar da isowar dakarun sojojin Amurka 100 a wani bangaren yarjejeniyar da aka cimma
  • A kwanakin da suka gabata ne aka ga jiragen sojojin Amurka sun sauka da jami'ai a jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya
  • Mai magana da yawun DHQ, Manjo Janar Sama'ila Uba ya ce jami'an za su taimaka wa dakarun Najeriya a fannin horarwa da leken asiri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hedkwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta share duk wata tantama game da rahoton da ke yawo na isowar dakarun sojojin Amurka 100 cikin kasar nan.

Hedkwatar Tsaro (DHQ) ta sanar tare da tabbatar da isowar kusan jami’an sojojin Amurka 100 tare da kayan aiki masu alaka da su a filin tashi da saukar jirage na Bauchi.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun kashe kwamandan Boko Haram, an kwato miliyoyin kudade

Dakarun sojojin Amurka.
Dakarun rundunar sojojin sama na kasar Amurka a bakin aiki Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun DHQ na kasa, Manjo Janar Sama'ila Uba ya rattaba wa hannu kuma aka wallafa ta a shafin X yau Litinin.

Abin da ya kawo sojojin Amurka 100 Najeriya

Jamar Uba ya ce zuwan dakarun sojojin yana daya daga cikin yarjejeniyar da aka cimma a tattaunawar da ta gudana tsakanin wakilan Najeriya da takwarorinsu na Amurka.

A cewarsa, gwamnatin Najeriya ce ta nemi Amurka ta turo dakarun sojoji masu kwarewa da za su taimaka wajen yaki da ta'addanci.

Ana sa ran sojojin Amurka za su tallafa wa fannin horar da sojojin Najeriya, tallafin fasaha, da kuma musayar bayanan sirri domin ganin an kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.

Wannan hadin gwiwa zai ba da damar samun kwarewar fasaha ta musamman da nufin inganta karfin Najeriya wajen dakile barazanar ‘yan ta’adda da kuma inganta kariya ga mutanen da ke cikin hatsari a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Bukarti: Abubuwa 3 da Najeriya za ta kiyaye bayan sojojin Amurka sun sauka Borno

Taimakon da sojojin Amurka za su ba Najeriya

Hedkwatar tsaro ta ce:

"Jami’an sojojin Amurkan da aka turo kwararru ne a fannin fasaha, kuma za su yi aiki ne kawai a matsayin masu ba da shawara da horarwa, ba dakarun yaki ba ne.
"Dukkan ayyukan horarwar da za a shirya za su kasance ne a karkashin iko, umarni, da kulawar Gwamnatin Najeriya, tare da hadin gwiwar Rundunar Sojin Najeriya.
"Sojojin Najeriya, tare da da wadanda aka turo daga Amurka, za su fara shirya tarukan horarwaa da kuma ayyukan hadin gwiwa da za su maida hankali kan leken asiri
"An dauki wannan mataki ne son bunkasa karfin sojojin Najeriya wajen ganowa da kuma murkushe kungiyoyin ‘yan ta’adda masu tsattsauran ra'ayi da ke neman dagula zaman lafiyar kasar."
Hafsan tsaro.
Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Olufemi Olatubosun Oluyede Hoto: @DHQNigeria
Source: Facebook

Rundunar Sojin Najeriya ta sha alwashin ci gaba da jajircewa wajen ganin ta kakkabe kungiyoyin ‘yan ta’adda da ke barazana ga tsaron kasa, da kuma lafiyar ‘yan kasa.

Hedkwatar Tsaro ta kuma ba ‘yan Najeriya tabbacin za ta ci gaba da fada masu gaskiya da kuma samar da sahihan bayanai a kan lokaci dangane da wannan hadin gwiwar sojoji.

Kara karanta wannan

Da sake: ADC ta dura a kan Tinubu saboda yunkurin kama El Rufa'i

Hedkwatar tsaro ta fara cika umarni a Kwara

A wani labarin, kun ji cewa hedkwatar rundunar tsaron Najeriya ta sha alwashin kamo duk mai hannu a harin da aka kashe rayukan musulmi fiye da 100 a jihar Kwara.

Bayan umarnin shugaban ƙasa, Hedkwatar Tsaro tare da haɗin gwiwar Hedkwatar Rundunar Sojin Ƙasa (AHQ) da sauran rassa, sun ƙaddamar da runduna ta musamman mai suna Operation Savanah Shield.

Wannan runduna za ta mayar da hankali ne wajen fatattakar maboyar 'yan ta'adda da ke addabar jihohin Kwara da Neja

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262