NiMet Ta Gargadi Kamfanonin Jiragen Sama, Ta Hango Matsala a Kano da Jihohi 10
- Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen cewa za a samu hazo da kura a wasu sassan Kano da jihohi 10 a Arewacin Najeriya
- NiMet ta gargadi kamfanonin sufurin jiragen sama da su yi taka tsan-tsan don gudun samun hatsari sakamakon hazo, wanda zai haddasa rashin gani
- Ta kuma gargadi mutane masu fama da lalurar asma da sauran larurori masu alaka da numfashi da su kula da kansu matuka a yanayin da ake ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet), ta yi hasashen samun guguwa mai kura da hazo da wasu jihohin kasar nan.
Bisa haka ne hukumar NiMet ta gargaɗi kamfanonin sufurin jiragen sama da ke aiki a Najeriya da su kula, domin hazo na iya shafar ayyukansu.

Source: Twitter
Hukumar NiMet ta bayyana wannan gargadi ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X yau Litinin, 16 ga watan Fabrairu, 2025.
A sanarwar mai kunshe da hasashen yanayi da ta saba fitar wa na yau da kullum, NiMet ta bayyana cewa yanzu haka ana fama guguwa mai hade da ƙura a ƙasashen Chadi da Nijar da je makwaftaka da Najeirya.
Hukumar NiMet ta ce:
"Yanzu haka ana fama da matsalar guguwa da hazo a Chadi da Jamhuriyar Nijar. Ana sa ran hazon zai tunkari Arewa da kimanin gudun mita 800 tare da knots 25-30, wnada hakan na iya kai hazon zuwa yankunan Arewacin Najeriya."
Jerin jihohin da za a samu hazo
Hukumar NiMet ta ƙara da cewa ƙura mai kauri, wadda ka iya rage gani a sararin sama zuwa mita 1,000 ko ƙasa da haka, za ta shafi wasu sassan jihohin Najeriya guda 11.
Jihohin da NiMet ta ambata, wadanda za a samu hazo sun hada da Sokoto Zamfara, Kebbi, Katsina, Kano, Kaduna, Yobe, Jigawa, Bauchi, Gombe da kuma Borno.
NiMet ta shawarci kamfanonin jiragen sama da kuma al’umma su ɗauki matakan kariya da suka dace domin kaucewa hatsari ko matsalolin da suka shafi lafiya.
Gargaɗi ga masu larurar numfashi
Hukumar ta kuma yi kira ga mutanen da ke fama da cututtukan asma da sauran matsalolin numfashi da su yi taka-tsantsan saboda yanayin da ake ciki.
Bugu da ƙari, ta ba kamfanonin jiragen sama shawarar su riƙa samun takamaiman rahoton yanayi na filayen jiragen sama daga NiMet domin tsara ayyukansu yadda ya kamata.

Source: Getty Images
Hazo a sararin samaniya na daya daga cikin abubuwan da ke jawo soke tashin jiragen sama saboda gudun samun matsala, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
NiMet ta yi hasashen samun ruwa a jihohi 15
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar NiMet ta yi hasashen samun ruwan sama da wuri a Kano, Neja da wasu jihohi 13 a kakar damina ta shekarar da muke ciki, 2026.
Ministan Sufurin Jiragen Sama da Harkokin Sararin Samaniya na Najeriya, Festus Keyamo , ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Talata da ta gabata.
Ministan ya jaddada cewa ana sa ran samun matsanancin yanayi tsakanin watan Maris zuwa Mayu, wanda zai iya shafar ayyukan yau da kullun a kasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

