Kano: Manyan Mutane da Suka Ziyarci Kasuwar Singer bayan Mummunar Gobara
Gobarar kasuwar Singer da ta sake ɓarke wa a ranar Asabar, 14 ga watan Fabrairu, 2026 ta girgiza jihar Kano bayan ta ɗauki kwanaki tana ci, gabanin wannan, an samu wata gobarar a ranar Alhamis ga watan Fabrairu, 2026.
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Tun bayan ɓarkewar gobara a kasuwar Singer da ke cikin birnin Kano, wasu manyan shugabannin jihar da suka haɗa da Gwamna Abba Kabir Yusuf suka kai ziyara waurin.

Source: Facebook
Kafin gobarar da aka yi a tsakiyar watan nan na Fubrairu wanda ita ce ta fi muni, kasuwar mai fitaccen tarihi ta kama da wuta mako daya gabanin nan.
Legit ta tattaro jerin shugabannin da suka kai ziyara domin jajanta wa yan kasuwar, yayin da wadansu suka fara bayar da gudunmawa.
Shugabannin da suka ziyarci kasuwar Singer a Kano
1. Gwamna Abba Kabir Yusuf
Hadimin gwamnan Kano, Sanusi Bature D-Tofa, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya isa kasuwar Singer a daren da gobarar ta tashi.
Gwamnan ya kai ziyarar ne yayin da wutar ke ci gaba da yaɗuwa, tana lalata shaguna da kayayyakin yan kasuwar.

Source: Facebook
A ziyarar, Gwamna Abba ya roƙi Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta kai ɗauki ta hanyar samar da na’urorin kashe gobara na zamani.
Daga cikin abubuwan da ya nema har da tallafin jiragen sama da sauran kayan aiki masu muhimmanci domin shawo kan lamarin da kuma hana faruwar irin gobarar a nan gaba.
2. Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II
Ƙungiyar ƴan kasuwar Singer ta sanar da ziyarar da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya kai kasuwar a yammacin ranar Lahadi, 15 ga watan Fabrairu, 2026.

Source: Twitter
Sarkin ya shiga kasuwar tare da rakiyar tawagarsa, inda ya zagaya domin ganin irin barnar da gobarar ta yi da kuma jajanta wa waɗanda abin ya shafa.
3. Mustapha Rabi’u Musa Kwankwaso
Tsohon Kwamishinan Matasa da Wasanni, Hon. Mustapha Rabi’u Musa Kwankwaso, shi ma ya kai ziyara kasuwar domin jajanta wa ƴan kasuwar da wannan ibtila’i ya rutsa da su.
Aliyu Yakubu Sarauta ne ya wallafa hakan a shafinsa na Facebook, inda tsohon kwamishin ya jajanta wa yan kasuwa.
4. Abdullahi Umar Ganduje
Tsohon Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ziyarci kasuwar Singer a ranar Lahadi, 15 ga watan Fabrairu.
Dr, Ganduje ya yi shekaru takwas yana mulki a Kano kuma ya gamu da irin wannan matsala lokacin daya yi mulki.

Source: Twitter
5. Nentawe Yilwatda
A wani bidiyo da Premier Radio ta wallafa a shafinta na Facebook, an ga Ganduje tare da Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda.
Nentawe da magabacinsa sun jajanta wa ƴan kasuwar tare da ba su haƙuri, suna addu’ar Allah Ya mayar masu da alheri fiye da abin da suka rasa.
6. Barau I Jibrin
Jaridar Daily post ta wallafa cewa Sanata Barau I Jibrin ya kai ziyarar jaje kasuwar Singer inda ya mika tallafin Naira miliyan 100 ga yan kasuwa.

Source: Facebook
A yayin ziyarar, ya bayyana cewa wannan gobara ba iya yan kasuwar ta shafa ba, har da dukkanin al'ummar Kano.
Ya yi addu'ar Allah Ya mayar wa ƴan kasuwa da alheri da fatan hakan ba za ta sake faruwa a nan gaba ba.
7. Ibrahim Shekarau
Premier Radio ta wallafa a shafin Facebook cewa cewa tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya kai ziyartar jaje kasuwar Singa, biyo bayan samun gobara a kasuwar.
Malam Ibrahim Shekarau ya samu tarba daga shugabanni da 'yan kasuwar da sauran al'umma.
8. Rabiu Kwankwaso
Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyarar jaje kasuwar Singer a gobarar da ta tashi a makon da ya gabata.

Source: Facebook
Tsohon gwamnan ya taya su alhini, tare da fatan Allah Ya mayar wa da yan kasuwa da suka yi asarar dukiyoyinsu da alheri.
9.Peter Obi
This day ta wallafa cewa dan takarar shugaban kasa na LP a zaben 2023, Peter Obi, a jiya ya ziyarci kasuwar Kano domin jajantawa wadanda gobarar da ta jawo asarar miliyoyin Naira.

Kara karanta wannan
Aminu Vs Sanusi II: Gwamna Abba ya sake tabo batun rikicin sarautar Kano a gaban Sanata Barau
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya jajanta wa wadanda abin ya shafa, ya kuma yi alkawarin ba su tallafin kudi da ba a bayyana ba.
10. Kashim Shettima
Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima ya jagoranci tawagar Fadar Shugaban kasa zuwa kasuwar Singer a ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairu, 2026.
An kiyasta cewa gobarar ta kone kayayyaki da dukiyoyi da darajarsu ta haura Naira biliyan biyar, inda ta shafi fiye da shaguna 1,000. Har yanzu ba a ga wasu mutane bakwai ba.

Source: Twitter
Gobarar ta tashi ne da yammacin ranar Asabar, 14 ga Fabrairu, 2026, a sashen Gidan Glass na kasuwar da ke kan titin Ado Bayero, inda ta ci gaba da ci har zuwa safiyar Litinin.
Ziyarar da Shettima ya kai ta biyo bayan umarnin Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, wanda ya umarci Mataimakin Shugaban Ƙasar da ya jagoranci tawagar domin duba lamarin.
An yi gobara a Kano
A baya, mun wallafa cewa an shiga jimami bayan gobarar da ta barke a wata kasuwa da ke jihar Kano ta haddasa mummunar asara mai tarin yawa.
Lamarin ya faru ne a kasuwar kayan gado ta Sabuwar Lale da ke unguwar Tal’udu, a karamar hukumar Gwale ta jihar Kano, inda wuta ta tashi a cikin dare.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 2:30 na dare, lamarin da ya jefa ’yan kasuwa cikin tashin hankali da lalata dukiyoyi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



