Shirin da Ya Kamata Musulmai Su Yi kafin 1 ga Watan Ramadan

Shirin da Ya Kamata Musulmai Su Yi kafin 1 ga Watan Ramadan

Ana bukatar al'ummar Musulmi su yi shiri na musamman domin samun damar yin ibada a Ramadan, a kan haka muka tattaro muku abubuwan da ya kamata ku yi kafin 1 ga wata.

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ramadan wata ne da al'ummar Musulmi ke gudanar da ibada a kowace shekara domin neman kusanci da Allah Madaukakin Sarki.

Kasancewar wata ne da ake ibada da suka hada da azumi, sallah, sadaka, da sauransu, ana so kowane Musulmi ya yi shiri na musamman.

Yadda Musulmai ke sallar tarawih
Ana sallar tarawih a hagu, wata a sama a gefen dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A wannan rahoton, mun tattaro muku wasu muhimman abubuwa da ya kamata kowane Musulmi ya yi domin shirin maraba da Ramadan 2026.

Muhimmancin shirya wa Ramadan 2026

Shafin Muslim Aid ya wallafa cewa Ramadan lokaci na mai muhimmanci wanda shiri mai kyau zai sa a samu nasara da fa’ida sosai a cikinsa.

Kara karanta wannan

Dalilan da ke sanya ranakun fara Ramadan sauyawa kowace shekara

Ya bayyana cewa ya kamata shirye-shiryen Ramadan su haɗa da tsara rayuwa tun kafin 1 ga wata, da sauya jadawalin yau da kullum domin dacewa da:

  • Lokacin sahur
  • Buda-baki bayan faduwar rana
  • Sallar Tarawihi
  • Tsara lokacin karatun Alƙur’ani da sauransu
Ana salar tarawih a Makkah
Yadda ake sallar tarawih a Makkah. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shirin kafin 1 ga Ramadan ga Musulmi

1. Tabbatar da ranar fara azumi

An bayyana cewa tabbatar da ranar fara azumi farilla ne a kan dukkan wanda zai gabatar da azumi, domin hakan ne zai ba mutum damar yin niyya kafin alfijir ya keto.

Mutum zai gane haka ne ta hanyar sanarwar da Mai alfarma Sarkin Musulmi zai yi a Najeriya da cewa an ga wata ko za a cika kwana 30.

Mai alfarma Sarkin Musulmi a fadarsa
Sarkin Musulmi zaune a fadarsa. Hoto: National Moon Sighting Committee
Source: Facebook

2. Sanin muhimman lokuta a Ramadan

Yana da kyau kowane Musulmi ya san lokutan fara sahur da karshensa da lokutan buda baki. Hakan zai taimaka wajen kauce wa fadawa matsalar cin abincin sahur bayan lokaci ya kure ko shan ruwa kafin lokaci ya yi.

Baya ga lokutan buda baki da sahur, yana da muhimmanci ga kowane Musulmi ya san lokutan salloli biyar da na tarawihi domin zuwa masallaci a kan lokaci.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ware Naira biliyan 1, zai ciyar da talakawa abinci a watan Ramadan

Agogon lokutan sallah
Yadda agogon lokutan sallah ke aiki. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

3. Tsara lokutan ibada a Ramadan

Musulmi na bukatar tsara jadawalin ibada na yau da kullum, hakan yana da matukar muhimmanci domin zai ba mutum damar yin ayyuka yadda ya kamata. Mutum zai iya ware lokutan yin:

  • Karatun Alƙur’ani
  • Addu’o’i
  • Zikiri
  • Zuwa tafsiri da sauransu
Yadda Musulmi ke karatun Qur'ani
Wasu musulmai na karatun Qur'ani a Kashmir. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

4. Shirya jerin addu’o’i a Ramadan

Daga cikin abubuwan da ya kamata mai shirin shiga Ramadan ya yi akwai lissafa manyan abubuwan da ya ke bukata domin yin addu'a ta musamma a kansu.

Sheikh Muhammad Salih Al-Munajid ya wallafa cewa akwai lokuta na musamman da ake amsa addu'o'i a Ramadan, saboda haka ya dace mutum ya ribaci lokutan.

Mutum zai iya lissafa:

  • Abubuwan da ya ke son roƙa
  • Kura-kuran da ya ke son neman gafara a kansu
  • Addu'ar da zai yi wa 'yan uwansa
  • Addu'ar da zai yi wa kasarsa da sauransu
Musulmai na addu'a a masallaci
Yadda wasu Musulmai ke addu'a a Masallaci. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Baya ga wadannan abubuwa, ya kamata mutum ya tabbatar yana da ilimi a kan ayyukan ibada da ake yi a Ramadan, abubuwan da suka shiga masa duhu ya tambayi malaman addinin Musulunci.

Kara karanta wannan

Sojan Amurka dan asalin Najeriya ya nutse a teku bayan fadowa a jirgin yaki

An bayyana cewa ya kamata mutum ya samu ilimi a kan abubuwa da suka hada da zakkar fidda a kai da ake yi a karshen azumi da sauransu tun kafin shiga Ramadan.

Za a duba watan Ramadan 1447

A wani labarin, kun ji cewa mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi kira ga 'yan Najeriya su fita duba jinjirin wata a ranar Talata, 17 da Fabrairun 2026.

Ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da majalisar kolin addinin Musulunci ta Najeriya ta fitar tana kira ga dukkan Musulmai.

Sanarwar ta bayyana cewa Musulman Najeriya da ma fadin duniya sun fuskanci kalubale mai girma a shekarar 2025 da ta wuce.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng