Dalilan da ke Sanya Ranakun Fara Ramadan Sauyawa Kowace Shekara
- Al'ummar Musulmi a fadin duniya sun fara shirye-shirye yayin da ake daf da fara azumin watan Ramadan na shekarar 2026 da muke ciki
- Kusan duk shekara a kan samu sauye-sauye a kan lokacin da ake fara azumi, galibi yana yin baya idan aka kwatanta da shekarar da ta wuce
- A wannan rahoton, Legit Hausa ta yi nazari game da dalilan da suka sanya lokacin fara azumi ke sauya wa a duk shekara a duniya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ana sa ran watan Ramadan na shekarar 2026 zai fara a ranar 18 ko 19 ga Fabrairu, gwargwadon yadda aka ga jinjirin wata.
A cikin watan, Musulmin da ke azumi za su kaurace wa ci da sha daga fitowar alfijir zuwa faɗuwar rana, yawanci na tsawon awa 12 zuwa 15, gwargwadon inda suke zaune.

Source: Getty Images
Tashar Al-Jazeera ta hada wani rahoto na musamman a kan abin da ya shafi bambancin da ake samu a lokutan fara azumi a kowace shekara.
Lokacin fara Ramadan na bambanta
Binciken masana ya nuna cewa watan Ramadan kan fara kwanaki 10 zuwa 12 da wuri a kowace shekara a kan shekarar da ta gabata.
An bayyana cewa hakan na faruwa ne domin kalandar Musulunci tana dogara ne da kalandar Hijira, wadda watanninta ke ɗaukar kwanaki 29 ko 30.
A shekarar 2025, rahoton Daily Trust ya nuna cewa na fara azumin Ramadan a Najeriya a ranar 1 ga Maris. Lamarin da ke nuna za a iya samun bambancin kusan kwana 10 a bana.
Sa'o'in da ake azumi a fadin duniya
Ga kusan kashi 90 cikin 100 na al’ummar duniya da ke zaune a Arewacin duniya, adadin awannin azumi zai ɗan ragu a wannan shekara, kuma zai ci gaba da raguwa har zuwa shekarar 2031.
Sabanin haka, ga Musulmin da ke zaune a Kudancin duniya kuma, awannin azumin shekarar 2026 za su fi na bara tsawo.
Saboda shekarar wata ta fi shekarar rana gajarta da kwanaki 11, za a yi Ramadan sau biyu a shekarar 2030. Rahotanni sun nuna cewa na farko zai fara a ranar 5 ga Janairu, sannan na biyu ya fara a ranar 26 ga Disamba.

Source: Getty Images
Tunda yanzu lokacin sanyi ne a Arewacin duniya, a Ramadan na bana, mutanen da ke zaune a can za su yi azumi mafi gajerta, wanda zai kai kimanin awa 12 zuwa 13 a ranar farko, sannan awannin su ƙaru a hankali yayin da watan ke tafiya.
Mutanen ƙasashen Kudanci kamar Chile, New Zealand da Afirka ta Kudu za su yi azumi mafi tsawo, kimanin awa 14 zuwa 15 a ranar farko. Sai dai kuma awannin azumin za su ragu a hankali yayin da watan ke ci gaba.
Za a fara azumin Ramadan a Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa fadar mai alfarma Sarkin Musulmi ta bukaci a fara duba watan Ramadan na 2026 a Najeriya.
Za a fara duba watan Ramadan a Najeriya ne a ranar Talata, 17 ga watan Fabrairun shekarar 2026 a fadin kasar nan.
Majalisar koli ta addinin Musulunci a Najeriya ta yi magana kan matsalolin da ke addabar al'ummar Musulmi a Najeriya.
Asali: Legit.ng


