Aminu Vs Sanusi II: Gwamna Abba Ya Sake Tabo Batun Rikicin Sarautar Kano a gaban Sanata Barau
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce addu'o'in neman hadin kai da zaman lafiya tsakanin jagororin siyasar Kano sun fara haifar da sakamako
- Abba Gida-Gida ya sake jaddada cewa nan ba da jimawa ba, za a warware rikicin sarautar Kano ta hanyar da kowame bangare zai gamsu
- Mataimakin shugaban Majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya bukaci sauran jihohi da su yi koyi da Kano wajen shirya tarukan addu'o'i
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Gwamnan jihar Kano, Abba Akbir Yusuf ya bayyana cewa an fara samun zaman lafiya da hadin kai a tsakanin shugabannin siyasa na jihar.
Gwamnan ya ce sadaukarwar da aka yi kwanan nan ta hanyar mika komai ga Allah Madaukakin Sarki domin neman hadin kai, zaman lafiya, da ci gaba a Jihar Kano tuni ta fara samar da sakamako mai kyau.

Kara karanta wannan
Bidiyo: Yadda gobara ke cinye Kasuwar Singer, Gwamna Abba Ya Nemi Taimakon Tinubu

Source: Facebook
Wannan bayanin yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu kuma ya wallafa a shafin Facebook yau Lahadi.
Abba Gida-Gida ya kafa hujja da halartar shirye-shiryen jiha da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya yi a matsayin wata alama bayyananna ta karuwar fahimta tsakanin jagororin siyasa a jihar.
Gwamna Abba ya tabo rikicin sarautar Kano
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron addu’a da saukar Alkur'ani na musamman karo na biyu, inda mahaddata 4,444 suka taru a gidan gwamnatin Kano a ranar Asabar.
Ya nuna kwarin gwiwar cewa, sakamakon wadannan addu’o’i da mahaddatan suka yi, nan ba da dadewa ba za a sasanta takaddamar Masarautar Kano cikin ruwan sanyi ta hanyar da za ta gamsar da dukkan bangarorin da abin ya shafa.
Abba Kabir ya jaddada cewa zai yi duk abin da zai iya don hada kan ‘yan siyasar Kano, inda ya bukace su da su guji siyasar gani kashe-ni, maimakon haka su rungumi girmama juna da fahimtar juna.
Gwamna Abba zai tsaftace siyasar Kano
Haka kuma, ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na kawar da bangar siyasa a jihar, yana mai takaicinta cewa matasan da ke shiga irin wadannan ayyuka ‘yan jihar ne wadanda ya kamata su bada gudunmawa mai kyau ga ci gaban Kano.
Ya tabbatar wa mazauna Kano cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da ayyukan da da za su taimaki ratuwar jama'a kai-tsaye.
Gwamnan ya yaba wa mahaddatan Alkur’anin bisa sadaukar da lokacinsu da karfinsu wajen yin addu’ar neman ci gaba da daidaiton jihar.
Jawabin Sanata Barau Jibrin
A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya yaba wa hangen nesa na Gwamna Abbawajen kaddamar da shirin addu’ar hadin kai.
Ya bukaci sauran jihohin kasar nan da su yi koyi da Kano ta hanyar shirya makamantan wadannan tarukan addu’o’i don samar da zaman lafiya mai dorewa da dunkulewar kasa.

Source: Facebook
Tun da farko, Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya yi kira ga mazauna jihar da su ci gaba da kasancewa masu jajircewa wajen addu’o’in dorewar ci gaban Jihar Kano da ma Najeriya baki daya.

Kara karanta wannan
Babbar magana: Ganduje ya yi magana kan batan Dadiyata, ya maida martani ga El Rufai
Barau ya yiwa Gwamna Abba alkawari
A wani labarin, kun ji cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yi alkawarin samar wa yan takarar APC kuri'u masu yawa a zaben 2027.
Sanata Barau ya bayyana aniyarsa ta tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Abba Kabir Yusuf sun samu kuri’u masu yawa da za su kai su ga nasara a zaben badi.
Barau ya ce shugabannin APC a Kano ta Arewa sun cimma matsaya daya tare da kudirin hada kai domin ganin jam’iyyar ta samu nasara.
Asali: Legit.ng
