Gwamna Abba Ya Tsige na Hannun Daman Kwankwaso daga Kujerarsa

Gwamna Abba Ya Tsige na Hannun Daman Kwankwaso daga Kujerarsa

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauke Buba Galadima daga kujerar shugaban majalisar gudanarwa ta kwalejin kimiyya da fasaha a jihar
  • Sanarwar da hadimin Gwamna Sanusi Bature D-Tofa ya fitar ta tabbatar da cewa an sauke Injiniya Buba Galadima kafin wa'adinsa ya cika
  • Sanarwar ta kara da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya maye gurbin Buba Galadima domin a samu damar cimma muradun da aka tsara

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauke Injiniya Buba Galadima daga mukamin shugaban majalisar gudanarwa ta kwalejin kimiyya da fasaha a jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Asabar, 14 Fabrairu 2026.

Kara karanta wannan

An kada hantar Kwankwaso, Barau ya yi alkawari ga Abba, Tinubu kan zaben 2027

Gwamnatin Kano ta sauke Buba Galadima daga mukami
Injiniya Buba Galadima, Gwamna Abba Kabir Yusuf Hoto: Buba Galadima/Sanusi Bature D-Tofa
Source: Twitter

A sanarwar da ya wallafa a shafin Facebook, Sanusi Bature ya ce an yanke shawarar sauke Injiniya Buba Galadima ne saboda ci gaban jihar Kano.

Dalilin Abba na sauke Buba Galadima

Sanarwar ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan sake fasalin tsare-tsare da kuma daidaita ayyukan cibiyar da shirin sanya Kano a gaba na gwamnatin jihar.

Ta ce ko da yake wa’adin majalisar gudanarwar na tsawon shekara uku ne, an dakatar da nadin shugaban kafin cikar wa’adin sakamakon gyare-gyaren da ake yi domin inganta makarantar.

Gwamnan Kano ya godewa Buba Galadima
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Gwamna Yusuf ya gode wa Injiniya Buba Galadima bisa gudunmawar da ya bayar a lokacin da yake rike da mukamin shugaban majalisar gudanarwar.

Sannan sanarwar ta bayyana wanda zai maye gurbin Injiniya Buba Galadima a matsayin Shugaban majalisar gudanarwar kwalejin.

Gwamna Abba ya naɗa sabon Shugaba

Gwamnan ya amince da nadin Sarkin Gaya, Aliyu Ibrahim Abdulkadir, a matsayin sabon shugaban majalisar gudanarwa a kwalejin kimiyya da fasaha.

Kara karanta wannan

An zo wajen: Gwamnatin Abba ta yi magana kan batun hana Kwankwaso zuwa Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bukaci sabon shugaban da ya yi amfani da kwarewarsa, gogewarsa da jajircewarsa wajen jagoranci domin sake fasalta makarantar.

Sanarwar ta ce gwamnatin jihar na sa ran sabon shugaban zai taka rawar gani wajen tabbatar da nagarta da inganci a harkokin makarantar.

Ya kuma yi fatan wannan sabon jagoranci zai taimaka wa gwamnatin Abba Kabir Yusuf wajen cimma muradun inganta makarantar da aka saka a gaba.

Wannan matakin da gwamnati ta dauka ta zo a lokacin da Buba Galadima ya soki Gwamna Abba Kabir Yusuf kan sauya sheka tare da rabuwa da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

Gwamnatin Abba ya naɗa Suraj mukami

A baya, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada Dr. Suraj Sulaiman a matsayin sabon Shugaban hukumar kididdiga ta jihar Kano biyo saboda kwarewarsa a ɓangaren ƙididdiga.

Sabon nadin ya biyo bayan kammala wa’adin Dr. Aliyu Isa Aliyu, wanda yanzu haka ya zama kwamishinan raya kiwo da gwamnatin Kano ta naɗa domin haɓaka kiwon dabbobi.

A cikin sanarwar da hadimin Gwamna, Sanusi Bature D-Tofa ya fitar, gwamnan ya yabi Suraj Yana maja zai taimaka wajen inganta tsarin gwamnati ta fuskar samar da sahihan bayanai

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng