Kwalejin kimiyya da fasaha na Adamawa za ta fara karatun digiri, in ji Rector

Kwalejin kimiyya da fasaha na Adamawa za ta fara karatun digiri, in ji Rector

- Kwalejin kimiyya da fasaha na jihar Adamawa ta fidda sanarwar fara karatun digiri a fannoni daban-daban

- Makarantar ta bayyana cewa ta samu nasarar samun lasisin karantar da wasu fannoni

- Makarantar ta bayyana cewa ta gama dukkan shiri don fara karatun a makarantar

Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Adamawa, Yola, tare da hadin gwiwar jami'ar Maiduguri, sun kammala shirye-shirye don fara ba da kwalin Digiri, The Nation ta ruwaito.

Farfesa Ibrahim Umar, Rector na makarantar, ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai ranar Talata a Yola.

Umar ya ce Majalisar Dattawan jami’ar ta bayar da amincewa kan shirye-shiryen da za su iya farawa a 2021.

KU KARANTA: Bamu gayyaci Sunday Igboho ya ya taya mu korar Fulani ba, gwamnan jihar Ogun

Kwalejin kimiyya da fasaha na Adamawa za ta fara karatun digiri, in ji Rector
Kwalejin kimiyya da fasaha na Adamawa za ta fara karatun digiri, in ji Rector Hoto: Ripples Nigeria
Source: UGC

“Kwalejin Kimiyya da Fasaha, tare da hadin gwiwar Jami’ar Maiduguri, sun amince da Shirye-shiryen karatun Digiri, bisa la’akari da amincewar karshe daga Hukumar Jami’o’i ta Kasa.

"An bai wa Makarantar Kimiyya da Fasahar cikakken tabbacin cewa shirye-shiryen za su fara a cikin 2021, kuma duk kayan aikin da ake bukata sun riga sun kasance a kasa don farawa." A cewar Umar.

Ya lissafa kwasa-kwasan digirin kamar Digiri Ingilishi, Digiri a Fannin Sadarwa, Digiri a Ilimin Kasuwanci, Digiri a Fannin Banki da Kudade, Digiri a fannin Akawuntin da Digiri a Tattalin arziki.

A cewar Rector, a yanzu haka makarantar kimiyya da fasaha tana gudanar da karatu a fannoni 19 da aka amince da su, wadanda Hukumar Kula da Ilimin Fasaha ta Kasa (NBTE) ta amince da su, a Kwaleji bakwai na makarantar.

KU KARANTA: Zan bar aiki cikin farin ciki domin na cika burina, tsohon hafsin sojin sama

A wani labarin, A cewar wasu masu yada ilimin Kimiyya, Fasaha, Injiniyanci da Lissafi (STEM), idan aka zo batun shiga STEM, alkaluman suna kan raguwa a Arewacin Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Masu ba da shawara na STEM sun ce wannan raguwar za a iya danganta shi da dalilai da yawa.

Aisha Amoka-Mohammed, mai nazarin shirin kuma mai yada shirin STEM ta lura cewa rashin tallafi na daya daga cikin manyan matsalolin da ke hana ci gaban STEM tsakanin mata a Arewacin Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel