Bashir El Rufa'i Ya Fadi Yadda Mahaifinsa Ya Samu Bayanan Wayar Nuhu Ribadu
- Bashir El-Rufai ya ce mahaifinsa bai bayyana cewa da ya yi kutse a wayar Mashawarcin Shugaba Bola Tinubu a kan tsaro Nuhu Ribadu ba
- Dan tsohon gwamnan Kadunan ya yi karin hasken a lokacin da Najeriya ta ɗauki zafi a kan hirar da Nasir El-Rufa'i ya yi bayan zargin yunkurin kama shi
- Bashir El-Rufa'i mai shekara 33 ya zargi wasu mutane da ƙoƙarin faɗin abin da mahaifinsa bai faɗa ba domin a miƙa shi gidan yari a kan batung
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Kaduna – Ɗan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wato Bashir El-Rufai, ya fayyace cewa mahaifinsa bai taɓa cewa shi ne ya yi satar sauraren wayar kowa ba.
Ya yi ƙarin bayani a kan kalaman mahaifinsa bayan ƴan Najeriya da jami'an gwamnati sun fara naman a binciki Nasir El-Rufa'i kan kalamansa.

Kara karanta wannan
'Baki ke yanka wuya,' Hadimin Tinubu ya bukaci a binciki El Rufai kan zargin kutsen waya

Source: Facebook
A martaninsa a shafin X, Bashir ya bayyana cewa abin da mahaifinsa ya faɗa shi ne wani mutum ne ya saurari wayar, daga baya kuma ya ba shi bayanan ba tare da ya nemi hakan ba.
Bashir El-Rufa'i ya kare mahaifinsa
'Dan tsohon gwamnan ya ce ana kuskuren fassara maganar ne ta yadda wasu ke ƙoƙarin danganta mahaifinsa da aikata laifi.
Ya roƙi jama’a da su guji yaɗa bayanan da za su iya jawo masa matsala, har ta kai a tura shi gidan yari a kan laifin da bai aikata ba.
Bashir ya ce:
"Bai ce shi ne ya saurari wayar kowa ba. Ya ce wani ne ya yi hakan kuma ya ba shi bayanin ba tare da ya nema ba. Don Allah ku daina ƙoƙarin saka mahaifina a matsala.”
Wannan karin bayani ya zo ne bayan hadimin shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya buƙaci a gudanar da bincike kan lamarin, yana mai cewa kalaman tsohon gwamnan suna da nauyi.
Kalaman El-Rufa'i da suka jawo matsala
Tun da farko, El-Rufai ya bayyana a wani shiri kai tsaye a talabijin cewa yana da bayanai kan wata tattaunawa da aka yi ta wayar Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu.

Source: Twitter
Ya ce a wannan hira ne suka ji yadda aka kitsa amfani da jami'an DSS sun cafke shi idan ya shigo Najeriya, sannan su miƙa wa jami'an ICPC.
Da farko ɗansa ya musanta cewa mahaifinsa ne ya fara ko ya umarci a yi satar sauraren wayar, yana mai jaddada cewa an ba shi bayanan ne daga wani daban.
Jaridar Daily Post ta rahoto abin da ya gudana tsakanin matashin da masu bibiyar al'amura a kafafen sada zumunta na zamani inda Bashir ya yi suna a dandalin X.
Mintuna bayan ya yi kokarin ba mahaifin nasa kariya, Bashir ya gaji har ta kai ya fito yana cewa El-Rufai ya yi wa Ribadu kutse a waya kuma a yi duk abin da za a yi.

Kara karanta wannan
"Ƙila don ya ƙi APC ne": El Rufa'i ya yi tir da kai sunan Kwankwaso majalisar Amurka
Abin da El-Rufa'i ya ce kan Kwankwaso
A wani labarin, kun ji cewa tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya ce bai dace a ware Rabi'u Musa Kwankwaso kaɗai ba kan batun ƙaddamar da shari’ar Musulunci a Arewa.
Nasir Ahmad El-Rufa'i yana wannan batu ne a lokacin da wasu 'yan Majalisar Dokokin Amurka ke ƙoƙarin kakaba wa Kwankwaso takunkumi a kan zargin take hakkin kiristoci.
Tsohon Gwamnan Kaduna ya tunatar da cewa jihohin Arewa 12 ne suka aiwatar da Shari’a Musulunci, tare da bayyana cewa akwai lauje cikin nadi na tsamo sunan Kwankwaso kawai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
