Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Saki Bidiyon Mutane 176 da Suka Sace a Kwara

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Saki Bidiyon Mutane 176 da Suka Sace a Kwara

  • Wasu yan ta'adda sun saki bidiyon mutane 176 da suka sace a garin Woro dake jihar Kwara kuma suke ci gaba da tsare su
  • A cikin bidiyon, an jiyo mutanen da aka sacen, wadanda mafi yawansu mata da kananan yara ne, suna neman daukin gaggawa
  • Al'ummar garin Woro, sun ce 'yan bindigar sun dade suna masu barazana, a karshe suka kai masu hari mafi muni a tarihin garin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kwara - Wani faifan bidiyo mai tada hankali da 'yan ta'adda suka saki ya nuna halin da mutanen garin Woro da aka sace a harin baya-bayan nan suke ciki.

Wannan lamari ya faru ne a ƙaramar hukumar Kaiama dake jihar Kwara, inda mutanen garin suka rika kira ga gwamnati da ta gaggauta ceto 'yan uwansu da aka sace.

Kara karanta wannan

Da sake: ADC ta dura a kan Tinubu saboda yunkurin kama El Rufa'i

'Yan bindiga sun saki bidyon mutanen da suka sace a Kwara a cikin yanayi na ban tausayi.
Taswirar jihar Kwara, inda 'yan bindiga suka sace kimanin mutane 176. Hoto: Legit.ng
Source: Original

An ga bidiyon wadanda aka sace a Kwara

A cikin bidiyon da Barutem TV ta wallafa a shafinta na Facebook, an lura cewa mafi yawan waɗanda aka yi garkuwa da su, da suka kai kimanin mutum 176 mata ne da ƙananan yara.

Dangane da wannan bidiyo, wani ɗan uwan waɗanda aka sace da ya yi magana da jaridar Legit.ng ya bayyana cewa:

"Har yanzu ba mu samu kira daga 'yan bindigar ba, amma muna roƙon gwamnati ta yi gaggawar ceto 'yan uwanmu daga hannunsu."

Ya ƙara da cewa:

"Bidiyon ya nuna yadda 'ya'yanmu da matanmu suke kuka suna neman taimako, kuma rayuwarsu tana cikin babban haɗari a halin yanzu."

Wannan ci gaban ya zo ne kwanaki kaɗan bayan wasu 'yan ta'adda da ake zargin suna da alaƙa da Boko Haram sun kai hari garin Woro.

Yadda 'yan bindiga suka kai harin

Maharan sun kai hari ƙauyen ne a ranar Talata da yamma, inda suka riƙa harbin mutane ba kakkautawa tare da cinnawa gidaje wuta.

Kara karanta wannan

Ana wata sai ga wata: 'Yan bindiga sun sake kai hari coci, sun sace masu ibada

Wani wanda ya tsira daga harin ya ce:

"Sun zo da yawansu, suka fara harbi kan mai uwa da wabi. Sun ƙona gidaje kuma sun kashe mutane a lokaci guda a garin.
"Mutane da yawa sun boye a cikin gidajensu inda 'yan bindigan suka babbake su a ciki, lamarin da ya zama mafi muni a yankin."

Mazauna garin sun bayyana cewa maharan ba su raga wa kowa ba, har da malamai, shugabannin addini, da kuma iyalan gidan Sarkin Woro.

Gwamnatin Kwara ta dauki matakai da aka kai hari wasu garuruwan jihar.
Gwamnan Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya na sanya hannu a wata takarda. Hoto: @RealAARahman
Source: Twitter

Gargaɗin 'yan ta'adda kafin kai hari

Mazauna garin sun yi zargin cewa maharan sun daɗe suna yi musu barazana, inda suka buƙaci su karɓi wata baƙuwar akida, cewar rahoton jaridar BluePrint.

Wani mazaunin garin ya shaidawa manema labarai cewa:

"Sun gaya mana mu karɓi akidarsu, amma muka taru muka ƙi amincewa. Wannan ne ya sa suka kai mana wannan mummunan hari.
"Sun aiko mana da takardar gargaɗi cewa idan ba mu karɓi akidarsu ba, za su shafe mu daga doron kasa. Abin takaici sun aiwatar da barazanarsu."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi kisa yayin da suka sace limami, ladan da wasu mutane

Kalli bidiyon da 'yan bindiga suka saki a kasa:

"Dalilin kai hari Woro" - Gwamnan Kwara

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya ce akalla Musulmai 75 ne suka mutu a harin da ‘yan ta’adda suka kai a wasu kauyukan jihar Kwara.

Harin ya afku ne a kauyukan Woro da Nuku, inda aka ce maharan sun tattara jama’a, suka daure musu hannu, sannan suka bude musu wuta, saboda kin karbar akidarsu.

Gwamnan ya jaddada cewa abin da ya faru kisan kiyashi ne tsantsa, yana mai bayyana hakan a matsayin abin Allah-wadai da ke bukatar daukar mataki mai tsauri a jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com