'Baki ke Yanka Wuya,' Hadimin Tinubu Ya Bukaci a Binciki El-Rufai kan Zargin Kutsen Waya

'Baki ke Yanka Wuya,' Hadimin Tinubu Ya Bukaci a Binciki El-Rufai kan Zargin Kutsen Waya

  • Hadimin Shugaban Kasa, Bayo Onanuga ya nemi a binciki kalaman da tsohon gwamnan Kaduna NasiR El-Rufa'i ya yi game da Nuhu Ribadu
  • Tsohon gwamnan ya bayyana cewa sun samu wasu bayanai a kan shirin da Mashawarcin Shugaban kasa kan tsaro Nuhu Ribadu
  • Ya tabbatar da cewa sun samu bayanan ne ta hanyar kutse da aka yi a cikin wayar Nuhu Ribadu, lamarin da ya jawo mamaki a tsakanin jama'a

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya buƙaci a gudanar da cikakken bincike a kan Nasri El-Rufa'i.

Kiran nan zuwa ne bayan tsohon gwamnan ya bayyana cewa sun samu wasu bayanai bayan sauraren kiran da Mashawarcin Shugaban kasa a kan tsaro, Nuhu Ribadu ya yi.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ganduje ya yi magana kan batan Dadiyata, ya maida martani ga El Rufai

Hadimin Tinubu ya nemi a binciki El-Rufa'i
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i Hoto: Nasir El-Rufai
Source: Twitter

A martanin da ya yi a shafinsa na Facebook, Bayo Onanuga ya bayyana cewa bai dace a bar wannan al'amari ya tafi ba tare da bincike ba.

Yadda El-Rufa'i ya tonawa kansa asiri

Jaridar Punch ta wallafa cewa El-Rufai ya yi zargin cewa Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ne ya bayar da umarnin kama shi bayan yunƙurin tsare shi a filin jirgin saman Abuja.

Tsohon gwamnan ya kuma yi ikirarin cewa Hukumar ICPC ta haɗa kai da DSS domin a damke shi da zarar ya dura a Najeriya daga Cairo.

Onanuga na zargin El-Rufa'i ya amsa aikata laifi
Mashawarcin Shugaban kasa a kan tsaro, Nuhu Ribadu Hoto: Nuhu Ribadu
Source: Facebook

A cewarsa:

“Mun gano cewa ICPC ce ta nemi DSS su kama ni sannan su miƙa ni gare su.”

El-Rufai ya ƙara da cewa Ribadu ne ya bayar da umarnin a tsare shi, yana mai cewa:

“Ya kira waya ya bada umarni cewa dole ne a tsare ni jiya.”

Da aka tambaye shi ta yaya ya san cewa Ribadu ne ya bada umarnin, sai ya ce:

Kara karanta wannan

"Ƙila don ya ƙi APC ne": El Rufa'i ya yi tir da kai sunan Kwankwaso majalisar Amurka

“Mun saurari kiran wayoyinsu. Gwamnati tana tunanin ita kaɗai ce ke sauraron waya, amma mu ma muna da hanyoyinmu.”

Martanin Onanuga ga kalaman El-Rufa'i

Bayo Onanuga ya ce kalaman El-Rufai kamar amincewa ne da aikata ba dai-dai ba, kuma ya kamata a yi cikakken bincike a kan lamarin.

A cewarsa, babu wanda ya fi ƙarfin doka, kuma dole ne a hukunta duk wanda aka samu da laifi. A wani ɓangare kuma, lauya kuma mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama, Deji Adeyanju, ya bayyana cewa bai gamsu da cewa akwai wani tsayayyen shiri na kama El-Rufai ba.

Adeyanju ya ce dokokin Najeriya sun tanadi hanyoyin kama mutum, ko dai da sammaci daga kotu ko kuma idan akwai hujja mai ƙarfi kamar yadda doka ta tanada.

Abinda El-Rua'i ya fada wa Atiku

A baya, kun ji cewa tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da jami'an tsaro suka yi yunkurin kama shi ya karbi bakuncin Atiku Abubakar a gidansa.

Nasir El-Rufai ya shaidawa Atiku Abubakar cewa abin da ya faru da shi a filin jirgi ya kara tabbatar da cewa dole 'yan adawa su kafa gwamnati a shekarar 2027.

Tsohon gwamnan ya kuma fada wa Atiku cewa bai kamata su runtsa ba har sai sun kawar da Shugaba Bola Tinubu daga mulki a filin babban zaben kasar nan mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng